Sashe 16
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina raye, da rai na da lafiya ta amma kayi aure ban sani ba Abdallah, kana son nuna min ban isa da kai bane ko me, ko da yake haka ne dan ka nunawa duniya ta hanyar take magana ta ka aura wadda na nuna ban aminta ba".
Sam kalaman mahaifin nasa basu yi masa daÉ—i ba amma haka ya danne zuciyar sa ransa na sake zafafa da wariyar launin Fatar da mahaifin nasu ke nuna wa tsakanin su kamar shi da sauran yan uwan sa ba abu É—aya bane.
"Kayi haƙuri baba, ban auri salma dan baka isa dani ba se dan soyayyar da nake mata da kuma abin da ya faru dan kar a sanadin kuskure na mutuncin ta dana ƴaƴan ta ya tabu".
Hajiya Babba ce tayi tsumut tasa baki cikin maganar bakin ta har yana karkarwa
"Aikuwa sedai ka sake ta dan wannan auren sam ba mai yiwuwa bane dan tuni nayi maka mata matsayi na na uwa a gare ka, tuntuni kuma kasan da maganar dan har mahaifan ta sun sani dan haka yanzu base anjima ba ka saki wannan abar me suffar yan ruwa, yo banda ma rashin tunani irin naka me za kayi da bazawara me yaya biyu bayan ga budurwa yarinya danya me jini a jika".
"To kaji hukuncin mahaifiyar ka wanda Nima ina bayan ta dan ban taɓa ganin bahagon aure irin wannan ba, ba wakilan ango ba komai a ɗaura aure kamar dai dangin nata sun gaji da ita ko kuwa ta ishe su".
Sosai zuwa yanzu yake jin ya kai gejin da baze saurara wa kowa ba ciki har da mahaifin nasa da baida wata ra'ayi ko magana ta karan kan sa se abinda wannan munafukar tsohuwar ta faÉ—a
"Ka gafarce ni baba dan ban da ra'ayin auren kowa se salma, ya kuma kamata Ku amshi nawa ra'ayin wannan karon dan wancan na farko ku kukai min zabi na kuma yi muku biyayya, sedai a yanzu bana jin zan iya rayuwa da wata mace da ba wannan ba, maganar mahaifiya kuwa na dade da sanin ban da ita balle har ta zaba min mata ban sani ba ko kafin ta rasu ne tayi hakan"!.
Da wani irin hanzari Hajiya Babba ta É—ago cikin firfito da idanu waje na mamakin kalaman Abu Aulad, shi kan sa baba seda ya Sha jinin jikin sa da words din balle kuma Æ´aÆ´an Hajiyar da suka zaburo tamkar masu shirin kai duka
"Maza ka kiyaye bakin ka kan mahaifiyar mu dan ba zan dauki rainin ka a kanta ba, ba tun yanzu na fahimci hayaƙi kanka yake ba sedai akan Hajiya wallahi zan gyara maka zama ƙaramin mara kunya kawai".
Wannan karon kam dariya yayi har se da fararen jerarrun hakwaran sa masu tsananin haske suka bayyana tare da sauke su Ibty daga jikin sa ya yunƙura daga kwantar da bayan sa da yayi jikin kujera tare da duban fuskar yar sa ɗaya tal wato sumayya da tayi maganar
"Bisimilla uwar Saudah, in har kin fasa gyara min zama ke ba sumayya Abdulsalam Gamji bace, maza ƙaraso ina jiran ki".
"Bana son neman fitina sumayya, magana ta ƙare tun da ka kafe kana son matarka se ka kaita wajen da zata zauna ko, kuma ka saurare ni da kyau dan, zan yi bincike na a kanta, duk na samu wani abu na assha a tattare da ita tabbas zaka sau ta dan ba zan yarda ka bata min zuri'a ba haka kuma a ko da yaushe hukuncin take magana ya ka iya riskar ka".
Be damu da kalmar bincike da Baban ya ambata ba balle kalmar hukunci, ya riga ya saba da wannan dan har gwara wannan karon hukuncin akan laifin da ya aikata ne ba sharri ba.
Hannun sa ya miƙa ya ruƙo na Salman bayan ya miƙe ya miƙar da ita itama kana ya sake ta tare da sunkuya wa ya sabi Ifty ya riƙe hannun Ibty sannan ya nuna mata hanya alamun tayi gaba, cikin hanzari ta nemi wucewa sedai fimcikar da aka yiwa mayafin jikin ta yasa ta dakata tare da saurin riƙe mayafin dan kar ya fita daga jikin ta.
Kakkausan kallon gargadi ya shiga wurgawa sumayya yayinda hannun da tai yunƙurin marin Salman ke riƙe cikin nasa yayi masa riƙon tsauri, azabar zafin da take ji kan rikon ya kasa ɓuya kan fuskar sumayya
"Ko da wasa, wallahi ko a mafarki kar ki sake attemptimg kai hannun ki jikin matata dan ban san me zan iya aikata miki ba sedai komai zai iya faruwa ciki kuwa har da zage ƙwanji dan kare martabar ta".
Ya ƙarasa yana wulli da hannun nata da tayi saurin rikowa da dayan tana yarfewa, be damu da zagin da Hajiya Babba ta shiga surfa masa ba ya juya ga baba da yake nan zaune a gurin amma ake wannan iya shegen
"Ban cire kowa ba ban da kai baba, Babba komin girman sa da kuma yaro komin kankantar sa yayi yunƙurin taɓa min mata to fa se inda ƙarfi na ya kare dan a kanta zan iya aikata komai, in nace komai ina nufin komai kuwa".
Be saurari me baba ze ce ba ko ya kula maganganun Hajiya Babba yaja hannun yaran yayi waje dasu dan ita salma tuni ta tsufa da ficewa, tun lokacin da ya tare hannun sumayya daga sauka kan fatar fuskar ta.
Batare da ya kalli inda take ba yayi gaba riƙe da hannun yaran hakan yasa ta rufa masa baya jiki a sanyaye har zuwa part din sa.
Madaidaicin falon ne da ya É—auke set na kujeru, kitchen da dining set bedroom biyu se É—an siririn ventilation.
A tsakar falon ya sake hannun twins ya nuna mata dakin without giving her a glance
"Here's your room, ga can kitchen Wanda ke dauke da store, zuwa anjima zan kawo kayan girki".
Kai ta gyada tare da yin godiya kana ta ja hannun babies din ta zuwa dakin, kallo ta shiga ƙare masa kusurwa kusurwa cikin yabawa da tsarin wajen, makeken bed ne lafiyayye da ke shimfiɗe da zanin gado me kyau, dressing mirror se ƙatuwar walk in wardrobe me ƙofofin glass, ƙatuwar foam a tsaye se ko ƙofar toilet dake can gefe.
Ajiyar zuciya ta saki a hankali ta shiga takawa cikin sanyin jiki, kan mirror ta ajiye handbag din ta tare da neman bakin bed ta zauna twins na zama kusa da ita.
Mintuna kaÉ—an ya shigo da jakunkunan kayan su ya ajiye tare da ficewa.
Kamar wadda aka tunawa da wani abu ta miƙe da sauri ta hau cire kayan ta tare da sauya wa da uniform ɗin wajen aiki, da sauri da sauri takarasa ɗiban komai da take buƙata kafin ta ja hannun yan biyu suka fita falo.
Baya nan dan haka ta shiga tunanin yadda ya kamata tayi, ta fita be sani ba ko kuwa ta zauna, makarantar su Ibty fa bayan ko jiya kamar basu je bane?, Amma kuma ya zata yi da sashen tunda ba zata bar shi a buÉ—e ba?
Cikin fatan tadda mukulli ta ƙarasa tana duba jikin ƙofar, cikin Sa'a kuwa yana jiki be cire ba, da hanzari ta kira su Ibty suka fita tayi locking ƙofar tare da jefa keys din jaka suka nufi hanyar gate gaban ta na ɗan faduwa na tsoron haduwa da wani ɗan gidan.
Ƙaƙƙarfan numfashi ta sauke lokacin da suka bayyana gaban gate ɗin ba tare da ta haɗu da kowa ba, napep ta tsare musu kamar yadda suka saba.
Seda ta tabbatar da shigar yaran aji kafin a juya da ita zuwa ma'aikata.
A hankali take takawa har ta ƙaraso gaban gate ɗin kana ta zare baƙar doguwar rigar jikin ta ta saka a haka yayinda security suka shiga aikin su, seda suka tabbata da bata dauke da komai na cutarwa sannan aka bar ta ta shige.
"Congratulations Salma, you now Mrs Gamji".
"Congratulations Salma, Allah ya sanya alkhairi".
"Happy married life colleague".
Ire iren wannan kalaman ta ringa receiving daga yan uwan ta ma'aikata na taya murna, ita dai bata cewa komai se murmushi da thanks yayinda cikin ranta ke cike da mamakin wa ya sanar musu sedai bata da me bata amsa.
Table ɗin ta tasa tissue ta goge kafin ta zauna ta fara ƙoƙarin kunna laptop ɗin ta dan fara ayyukan ta, hankali kwance take operating din ta tana haɗa schedules da kuma gyara wasu appointments ɗin, tana gamawa ta shiga duba wasu files da ke ajiye suna jiran ta, tana tsaka da aikin Haisam ya ƙaraso wajen, file ne se shiga ya ɗauka a outer office ɗin CEO dan Yana da damar shiga iya wannan ko da shi CEO ɗin baya nan.
Cikin mamaki yake kallon ta da tunanin me take yi kuma a nan ita da ta tare a gidan miji yau yau É—in nan
"Salma, me kike yi a office Kuma ke da kike amarya".
Ajiye takardar hannun ta tayi ta É—ago ta shiga gaida shi mutunce kamar yadda ta saba a baya, amsawa yayi yana sake maimaita mata tambayar sa
"Ehm aiki nazo".
Ta faÉ—a tana nanata kalmar amarya a zuciyar ta tana jin ta banbarakwai jin ita ake dangantawa da ita.
"Shi yace ki zo aikin?, Yana ina lokacin da kika fito?".
ÆŠan tsai tayi kafin ta girgiza kanta
"Ba shi bane, baya nan na fito, na kai su Ibty school ne shine na taho nan".
"Sam be kamata ki fito yau ba salma, É—azu É—azu fa kika tare a gidan ki, wannan ai se kisa a kuma buga ku a jarida ku sai shiga bakin duniya, dan Allah tattare komai ki ajiye ki tashi ki koma gida hakanan".
Bata ji dadin ta koma gidan da yace ba dan ita kam tsoron mutanen gidan take ji ganin a tashin farko da ganin ta basu karɓe ta ba se ma rigima da fitina da ta tashi, bayan haka kuma ga zaman kadaici, a Ifty se 4pm zasu taso makaranta dole se ita kaɗai zata wuni a gidan.