← Book details Buzu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 82

Sashe 69

Buzu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce "To shikenan, tashi" Sai dai ƙafafuwanta suka yi mata nauyi, ta kasa tashi, saboda haryanzu tana jin nauyinsa, kenan har soyayyar da suka yi da Omar ya sani, amma ya ƙyale ta a gidansa.
Babu tsammani ta ji ya saka hannu ya ɗago ta tsaye. Ya ce "Na saka an ɗan yi mana gyara a gida, zan canza miki komai. Har cikin zuciyata na yafe miki, na san wasu abubuwan ba laifinki ba ne, kuma ko dan kusanto da Nana gare ni da ki ke yi yakamata na yafe miki. Allah ya sanya kin yi tabbataccen tuba" A duk lokacin da ya ambaci Nana, sai ta ji baƙin ciki kamar ya halakka ta. Ya sumbaci goshinta, ya mayar da ita kan gadon ya zaunar da ita, ya ce "Allah ya baki lafiya" Daga haka ya juya ya fita. Wani irin kuka ta saka, gaba ɗaya alamu sun nuna, a yanzu baya ganin mutuncin komai idan ba na matarsa da ɗansa ba. Ƙarara a idonsa da mu'alarsa ake iya karanto tsagwaron son da yake yi wa Nana.

Duk da yadda Sultan ya yi watsi da Imam Zahradeen, amma bai yi zuciya ba ya yi uwa ya yi makarɓiya a kan shirin gudanar da bikin ɗan uwansa.
Tuni baƙi suka fara hallara, aka ɗauke Nana daga cikin gidan Sultan, zuwa estate ɗin da yake mallakin masarauta, da galibi ake saukar baƙi a can. Estate ɗin da sunan Hammad aka saka masa, wanda a nan ta fara zama tare da Asal da ƙawayenta a ɗaya daga cikin gidajen.
Nana ba ta yi zato ba, ba ta yi tsammani ba, kawai ta tarar da mahaifiyarta da ƙannenta su Walida.
Gaba É—aya Nana ta yi wata irin rikicewa, jikinta ya hau tsuma.
Maijidda da kanta ta tashi ta nufi Nana cikin farinciki. Nana ta faɗa jikinta ta rirriƙe ta, cikin dashewar murya ta ce "Um.umm.Umma! Umma ki yi haƙuri dan Allah"
Maijidda ta ce "Shhh, kar ma ki kawo wannan zancen, ni yanzu lokacin farinciki ne da murna, dan haka kuka ya ƙare. Abin arziki da farinciki ne ya tara mu. Ni dai na gode wa Allah da ya sanya ina da rabon sake ganinku cikin kwanciyar hankali da kuma ƙoshin lafiya"

"Umma idan ba ku yafe mini ba, hakkinku ba zai bar ni ba, na yi wauta na yi shirme, na bar ku da fargaba da kuma zullumi."

"Duk ya wuce, ya zama tarihi, Alhamdillah tun da Allah ya amsa addu'armu ya haɗa mu cikin aminci da kwanciyar hankali." Tuni idanun Nana suka rine zuwa jawur, ta ƙanƙame Maijidda duk da babu wata shaƙuwar a zo a gani a tsakaninsu, amma wani irin abu ne mara misaltuwa Nana take jin sa a zuciyarta game da Umman nata.
Ta ƙwaƙume ta, ta ƙi sakinta ta kwanta lamo a jikinta.
Maijidda ta ce "Ai mijin naki ma ya zo mun gaisa, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Na ce a kawo mini jikin nawa na gan shi, aka ce mini yana ƙarƙashin kulawa ta musamman, zan gan shi amma ba yanzu ba" Nana dai babu baki, ba ta iya cewa komai ba. Sai yanzu take ƙara jinjina girman laifin da ta aikata. Ta tuna lokacin da aka raba ta da Muhsin na ɗan kwanaki tashin hankalin da ta shiga, ita kuma ta bar gida kusan shekara uku ba ta waiwaya ba, kuma still ana rarrashinta.
Nene ce ta zo, tare da hadimai, da tarin kayan abinci, tare da su Anty Fati 'yan uwan Mai jidda da ta su motar isowarta kenan.
Babu abin da Nana take yi sai gode wa Allah, sai murna suke yi da ganinta, tare da taya ta murnar matsayin da Allah ya É—aukaka ta ya kai ta.
Nana ta ce "Nene ga Ummana, Umma ga Mamana ta Niger ni yanzu a iyaye bayan ke, ba ni da wata uwa da ta wuce Nene. A hannunta na haifi Muhsin, ban san ya zan misalta miki riƙon da Nene ta yi mana ba Umma. Ki yi mata godiya."

Nene ta ce "Dama idan uwa ta yi wa É—anta abu, sai an yi mata godiya ai hakkinta ne ta yi"

Ta miƙa wa Maijidda hannu suka gaisa, su Anty Fati suka hau yi mata godiya. Nene ta ce "Ni ina ƙaunar Nana saboda Allah, dan haka duk abin da na yi mata ina jin kamar na yi wa ɗan cikina ne"

Sam ranar Nana bata rintsa ba, ji take yi tamkar mai Jidda ta mayar da ita cikinta, gani take idan ta yi bacci zai zamana abin da yake faruwa mafarki ne.

Aka din ga ɗawainiya da su, Maijidda da ta taho da 'yan kayanta, na ƙara gyara Nana, yadda ta ga Nene na faɗi tashi a kan Nana, sai ta kasa komai.
Washegari su Imrana suka iso, mota uku ta 'yan Kano, hatta Suwaiba da ba ta da cikakken hankali, da Jamila da babu cikakkiyar lafiya, haka Mama ta tarkata ta taho da su. Saboda a yi komai a kan idonta.
Ana cewa ga motar su Baba can, Nana ta zabura za ta yi waje, Nene ta ce "Nana ya haka? Dole fa ki canza yadda ki ke gudanar da al'amuranki, da da kuma yanzu ba É—aya ba ne ba. Ki bari za su shigo ai.
Ummi ce ta fara shigowa, suka rumgume juna ita da Nana suka fashe da kuka. Su Uwani ma suka shigo gaba É—aya sai falon ya kaure da koke-koke.
Uwani da Ummi kamar su haÉ—iye Nana, Uwani ta ce "Ummi ke ce haka? Kin ga wani irin kyau da ki ka yi?" Nana ta yi murmushi.
Ta riƙo hannun Jamila cike da farinciki, duk ƙasan zuciyarta cike yak da mamakin, yadda ta ga Jamila ta yi wata uwar rama mai ban tsoro.
Duk da ba miji ɗaya suke aure ba yanzu sai da Mama ta yi turus ganin Mai Jidda, ba ta taɓa zaton za ta ganta gurin bikin Nana ba. Ta ganta tsaf da ita cikin nutsuwa.
Uwani ta zauna kusa da Maijidda da su Anty Fati, suna hirar yaushe gamo.
Nana dai kasa hirar ma tayi da su, gaba É—aya kunyarsu ta hana ta cikakken sukunin haÉ—a ido da su.
Bayan sallar isha'i, barori suka nemi da a yi shiru, Imam Hammad zai shigo. Aikuwa kamar ruwa ya cinye kowa aka yi shiru.
Shi ne ya shigo tare da Mahmoudu, da hadaimai biyu, suka tsaya a bakin ƙofa shi kuma ya shiga. Yana ganin Uwani ya saki murmushi, ya tafi gabanta ya durƙusa.
Ta ce "ÆŠan nan, dama babban mutum ne kai? Ka gane ni?"
Ya ce "ÆŠa ba zai manta uwa ba ai, kuma É—an halak baya manta alkhairi. Ba zan manta da ke ba, Allah ya saka da alkhairi"
Ta ce "A'a ai É—a baya yi wa uwa godiya, mun same ku lafiya?"
Ya ce "Alhamdillah" Ya kalli Ummi da take ta murmushi ita ma, ya ce "Babbar Yaya, fatan kun sauka lafiya, kuma kun ji daɗin ƙasar tamu"

Ummi ta ce "Alhamdillah, mun same ku lafiya?"

Ya ce "Lafiya ƙalau, ina sake amfani da wannan damar, gurin sake baku haƙuri, da abin da Asmy ta yi, duk laifin a kaina yake, nine mai laifin amma ina bayar da haƙuri dan Allah a yafe mana. Sannan ina sake yi muku godiya sosai da sosai, Sultan ma ya ce a gaishe ku"
WaÉ—anda ba su san shi ba, suka din ga yaba kyawu da kamalar Hammad.
Daga nan ya nemi zai tafi da Nana, za ta je gurin su Baba inda suka sauka su gaisa, sannan a dawo da ita.

Su na shiga mota, ya kwanta a jikin Nana yana sauke numfashi ya ce "Da na yi niyyar idan aka gama taron nan, ki yi kwana biyu ki huta, sannan ki tare amma gaskiya yanzu na fasa, ji nake kamar na gudu da ke"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bari a kwana biyun"

"Ba zan iya ba, ana tashi kawai a kai mini ke gida, gidanki ya kammala komai an saka mana, mukaÉ—ai muka rage mu shiga" Yayi maganar yana sumbatar bakinta.
"Ya naga jikinki ya yi sanyi ne, kamar wata amarya?"

"Wallahi Sayyid tsoro nake ji, ban san da wani idon zan kalli Baba ba, ban kyauta ba abin da na yi ko kaÉ—an"

"A'a ki kwantar da hankalinki, Baba fa tun kafin su zo, na tura an ba shi haƙuri, yau da suka zo an kai shi har gurin Sultan, ya ba shi haƙuri, nima na je na same shi, shi duk damuwarsa ma ya ganki ne. Babu wani abu in sha Allah"
Haka suka ƙarasa jikin Nana a sanyaye duk a tsorace take.
A wani sashi na gidan Sultan, aka sauki su Baba, tare da Imrana da Gaddafi.
Nana ta tsaya cak, ta sanya hannayenta, ta toshe bakinta, wani irin kuka mai ƙarfin gaske yana kufce mata.
Gaddafi ne ya taso ya riƙo hannunta, ya ƙarasa gaban Baba da ita. Sai da Sayyid ya ji wani iri, duk da kasancewar Gaddafin yayanta ne.
Nana tun da ta buɗe ido, Baba bai taɓa rungume ta ba sai yau, tana kuka yana kuka. Da kyar maganarta take fita ta ce "Baba ka yi haƙuri, ka yi haƙuri dan Allah ka yafe mini. Baba na yi wauta da rashin hankali Baba ka yi haƙuri na san na sanya ku a tashin hankali"

Sai da Baba ya yi kuka mai isar sa sannan ya iya furta "Babu komai Nana, ni dai na gode wa Allah tun da kina nan cikin ƙoshin lafiya, Alhamdillah, Alhamdillah na gode wa Allah".

Haka ta rungume Nasiru ma tana kukan farinciki, ta ƙara tabattar da duk lalacewar naka naka ne, ta shiga farinciki mara misaltuwa da ganin ahalinta a tare da ita.
Chapter 69 · 0% Book details