Sashe 14
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Seda ya ga shigar ta gidan sannan ya tashi motar ya fita daga layin cike da sanyin jikin da gajiya ta haifar masa, wannan dogon tuƙin da yayi jiya da yau sam be saba masa ba shiyasa gaba ɗaya jikin sa yayi masa nauyi.
Kulle motar yayi ya fita batare da ya kula ganin ta da yayi tsaye ba, da sauri tabi bayan sa har tana haÉ—awa da gudu saboda takunsa irin na cikakkun maza ne masu isasshiyar lafiya
"Yaya Abdu, ya Abdu".
Yana jin ya tsaf amma yayi mata banza hakan yasa ta kuma kwasa da gudu tasha gaban sa lamarin da ya tilasta masa tsayuwar dole sedai tuni ya sake ɗin ke fuska tsaf kamar wanda be taɓa sanin wani abu wai shi annurin dariya ko murmushi ba a duniya.
"Dama Anna ce ke neman ka, tuntuni nake kiran wayar ka in faɗa maka yaƙi shiga, gashi ita kuma se kuka take da kiran sunan yaya nafi wuni guda yau taƙi cin komai".
"Kije ki faÉ—awa baba".
"Zuwa yanzu ya kwanta yaya Abdu, Please ka taimaka kazo muje kayi mata magana ko zata ji, na bata baki amma taki saurara ta".
Sam baya son kallon ta sabida irin shigar dake jikin ta, duk da kasancewar dare ne amma gidan nasu tarwai yake da haske da ko allura ce ta faÉ—i tsaf mutum ze tsugunna ya É—au abar sa ya tashi.
Tun ba yau ba yasan ita da yayar ta nafisa Allah ya ji ƙan rai kamar gabas da yamma ne, sam bata inda suka yi kamanceceniya se ko ta fuska da kuma jini shiyasa ko da sam be sake mata fuska balle ta samu damar kawo masa raini bare kuma yanzu da yake jin kowa ma daidai yake dashi.
"Kije zan zo in nayi wanka, nayi gumi da yawa I can't go to her a haka".
Ya faɗa yana wuce ta cikin tafiyar nan tasa me cike da karfi da isa, bin bayan sa tayi da kallo cike da maɗaukakin shauƙi, lumshe ido tayi tare da rungume hannuwan a ƙirji inda take ji kamar shine ta rungume, wannan maganar da ya mata ji take kamar an mata albishir da shiga aljanna.
Tun yayar ta na da rai take so da ƙaunar yaya Abdu sedai tayi ta ƙoƙarin dannewa, yanzu kuwa da babu yayar ta bata tunanin akwai abinda ze tsayar da ita kuma.
A saɗaɗe ta juya zuwa part ɗin su, bakin ƙofa ta tarar da anna tsaye, da sauri ta riƙo hannun ta suka ƙara sa ciki kafin ta dube ta
"Yaya, cewa yai baze zo ba?".
"Yace zezo amma se yayi wanka, dawowar sa kenan baze iya zuwa gare ki a haka ba".
"Kai masha Allah bari maza in shafa rob ɗin nan a ido na ɗan suyi ja su dinga hawaye, insha Allah buƙatar mu zata biya bari ki gani".
Tsohuwa Anna ta faÉ—a tana murza Rob a fuskar ta, duk yadda idanun ta ke hawaye be sa ta fasa ba se da ta saka sosai ta yadda in ka kalle ta zaka ce ta daÉ—e tana kuka dan yadda fuskar ta tayi jajir kasancewar ta fara haka ma idanun ta suka yi ja suka tasa.
A can ɓangaren Hajiya Babba kuwa da sauri shuraiha dake tsaye jikin window riƙe da curtains tana kallon abinda ke faruwa tsakanin Abu Aulad da Nuriyya ta saki uban ashariya
"Kan uba".
Ta faÉ—a da sauri tana sakin curtains É—in, bata tsaya wata wata ba ta zura bedroom slippers É—in ta tayi waje without minding cewa kayan bacci ne a jikin ta ba, burin ta a lokacin shine ta kai gare su taji me suke tattaunawa a wannan tsohon daren.
Baza tayi sanyar da wata can daban zata ƙwace mata Abdallah ba bayan an gama kwaɗaita mata shi tare da lasa mata zuma a baki yanzu kuma a ce za'a janye, ina ba zata yarda ba.
Sedai kash ko kafin ta kai ga fita daga part É—in su tuni ya shige nasa part É—in ita kuma Nuriyya ta koma nasu hakan yasa ko da ta fito compound É—in bata tadda kowa ba se ma'aikata dake É—an kai kawo dan wasun su ma tuni sun nemi makwanci.
Haka ta koma part ɗin nasu tana cizon yatsa, taso taji me waccan karuwar ke faɗa masa wanda har ya tsaya saurara haka sedai kash bata samu ji ba, ya zama dole ta tunzura Hajiya Babba ayi ayi ai bikin su ko hankalin ta ya kwanta, daga lokacin da ta sami wannan damar a lokacin ita kanta Hajiya babbar zata raina kanta dan kallon ta kawai take itama da tata tsarin da buƙatar akan Abdallah ɗin.
A hankali yake rage kayan jikin sa cike da gajiya, wanka yake buƙata yake kusan sanyi dan yadda yake jin jikin sa na ƙaiƙayi shine kawai abinda se yi yaji sauƙi.
Singlet ɗin jikin sa yake ƙoƙarin cirewa se kuma ya fasa sanadin hango inuwa da yayi jikin labulen sa alamun akwai wani laɓe a ta wajen.
Cikin nutsuwa ya shiga takawa har ya kai wajen yasa hannu ya yaye curtains É—in da suka rufe tagar, tsaye take cikin shaiÉ—anun kayan da dasu da babu a jikin ta basu da wani banbanci, suna haÉ—a ido ta sake masa wani arnen murmushi cike da barikanci kafin cikin kwarkwasa ta shiga lauya jikin ta tana magana da wata seducive voice
"Sannu da zuwa Abu Aulad, ga dukkan alamu ka gaji, don't mind I can takeaway all your stresses, yanzu dai muje kayi wanka ko super man?".
Kamarw anda garwashin wuta ya taɓa haka yayi watsi da hannun da takai jikin sa, ya rabbal alameen be san ya zai yi da rayuwar sa a cikin wannan gidan da a wajen sa gara kabari dashi ba.
Wani irin birkitaccen mafi ya watsa mata da yasa ta yin katantanwa ta faɗi can gefe kanta ya bugu da jikin Centre table ɗin dake falon, cikin wata irin zuciya da ta ciwo shi ya bita yasa ƙafa ta taka sangalalin hannun ta har se da yayi ƙarar dake shaida alamar in har bata sami fracture ba to tabbas ƙashin nan ya fita daga bigiren sa.
Wani wahalallen ihu ta saki da be wani fita da karfi ba saboda tsabar wahala yasa a take Muryar ta ya shaƙe, cikin wani dakusasshen Muryar da ɓacin rai ya haifar masa ya shiga yi mata concrete warning
"This is the first and last time da zan kuma ganin ki a part ɗina, na rantse da Ubangijin da ya busa min rai da second time na kuma ganin ki zan iya ɗaukar ranki dan ko banza an rage mugun iri, annoba kuma jinin shaiɗan, before the count of three ki fice min ɗaga ɗaki in ba haka ba wallahi rataye kibzan yi jikin fanka, fitsararriyar fasiƙa kawai mara kunya da tsoron Allah".
Ai ko kafin ya gama bayanin sa tuni ta tarkata hannun ta tayi waje da mugun sauri dan a yadda ta gan shi da kuma rashin imanin da ya gwada mata ta tabbatar ze iya rataye tan kamar yadda ya faÉ—a.
Da numfarfashi da komai takai kanta part ɗin ta zube kan kujera tana maida numfashi, wani irin zufa ne ke keto mata na wahala da azabar da take sha a jikin ta, bata taɓa sanin haka zafin karaya yake ba se yau.
Ƙwalla take zubar wa tana bin hannun da kallo yayinda cikin ranta take shan mugayen alwashi kala kala a kan shi, tun da ta riga ta ɗora ido a kan shi takuma kwaɗaitu da shi ta rantse ita kuma se ta same shi, in kuwa ba haka ba to tabbas sedai ayi biyu babu uku ba ko ɗaya ma'ana indai ba zata same shi b ato sedai kowace mace ta rasa.
Da sauri ta runtse idon ta lokacin da ta auno shi a idanun ta tare da wata mace, inaaa, ba'a haifi macen da zata amfane shi ba, ada dai tayi wannan imanin amma a yanzu zata iya yin komai in tace komai tana nufin komai wajen ganin ta saka kyakkyawar barrier tsakanin sa da duk wata Æ´a mace kowace ita kuwa.
Ranar haka ta kwanan cikin azaba da raÉ—aÉ—in zuci da na jiki, ga dai jinya ya kwantar da ita kuma wai batare da ya bari ta amfanu da komai daga gare shi ba, ita da ta samu abinda taje nema to da sauki ba karya ta ba ko kashe ta yayi ba zata damu ba tunda ta cika burin ta.
A ɓangaren Abu Aulad ma haka ya kwana a zaune cikin wani irin yanayin da baze fassaru ba, be san da wane suna ze Kira gidan da yake ciki ba haka be san da wane suna ze kirayi mutanen cikin sa ba, be taɓa sanin bawa kan zaɓi mutuwa kan rayuwar sa ba se a kan shi, da ace kisan kai ba haram bane a musulunci da tuni ya daɗe da sheƙe kan sa ya huta.
Tun tasowar sa be san wani abu wai shi farin ciki ba, kullum cikin baƙin ciki da damuwa yake tun fara wayo sa har kawo yanzu da yake shekarun sa na cikakken namiji mai ji da sabon jini da ƙuruciya.
Rayuwar sa a hagunce ta faro kuma har kawo yanzu a haka take, be san se yaushe ne ze samu daidaito na rai, ruhi da rayuwa ba balle har ya samu salama, a duk sanda yaga mutane na rayuwa suna dariya da nishaɗi ya kan tsinci kansa da ayyana dama shine, so da yawa yasha kusan yin saɓo in ya zauna tunani dan ya kan dinga aiyana me yayi wa Allah da yasa ƙaddarar jarabawar tazo a haka, me yasa ba wata daban ba.
Kiran sallar asuba da ake yi ne yasa shi miƙewa yana dafe kan sa dake sara masa ya shiga toilet, daga tsayen da yake ya sakarwa kansa ruwa masu sanyi sanye da wandon shaddar da singlet ɗin batare da ya cire ba, tsayin lokaci Sannan ya gabatar da wanka ya ɗaura alwala ya fito.
Jallabiya ya zura a jikin sa tare da É—aukar tasbah É—in sa ya wuce masallaci, seda aka idar da sallah har gari yayi haske kafin ya taho gida.