Sashe 28
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya kwantar da Ifty kamar wata kwai kana ya nemi drower jikin gado ya zauna tare da bin ɗakin da kallo, komai a nutse a kuma gyare a wajen da ya kamata, babu shirgi ko daya balle kuma datti a ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke tare da yin luuu da idanun sa kamar ze rufe se kuma ya buɗe ya sauke cikin wardrobe ɗin dake buɗe, kayayyaki ne kala kala ninnike a jere tsaf tsaf kamar ba'a taba su ba tun da aka jera, Allah ya sani shi mutum ne me matuƙar son tsafta a rayuwarsa shi yasa baya shiri da kazami ko kazan ta, abu kaɗan ke iya tayar masa da hankali da zuciya shiyasa gaba ɗaya baya ta'ammali da mutumin da be yarda da tsaftar shi ba.
Maida duban sa kan Ifty yayi dake bacci numfashin ta na fita a hankali alamun zazzabin ya sauka ba kamar É—azu da take numfarfashi ba.
Ƙure fuskar ta yayi da kallo yana jin wani yanayi dangane da ita a ransa, shi ɗin mutum ne me matuƙar son yara shi yasa ma tun yana yaro abokai da yan uwa suka sa masa Abu Aulad se gashi sunan ya bishi har girma, duk miskilancin sa a gaban yara zama yake kamar wani aku dan biye musu yake su yi ta shirme, son yaran sa ne ma yasa duk irin dukan da Hajiya take masa baya fashin shiga sashen ta lokacin da ta haifi Nadiya, haka ze dauke ta a ɓoye batare da Hajiya ta sani ba, in kuwa ta gani ranƙwashi mari da dundu ne se yasha ranar amma ba hakan ze Hana ya koma anjima ba.
Akayi na Nadiya aka gama aka zo lokacin haihuwar Abdulkarim, tsananin so da kaunar da ya nunawa kareem ba kaɗan bace hakan yasa yaron ya taso da so da kaunar sa dan lokacin ya zama saurayi Yana junior school lokacin, duk wani kuɗin break ɗin sa akan kareem da kayan wasan sa yake ƙarar dasu, komai ya gani na kareem ne, ci banza ci wofi haka ze kashe masa su gaba ɗaya, tun Ummu na masa fadan ya dinga siyan abinci a school har ta haƙura take masa abinci ya tafi dashi dan komai yawa komai kankantar kuɗin da za'a bashi ba fa ze kashe ba se ya dawo tare da kareem su kashe.
Tsananin shaƙuwar dake tsakanin su ne yasa Hajiya shiga da fita har se da ta raba su kafin hankalin ta ya kwanta dan tace muddin tana raye ba yayan ta ba dan miji, sam sam bata yarda ba ba kuma zata yarda ba.
Dole ba dan yaso ba Abdallah ya hakura da kareem saboda yadda yaron ya ƙware a rashin kunya tashi daya, ban da kuma janye masa da yayi, duk yadda yakai ga kulafucin sa seda ya hakura dan ko hanyar da yabi kareem baya son bi.
Yayi addu'a har so ba adadi kan Allah ya bawa Ummun sa ciki itama ta haifa amsa qani sedai iya shi É—in Allah ya rubuta zata haifa shiyasa har ta koma ga mahaliccin ta ko bari bata sake yi ba bayan shi.
A hankali ya lumshe idanun sa tare da kai hannu kan kyakkyawar sumar iftihal dake gyare ya shiga shafawa cike da matsananciyar ƙauna, ba wai irin gamagarin kauna da yake ji kan Kowane yaro ba a'a, wannan gangariya ce ta daban da take yawo cikin jinin sa tana zagaye dukkan jikin sa.
Da kyar ya haɗiye wani irin ƙullutu me matuƙar ɗaci da ya tsaya masa a makogaron sa, wasu shekaru can baya da suka shuɗe na dawowa cikin kwalkwalwar sa daki daki kamar a lokacin komai ke faruwa, sake runtse idanun nasa yayi da matukar ƙarfi yana hango su kwance cikin jini, kowanne lullube da farin kyalle, wani irin dum kan sa yayi masa da ya sashi sanya hannayen sa biyu ya dafe kan dan ji yayi kamar ze fado.
Bisa tilas ya buÉ—e idanun sa ko ya samu ya dena ganin abinda ke barazana ga rayuwar sa, fararen idanun sa sun kada sun yi jajir saboda tashin hankali, sake kallon iftihal yayi amma a maimakon ya ganta, su ya sake gani hakan yasa aya mike ya fita daga É—akin har lokacin yana dafe da kan sa.
Dakatawa tayi daga shirin kai tuwon bakin ta ta zuba masa ido cike da mamakin yanayin da ta ga ya fito dashi, me kuma ya same shi?, Ta tambayi kanta sedai bata da amsar hakan.
Tana ji tana gani ya shige ɗakin sa tare da maida ƙofar ya rufe da karfi dan har seda ta runtse ido haka ma Ibty, kwata kwata se taji abincin ya fita a ranta saboda damuwar yanayin sa, sosai taji ta damu da halin da yake ciki ba dan komai ba se dan irin so da kauna hadi da kulawar da yake nuna wa ƴaƴan ta, bata damu da yadda baya ko kallon ta ba balle ya damu da ita, iya kaunar sa kan yan biyu ya wadace ta ya kuma isa dalilin da zata damu da damuwar sa.
"Allah ka yaye masa ko me ke damun sa". Ta samu kan ta da yi masa addu'a, haka ta cigaba da bawa Ibty abincin har ta ƙoshi batare da ta kuma ci ba dan ko da tayi attempting hakan kasawa tayi dan se taji gaba ɗaya daddaɗan dandanon abincin ya juya ya koma tsananin daci kan harshen ta , ta haɗiye ma kasawa tayi se tissue ta ɗauka ta tofa a ciki ta nannaɗe.
Haka taja hannun Ibty zuwa bedroom din inda suka iske har lokacin bacci Ifty ke yi, kaya ta canja wa ibtisam zuwa na bacci masu É—an kauri dan kiran sallar magrib ake yi lokacin haka ma iftihal ta canja mata, alwala ta É—aura tayi sallah kana ta zauna gefen iftihal tana kallon fuskar ta yadda ta rame daga jiya zuwa yau.
Bata san yaushe bane se kawai tsintar kan ta tayi da shiga tunanin abinda yasa mood din sa ya canja alhalin har ya shiga kwantar da Ifty idanun sa tar suke farare tas dasu babu ko alamun ɓacin rai se gashi ya fito ido yayi masa jajir gashi kuma dafe da kai wanda ga dukkan alamu ciwo yake masa.
........."Seda aka yi masa ƙarin ruwa leda biyu tare da allurar bacci dan rashin hutu da damuwa ne suka haddasa masa ciwon kan, likitan yace a dena barin shi da yunwa haka kuma ya rage sa damuwa a ran shi da kuma yawan tunani"..........
Maganganun da Haisam ya faÉ—a mata suka dawo mata kamar bitar karatu, kenan yana da damuwa aransa?, Amma wace irin damuwa ce wannan da take haddasa masa shiga wani hali irin haka in ya tuna?!.
A nata hasashen da kuma tunanin babu wanda ya kai ta damuwa sedai tana kokarin ɓoye hakan, damuwar yadda ta rasa iyaye biyu a shekarun rashi wayo, damuwar rashin dangin da suka damu da ita da rayuwar ta se kuma damuwar yadda rayuwar ƴaƴan ta za ta kasance a nan gaba in suka bukaci sanin asalin mahaifin su ko kuma suka gano ba Abu Aulad ne baban su ba, ita kuwa in haka ta faru yaya za ta yi, me zata ce musu?, Wannan sune fargabar ta da damuwar ta a ko yaushe sedai tana kokarin ɓoyewa da yin rayuwa daidai gwargwado ko dan walwalar ya'yan ta
Ashe za'a iya samun wanda ya fita damuwa ko kuwa dai tsabar ragwantan zuciya ne yasa abin da be kai ya kawo ba yake sa shi cikin wani hali?.
..'aa salma, be kamata ki yanke hukunci batare da kin san me ke damun sa ba, watakil damuwar sa tafi taki, watakila ta ninka taki ninkin banin kin dan ko kema in Baki buÉ—e baki kin faÉ—a ba babu wanda ze San kina da wata damuwa, to kowa ma hakane, never judge a book by its cover'..
Abinda wani bangare na zuciyar ta ya tunatar da ita yasa ata sauke ajiyar zuciya tana yarda da hakan da har se da ta jijjiga kai a fili, tabbas haka ne, kai dai kawai ka kalli dan adam a yadda ka ga zahiri sa yake rayuwa, wani in da ze buÉ—e maka zuciyar sa kaga tarin kunci, damuwa da tashin hankalin da yake ciki yake rayuwa a zuciyar sa se kaji naka ba komai bane, se kaji kai baka ma da sauran damuwa, se kaji kai be kamata kayi kuka ba sam, se kaji kai É—in a aljanna kake.
Ba wai kuÉ—i ne jin dadi da kwanciyar hankali ba, a'a su É—in wani sashe ne na hakan, babban ginshikin jin dadi shine kwanciyar hankali, duk rayuwar da ta kasance ba kwanciyar hankali hadi da nutsuwar ruhi to tabbas babu jin dadi a cikin wannan rayuwar.
Masu kuɗi da yawa na rayuwa cikin daular kudi, komai na buƙatar rayuwa akwai shi a wadace amma su ɗin basa cikin jin daɗi, meye dalilin hakan?, Rashin kwanciyar hankali!
Misalin kamar rayuwa ce ada lokacin iyaye da kakannin mu da kuma rayuwa a yanzu lokacin mu.
Ada babu yawaitar mahaukatan kudi amma akwai kwanciyar hankali saboda wadatar zuci da rashi tsadar rayuwa amma a yanzu da kudin ya yawaita se kuma aka rasa cin kuÉ—in cikin daÉ—in rai saboda rashin kwanciyar hankali.
Ada gidan mutane kan kwana a bude, mutane kan kwana a waje batare da tsoron komai ba, amma a yanzu gida bayan an sa masa kofar da mutane da yawa ke gadi se an kara da su security camera, security wire da ragowar ababen tsaro amma na cikin gidan hankalin sa be kwanta ba, ko yaya yaji ƙarar wani abu me amo se ya firgice cikin tsoron hari ne aka kawo ko ana neman farmakar sa ne.
Talakawa dake ganin su basu dashi so da yawa kuma sukan fi masu kudin kwanciyar hankali, talaka ya bar gida a bude yayi bacci batare da wata fargaba ba, talaka yayi yawo ko ina batare da wani me tsaro ko kula dashi ba hankali kwance, amma me kuÉ—i fa?!.
Jin dadin rayuwa ya ta'allaka ne kan ginshikai uku
1- kwanciyar hankali
2- wadatar zuci
3- kuÉ—i