← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 44

Sashe 8

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai kam ai dama baka da fahimta, komai se an zauna an maka gwari gwari kafin kake ganewa, yanzu kamata yayi mu kama yaron nan a hannun mu kuma dole se ta hanyar matar sa dan ai shi ba sakarai bane da ze dawo ya yarda damu bayan duk abinda suka dinga faruwa, amma ina matar sa ta zama tamu ai ruwa tasha kaga ta nan zamu dinga samun duk bayanan da muke so a kan sa kuma mu dinga aiwatar da shirin mu a kan shi hankali kwance har mu kai shi ƙasa".

"A soke shi, ban yarda da wannan tsarin ba in har se ita zaki aura masa to a fasa".

"Zo tsaya mana jarumina, tsaya ka saurare ni kaji?".

Ta faɗa tana bin bayan shi da sauri sedai ko juyowa be yi ba balle ya tsaya saurarar ta kamar yadda take so, seda ya kai bakin ƙofar falon ya juya gare ta

"In har aka gabatar da tsarin nan tabbas za'a samu matsala dan haka kar kuce ban faÉ—a muku ba, a soke shi shine kawai kwanciyar hankali".

Yana faɗa ya fice yayin da dattijuwar ta dafe kanta tana koma wa bedroom ɗin da sauri ta ɗauki phone ɗin ta ta shiga dialing wasu numbers, tsawon lokaci tana ringing amma ba'a ɗauka ba har ta katse, tsaki taja ta kuma dialing, wannan karon ma kamar ba za'a ɗauka ba dan se a kusan ringing ɗin ƙarshe aka ɗauka, bata jira wani gaisuwa ba ta shiga kora dalilin kiran da tayi

"Plan cancelled, a daƙile komai a kuma tsayar da komai zuwa lokacin da zan sanar dake yanzu akwai matsala a ƙasa".

Tana gama faÉ—a tayi hanging call É—in tare da wurga wayar kan bed itama ta biya cikin tunaninnikan dake yawo a kwanyar ta.

                         ★★★★★★
                         5 years later
                         ★★★★★★

Cikin sauri sauri take Rolling veil ɗin a zagayayyar fuskar ta, pin ta manna a jiki bayan ta daidaita zaman mayafin sannan ta matsa daga wajen mirrorn, rashin ganin su a ɗakin yasa ta ja ƙwafa ta kwashi bags da food flask ɗin su ta fita dashi tare da jawo ƙofar ɗakin ta sa mata key.

ÆŠakin dake kusa da nata ta idasa tana É—aya labulen

"Barka da asuba Hajiya".

"Barka kadai uwar biyu, ina dai kun tashi Lafiya".

"Lafiya lau na tashi, su kam na san tuni kin san ya suke tin da sun ƙaura nan".

"Aikuwa dai muna tare da ƙawaye tun ɗazu muna gaisawa".

"Ai yayi kyau, bari mu wuce mun kusa makara, Ibty, Ifty maza ku taho mu tafi".

"To se kun dawo, Allah ya tsare ya bada Sa'a".

"Ameen Hajiya, mungode".

Daga bayan labulen Hajiya suka fito se zarar ido suke yi dan sun san sun yi ba daidai ba, ita kam bata tsaya wata wata ba ta kama hannun su a each hand É—in ta suka fita daga gidan.

Napep ta tare musu suka hau inda ta e ya kai ta Star light Academy wato makarantar yaran.

Juyowa tayi ta kalli Ibty dake gefen daman ta, da sauri yarinyar ta sunkuyar da kanta haka ma da ta kalli Ifty kafin kuma su haÉ—a baki wajen faÉ—in

"We are sorry Mamma".

Girgiza kai tayi ta maida hankalin ta batare da tayi responding masu ba

"Please kiyi haƙuri Mamma, Allah Ifty ce tace muje mu gaida Hajiya tun da baki gama da wuri ba".

"So Ifty ce yayar ki ko kece yayarta?".

"Ba zamu kuma ba, insha Allah Mamman musu".

"Allah yayi muku Albarka". Ta faÉ—a tana rungume kawun su, suma sosai suka kwanta a jikin ta suna faÉ—in ameen.

Ko da suka je school É—in bata bar su ba seda ta raka su class É—in su primary one Sannan ta tafi bayan ta sake jaddada musu zama good girls.

Cikin rashin jin daɗi ta tare wani napep ɗin ta shiga zuwa wajen aikin ta, sam bata so ba yau tayi latti, tun da ta fara aiki dasu zata iya cewa yau ne kawai ta makara amma se ta ke jin kamar ta aikata wani crime babba duba da yadda aka dinga maimaita mata rashin son makara a gare ta kasancewar tana riƙe da post ɗin secretary ɗin C.E.O na wajen baki ɗaya.

Bakin makeken building É—in ta tsayar da me napep ta biya shi kuÉ—in sa ta nufi gare É—in.

Ƙarin building me da yaji glass ta kusan ko ina haka kana kallon shi zaka bashi hawa kusan biyar ko bakwai a ƙiyasce, daga can saman building ɗin aka rubuta da manyan harufan, A.A GAMJI Company.

Kamar ko da yaushe yau ma se da aka caje ta duk kuwa da kasancewar ta ma'aikaciya a wajen wanda wannan doka ce hatta shi kan sa C.E.O É—in in ze shiga ko so nawa ne se an caje motar sa da shi kan sa, wannan yasa kamfanin ke daga cikin manyan kamfanonin da ke da cikakken tsaro da doka.

Tun a bakin gate ta zare baƙar after dress ɗin da ta ɗora kan white hijab ɗin ta iya kafaɗa da rigar jikin itama fara iya gwiwa se dogon dark blue ɗin wando daga ƙasa, ƙafar ta kuma sanye da blue ɗin socks da takalmin ta wedge baƙi.

Da sauri da sauri ta dinga takawa batare da ta kula gaisuwar da ma'aikata ke mata ba ta wuce lifter tayi pressing kan fifth floor inda nan ne office É—in C.E.O É—in yake, seda tayi wani gasping air ganin yau ya rigata zuwa dan ga nan office É—in a buÉ—e alamun yana ciki.

Kan table ɗin ta ta ajiye jakar ta da komai ta ƙara sa cikin office ɗin sosai da sallama, kanta a ƙasa amma yaji sautin amsawar sa can ƙasa.

Ta jima a tsaye shiru tana jiran yace wani abu da zata sami damar bashi haƙuri kan lateness ɗin da tayi sedai shiru bece komai ba kamar ba kowa a ciki se sautin Ac dake aiki a hankali.

"Ehm..am..amm..sorry sir..for the...lateness...it wasn't intentional, am sorry please".

Ta faÉ—a a rarrabe baki na É—an rawa jin shiru be da niyyar cewa komai.

"Any schedule for today?".

Da sauri ta ɗago tana gyaɗa kai uwa ƙadangaruwa

"Yes...sure sir".

Ta fice da sauri zuwa table ɗin ta tare da fara ƙoƙarin ciro iPad ɗin ta, inda Allah ya taimake ta duk sanda ta zama less busy ba wai ɓata lokacin take a banza ba, a'a tana rage wasu ayyukan ne kamar wannan schedule ɗin tun jiya ta haɗa shi gashi kuwa se mata amfani.

Komawa tayi office É—in.ta matsa gaban table ta ajiye masa iPad É—in ta shiga yi masa bayanin schedule É—in É—aya bayan É—aya, seda ta gama gaba É—aya sannan yasa hannun sa dake cike da gargasa ya É—au ipad É—in yana bi, sanar mata da wanda zeyi attending yayi yayinda yace ayi postponing ragowar.

With due respect ta karɓa ta juya ta fita first office inda nan take, gyara kayan ta tayi kana ta zauna ta shiga aikin ta cike da ƙwarewa da sanin makamar aiki.

Tana nan zaune ya taho shiga office ɗin, kamar kullum cikin mutunta juna suka gaisa dashi, tana matuƙar girmama shi domin yasan mutuncin ma'aikata haka kuma ya riƙe nashi mutuncin, manager kenan HAISAM ƘADEER, babban makusanci ga CEO ɗin su da alama dan shi kaɗai ne bashi da wani shamaki na shiga office ɗin sa a duk wadda yaso.

Alarm ɗin da ya shaida mata lokacin meeting ɗin da zasu yi yayi yasa ta miƙe ta tafi duba tsaruwar wajen, komai yayi yadda ya kamata se gabatar wa kawai, komawa tayi ta sake daidaita nutsuwar ta sannan tayi knocking a ƙofar, sakanni kaɗan aka bata umarnin shiga, kanta a ƙasa ta shiga

"Its time for the meeting with Al-azhar group of companies sir".

Takardun kan tables ɗin sa ya tura mata ta ƙarasa ta shiga tattara su har ta gama shirya su tas sannan ta riƙe a hannun ta ta fice dasu.

Duban sa ya maida kan Haisam dake zaune ba shida ko alamun tashi

"Haven't you heard what she said or you're deaf?".

"Won't mind repeating sir".

Dukan table ɗin yayi da hannun sa cikin nuna ɓacin ran sa da ba wanda ke katarin yawan gani se Haisam ɗin

"For God sake ba wasa nake ba Haisam ka kuma san ba lokacin wasan bane, when it comes to business kafi kowa sanin wane ni dan akan haka zamu samu matsala, babbar matsala wallahi cos I won't mind suspending you".

"Ai fa an taɓo rayuwar ka dole bakin ka ya buɗe, dan rashin mutunci tun ɗazu nake maka magana kamin banza amma yanzu ka cika min kunne da ihu, an ƙi aje meeting ɗin in ka tashi ba suspending ba kayi firing ɗina oga sir, aikin banza kawai".

Haisam ya faɗa yana ficewa daga office ɗin bayan ya doka ƙofar da ƙarfin da har yasa salma ɗan firgita.

Fashionable wrist watch É—in ta ta duba taga its five minutes past exactly lokacin meeting É—in, me yake damun boss yau, shine abinda take tunani, he's always a man of his word and time, Yana mutunta lokaci ta yarda ba'a jiran sa sedai ya jira, wannan principle É—in sa ne.

Buɗewar ƙofar yasa ta gyara tsayuwa ta yi ƙasa da kai, seda ya wuce gaba sannan ta bi bayan sa har zuwa scheduled hall ɗin, kamar yadda tayi zato kuwa kowa ya hallara hatta da manager kuwa se ita dashi ne kawai.

Wajen zaman su suka ƙarasa ya zauna ita kuma ta ajiye kayan hannun ta ta gaida mutanen wajen ta shiga gabatar da bayanan da ya kamata ta wajen ta har ta gama tsaf kafin ta zauna ana tafa mata manager ya miƙe yayi nashi ƙarin bayanin da su kaɗai suka gamsar da mutanen siyan share a Company ɗin so shi bece komai ba se negotiation kaeai da aka yi dashi.
Chapter 8 · 0% Book details