Sashe 32
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta na gama faɗa ta wancakalar da hannun Nuriyya da jikin ta ya ɗauki ɓari da tsumar kalaman salma, bata taba tunanin yarinyar nada baki haka ba, a yadda ta ganta ranar da suka tare ta ta zata ko da an sa mata yarda a baki bazata ciza ba, yadda ta farfada mata maganganu batare da ta yanka ba ta zata haka take bata iya kare kanta, ashe lambo tayi, ashe lumbu lumbu tayi musu suke mata kallo kamar dan Zomo se gashi ta bayyana gare su a yar damisa.
Tabbas ba zata bar ta ba, ba zata taɓa barin ta taci bulus ba, yanzu aka fara wasan kuma se ta tabbatar tasa ta lashe aman ta, badai ita Nuriyya ta faɗa wa wannan kalaman ba, to ai in tasan wata bata san wata ba.
Tuna hakan yasa ta saki murmushi wa salma da har lokacin take tsaye gaban ta tana bin kowane move da canjin yanayin fuskar ta da kallo, hannu ta kai gaban fuskar salma ta yi das das dashi irin mu zuba mu gani.................âœðŸ».
Ouummey 📚âœðŸ».
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 022 [ 12/10/2022 10:44 AM ]
★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★
_*PAID BOOK*_
Story/written by Ouummey.
Wattpad @ouummey.
From The author of:
*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*
            Paid page 022
_________________________📖 Bata kuma cewa komai kan Daddy ba suka cigaba da hirar su cikin kaunar juna kamar yadda suka saba, suna ta bata labarin Daddy ya Kai su zoo, Daddy ya Kai su park, Daddy ya siya musu icecream, Daddy ya siya musu chocolate and many more.
Tun tana iya gane me suke fadar an siya musu har ta koma ba abinda take ganewa face sunan Daddy din da suke ta ambata.
Tagumi kawai tayi tana bin su da kallo a ranta kuwa wani sashi na farin ciki da hakan ganin yadda yau yayan ta suka samu soyayyar uba abun da suka rasa tsawon shekarun su biyar sedai kuma ta wani bangaren fargaba ne zokar na ganin dagaske fa mutumin nan yake ya shirya kwace mata Æ´aÆ´a.
.....'Ba wanda ya isa ya kwace Æ´aÆ´an ki a hannun ki se Allah, kauna ce kawai yake nuna musu fisabilillah amma ba da wata manufa ba, da ga ni yana da son yara ne, ke baki ji sunan sa ba ma, Abu Aulad!'.....
Wata zuciyar ta faɗa mata haka, se taji ta yarda da hakan har kuma hankalin ta ya ɗan kwanta da har ta saki jiki cikin su Ifty suka yi ta shirmen su tana taya su, hakan kuma ya ƙarawa Ifty kwarin jiki dan ba zaka taɓa cewa bata da lafiya shekaran jiya ba.
Da rana kam bata yi girki ba, sakwarar da tayi wadda ba wanda ya taɓa se ita kaɗai da taci ta dauka ta ɗumama musu dan a fridge tasa ta har da miyar ganin basu da niyyar ci a jiyan duk da cewa bata ma tunanin miyar zata yi matsala sedai ko farfesun kayan cikin.
A tsakar dakin suka baje suka ci abincin su bayan ta nade Centre carpet din dan kar su bata shi da miya.
Wunin ranar tayi shi cikin jin dadi tare da yan ƴaƴan ta a jikin ta, bata tashi daga cikin su ba se after four sannan ta shiga ƙoƙarin ganin me zata dafa musu da daddare, tuna cewa be ci tuwon da tayi rannan ba yasa yanzu ma tayi tuwon amma wannan karon na semovita ne ba shinkafa ba, miyar taushe tayi wadatacciya da taji gyaɗa se tashin ƙamshi take yi.
Tana gama jerawa ta dan ƙara gyara falon dan ya ɗan yi datti saboda dabdalar wasan da suka yi a cikin sa, tana gama wa ta kunna turaren wutan ta me ƙamshi a burner sannun taja twins bedroom.
Wanka tayi musu ta shirya su cikin three quarter red jeans da farar t shirt daidai jikin su, a wajen siyan ire iren wannan kayan wa ƴaƴan ta kuɗin albashin ta yake tafiya, ba wani ƙarfi ne da ita ba se taimakon Ubangiji amma a haka bata siyawa ya'yanta suttura mara inganci, tafi ganewa ta siya abu me tsada da ze zauna a jiki yayi kyau haka kuma ba wai daga sawar farko ya lalace ba, shiyasa majorityn kayan su designers ne masu ɗan karen kyau.
Tana gama shirya su ta bawa kowacce hijab kan tayi sallah dan anyi kiran sallar magrib wasu masallatan ma har an idar, wanka tayi itama ta gyara jikin ta kana ta saka doguwar rigar ta ja me touches din fari, jan ribbon ta sa ta kama sassalkan gashin ta me matsakaicin tsayi dan da kaÉ—an ya wuce kafaÉ—ar ta sedai bakikirin ne gashi da cika da kalli tun bare ma in yaji mai wanda hakan ke É—aukar idon wanda ya kalla.
Farin scarf ta ɗaura a kanta sannan ta ƙarasa gaban mirror ta dau turaren ta ta feffesa tare da wadata cat eyes din ta da bakin kwalli me kyau, bayan haka lip gloss da powder kaɗai ta saka amma ba ƙaramin kyau tayi ba, kyan ma irin special kyau ba wai gamagari ba.
Kallon kanta ta shiga yi tana tunanin anya ta fita da wannan rigar ko kuwa dai ta canja kaya?, Ba wani abu rigar tayi ba dan bata kama ta ba asali ma loose ce Wanda mafi yawancin kayan ta haka suke se ko atamfa, yadin ne kawai me É—an rawa hakan yasa yake bin jiki.
Gaban wardrobe ta koma zata canja kaya se kuma zuciyar ta ta dakatar da ita
..'ba wani kaya da zaki canja, ai shima haka yake yawo da Three quarter wai shi me gida ba za'a takura masa ba, ai kema bake kika ce ya aure ki ba dan haka ba zaki takura kan ki ba....
Da wannan tunanin ta juya tare da saka wadataccen hijab din ta na sallah ta gabatar da magrib É—in ta, azkhar da tasbih É—in da ta saba tayi ta gama sannan ta fito falo wajen twins dake zaune suna wasa.
Bata ko kai ga zama ba shima ya turo ƙofar falon ya shigo da takaitacciyar sallamar da iya shi kaɗai yaji kayar sa, kafin ma ya ƙarasa shigowa yaran sun tafi da gudu sun dane shi hakan yasa ya saki ledar hannun sa ya tare su tare da daga su a tare ya rungume.
Be san wane irin so ne ba yake wa Æ´aÆ´an nan, abu É—aya ya sani yana jin su a can karkashin zuciyar sa, cikin jinin sa, ruhin sa kai komai ma na jikin sa.
Yana ɗauke da su ya durƙusa ya ɗau ledar da ya saki tare da ƙarasawa kan three sitter ya zauna ya zaunar dasu a jikin sa, ledar ya buɗe ya shiga firfito da kayan ciki wanda suka sa twins sakin ihun murna.
Kayan wasa ne ya siyo musu ganin basu da ko É—aya dan salma bata ma bari su fita wani wasa, kullum suna tare da ita a daki suna hira ko karatu shiyasa yanzu da suka ga wannan bakin su kamar ya yage dan dariyar murna.
Baby doll ne manya manya guda biyu duk mata, irin su ɗaya sedai kayan jikin su ne suka bambanta, Ifty ta dau me blue ɗin gown ita kuma Ibty me pink, ragowar kuwa tarkacen kayan saitin gado da kujerun wasa ne, motoci, jirage har dasu jirgin ƙasa.
Daga inda take ta kame ta kasa motsi, idanun ta kuwa ko ƙifta su bata yi daga kan sa tun lokacin da ya fito da baby dolls din nan har zuwa yanzu da ya sauka kasan carpet cikin su yana haɗa musu train din tare da kunna shi ya fara tafiya, ihu suke yi cikin jin daɗi shikuma se murmushi yake yi koma tace dariya dan hakwaran sa gaba ɗaya na waje ne abinda bata taɓa gani ba se yau, yau ɗin da yake tare da ƴaƴan ta.
Wasu irin hawaye ne da bata san na mene bane suka cicciko idanun ta, gaba ɗaya she's speechless, tun da yaran nan suka zo hannun ta ake nuna musu so da ƙauna, misali mutanen ƙauyen su baba Husaila, ga Mama Hadiza principal, ga Kuma Hajiya me gidan haya amma babu wanda ya taba nuna musu zurfafaffiyar kaunar da lokaci guda taji zuciyar ta tayi amanna da ita kamar shi, tsantsar soyayyar ƴaƴan da ta hango cikin idanun sa da ayyukan sa yasa taji kamar zuciya ta na narkewa a tsayen da take.
A hankali ta lallaɓa ta kai zaune kan kujera mafi kusa da ita sannan ta fara sauke numfashi da sauri da sauri wanda ta riƙe, se da ta tabbatar ta dawo daidai kafin ta sulale ta zauna kusa da Ibty wadda ke hannun daman sa, Muryar ta can ƙasa saboda sanyin da tayi
"Sannu da zuwa Daddy".
Be yi niyyar kallon ta ba amma jin sunan da ta kira shi dashi ya tilasta masa kallon nata.
Cikin tsakiyar golden cat eyes din ta da suka sha kajol ya sauke nasa, ba tun yau ba yake son sake ganin ƙwayar idanun ta, duk da ya tabbatar ba bakake bane amma be san wane kala bane dan bata bari su haɗa ido shiyasa yanzu ɗin ya tsai da idanun sa cikin nata yana faman karewa idon ta kallo.
Lumshe ido salma tayi dan ba zata iya cigaba da kallon shi haka ba, wanda tayi ma ji tayi gaba ɗaya kamar ya sa ƙaƙƙarfar igiya ya ɗaɗɗaure mata jiki haka kuma kafufuwan ta ji take kamar an sa gatari an sassare mata su, inda Allah ya taimake ta tana zaune ne da tsaye ne kuwa ta tabbata ba abinda ze Hana ta zubewa.