← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 44

Sashe 15

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jiri yake gani dan rabon shi da abinci tun na safen jiya kafin su tafi ƙauye ga kuma rashin bacci sedai kasancewar tsayayyen namiji ba wanda ze fahimci hakan se wanda yayi masa sani na sosai.

Wata jallabiyar ya canja kawai ya É—au key É—in motar sa zuwa gidan su, É—auko ta ze yi dan se yayi hakan hankalin sa ne kwnata, mutanen gidan su are so cunning, gwara tun kafin su farga yayi outsmarting É—in su ya shayar dasu mamaki ya kuma basu tsoro ba kuma ta kowace hanya ba se ta kawo macen da ya nema wa kan sa auren ta cikin gidan.

Ya sani in da mace a tare dashi abubuwa da yawa zasu masa sauƙi sedai matsalar shine shin itama irin su ce, wane assurance yake dashi na ba zata zama kamar su ba, shin in aka mata tayi da zunzurutun kudi ko matsayi zata karɓa ko kuwa?!.

Wannan sune tarin abubuwan da tuntuni suke hana shi aure sedai a yanzu da yayi ba wai ze saki jiki da ita bane, hasalima auren su na da wa'adin da ya É—ibar masa wanda yana cika ze sauta, zaman sa shi kaÉ—ai ya fiye masa dan be yarda da kowa ba baya kuma jin ze yarda É—in.

Yaro ya samu ya aika gidan, tana cikin sawa Ifty rigar school ta jiyo Muryar yaron na faÉ—in aiken da aka turo shi

"Wai salma ta fito inji Abdallah".

Sedai rigar ta kubce ta faɗi daga hannun ta saboda yadda zuciyar ta ta doka da jin sunan sa, hannun ta na rawa ta sake ɗaukar rigar ta shiga kici kicin sa mata sedai ta kasa saboda ruɗewar da tayi, Hajiya ce ta amsawa yaron da gata nan fitowa saboda jiya ta zauna tayi mata bayanin komai dan kamar mahaifiyar haka ta ɗauki Hajiya saboda ba ƙaramin taimako tayi mata ba a rayuwar ta.

Ɗakin Hajiya ta shigo ta karɓi shirya Ifty dan tuni ta gana da Ibty

"Je ki bashi uzuri daga nan ki nemo yara su fara fitar miki da jakunkunan, in an kwana biyu insha Allah zan zo in ga mazaunin ki, tashi kije".

Jiki ba laka ta fita, zaune cikin motar ta same shi ƙafar sa duka biyu a waje ya lumshe idanun sa tare da jingina kan sa da makarin kujerar, seda ta tattaro duk dauriyar dake gare ta kafin ta iya gaida shi

"Barkada safiya".

Saukar Muryar ta yasa ya buɗe idon sa, kallo ɗaya yayi mata ya kau da kai tare da maida ƙafafun sa cikin motar ya fara ƙoƙarin kunna ta

"Kayi haƙuri Ban ƙara sa shirya Ifty ba amma yanzun nan zamu ƙarasa, Bari in Sami yaro ya fitar min da jakunkunan".

Fasa kunna motar yayi ya koma ya kwanta kamar ɗazu ita kuma ta matsa ta sami wani almajiri suka koma ciki tare, ko da ta shiga tuni Hajiya ta gama shirya Ifty tare da haɗa musu launch box ɗin su, manyan jakunkunan kayan su dake shaƙe ta fara jawowa tana fitarwa tsakar gida almajirin na fita dasu har suka gama, kallon ɗakin take cike da matsanancin kewar sa da zata yi kafin kuma ta maida kallon ta kan Hajiya, matar da tayi mata halaccin da har abada ba zata manta ba, a rayuwa da ita da bana Husaila sun mata abinda in har ta manta to ita ɗin butulu ce cikakiya.

Nasiha sosai Hajiya ta yi mata da har tasa ta kuka ba dan komai ba se dan kewar mahaifiyar ta da kakarta da ta taso mata, ta sani da suna nan su zasu yi mata wannan nasihar.

Haka Hajiya ta rakata har mota, ko da suka je tuni ya zuba jakunkunan a booth É—in motar sa ita kawai yake jira.

Duk yadda yake moody be san lokacin da ya saki fuska ba da Ifty ta ƙarasa tana ɗane shi Ibty kuma na gaida shi, haka ya ɗauke su duk biyu ya riƙe yana kallon su cike da shauƙi yana sauraren shirmensu har Hajiya ta gama mata nasihar da zata yi suka idasa bakin motar, har ƙasa ya tsugunna ya gaida Hajiya abinda yayi salma matuƙar daɗi a rai.

Hala suka É—au hanya zuwa gidan da bata sani ba tana cike da kewar rabuwa da Hajiya da ragowar Æ´an uwan zaman hayar ta da basu san da maganar auren ba ma se yau da safe amma duk da haka suka bita da fatan alkhairi.

Har bakin ƙofar party ɗin mahaifin sa ya kai motar sannan ya fita ya zagaya ya buɗe mata itama ta fito a ɗarare sannan ya buɗe wa su Ibty baya suka fito, hannu yasa ya ɗau Ifty yayinda ya riƙewa Ibty hannu ya nufi falon mahaifin nasa ta rufa masa baya itama.

Gana É—aya mutanen É—akin suka zuba musu ido zuciyoyin marasa gaskiya na dukan uku uku, masu gaskiya kuma na musu kallon rashin fahimta.

"Barka da safiya baba, ga salma matata da Æ´aÆ´an ta kuma nawa".

A zabure mutane shida dake falon suka miƙe tsaye kowanne da kalar tambayar da yake jefowa

"What?, Me?, Kutumar uba?, Mata?, How comes?, Haba da Allah!.

Wannan sune ruwan tambayoyin da suka dinga yawo a falon cikin ihun muryoyi daban daban yayinda Abu Aulad ya saki hannun Ibty ya saka hannun ya jawo salma cikin jikin sa ya rungume.........................✍🏻.

Tooooooooh jama'a, gamu a ƙarshen free page da izinin Ubangiji, ko yaya paid pages zasu kasance?!.

Shin wacece Abu Aulad ya karyawa hannu jiya da dare?!

Wacece shuraiha?, Wai ma tsaya ita kanta Hajiya babbar wacece, meye alaƙarta da Abu Aulad?!

Jarumi, jarumi!, Shin kun Tuna shi?! Wanne shi?.

Nuriyya ƙanwar nafisa ƴa a wajen Anna, ko meye ƙudurin ta kan Abu Aulad?!.

Yace be yarda da kowa ba se kan shi kaÉ—ai, what about Haisam?!.

Haisam, Haisam, anya shima babu wani ƙulli kuwa a under sunan nan?!.

"Wai ma ku tsaya, wace irin rayuwa ce Abu Aulad ya taso a cikin ta, meye tarihin wannan gidan, wane irin bahagon rayuwa ake yi a cikin sa.

Duk ma ba wannan ba, yaya rayuwar auren Abu Aulad da salma zata kasance, me kuke hangowa, gashi dai auren ya ƙayyade masa wa'adi, shin kuna ganin ze sake ta?!.

Ni abinda bangane ba shine shi kan sa Abu Aulad É—in waye shi, ina mahaifiyar sa, anya baba mahaifin sa ne kuwa, to in ba mahaifin sa bane waye mahaifin nasa?!.

Shin ina labarin dangin mahaifiyar Salma, zata haÉ—u da dangin mamanta ko kuwa?, Baba Husaila da mama Hadiza principal, shin shikenan an rabu ko kuwa akwai wata rawa da zasu taka a rayuwar salma nan gaba?!

Duk amsoshin wannan tambayoyin na cikin paid pages, sister kar ki yadda ayi tafiyar nan bake domin na tausaya miki rashin da zaki yi dan littafin ze tabbatar da sunan sa akan ki wato ANJANE (RASHIN SANI) dan da kin san irin nisa da ƙarkon da tafiyar zata yi da ba zaki yadda a yi ta bake ba,!.

Ga duk me buƙatar yin payment ɗin sa ne bi ta wannan procedure ɗin,
₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 011 [ 12/3/2022 3:45 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

                    Paid page 011

_________________________📖 Kallo na sosai dattijon ya bi fuskar Abu Aulad dashi na tsawon lokaci kafin ya maida kan fuskar salma da har lokacin take cikin jikin Abu Aulad ɗin sai dai kanta na ƙasa ne haka kuma jikin ta na ɗan rawa da ba kowa ke ganin haka ba se shi da take jikin sa.

"Ban fahimci zancen ka ba Abdallah".

Duk da murmushi be kasance daya daga cikin abinda yake halayyar sa ba amma se da ya ya ƙoƙarta wanzar dashi a fuskar sa a lokacin, tafiya ya fara yi da ita a jikin nasa har zuwa kan three sitter dake falon ya zaunar da ita shima ya zauna gefen ta tare da ɗora Ibty da Ifty kan cinyar sa, a nutse yasa dogon hannun sa ya ratsa jikin salma ya manna ta da jikin sa sannan ya fuskanci mahaifin sa cikin danne nauyi da yar kunyar abinda yake aikatawa sedai hakan ya zama dole in har yana bukatar fahimtar murdaddiyar  rayuwar sa

"Sunan ta salma kamar yadda na faɗa maka baba, jiya aka ɗaura mana aure da ita bayan soyayyar da muka jima muna yi, wannan yaran nata ne dan ta taɓa aure a baya, itace dai wadda mukayi magana a kanta shekaranjiya wadda muke tare a newspaper dinnan".

Ya ƙarashe bayanin da ya kai da kyar tare da sake matsar salma da har lokacin kanta ke ƙasa, wani irin rawa na sosai jikin ta ya ɗauka jin bada sanin mahaifan sa ya aure ta ba haka kuma ga a yanayin da yake musu bayani wanda ita sam bata ga dacewar abinda yake yi ɗin ba.

"Sam ba zata yiwu ba, wallahi ba zata saɓu ba wai bindiga a ruwa, wannan auren karya ne, kai koma gaske ne wallahi se an kunce shi".

Hajiya Babba ke faɗin haka cikin fadan tashin hankalin da take ciki, wannan wani irin rainin hankali ne yaron nan ya zo musu dashi, yana nufin yayi aure bayan yasan ta riga tayi masa mata har ma gata a gidan, aikuwa sedai ayi wacce za'a yi dan ba ta yarda da wannan auren ba, ba ta kuma karɓe shi ba dan haka se an warware shi, wai imma da gaske ne kenan.

Hayaniyar yadda kowa ke reacting kan auren na Abu Aulad yasa baba tsawatar musu, dole suka yi shiru ba dan sun so ba sedai suna jiran suji me zai ce kan wannan tatsuniyar.
Chapter 15 · 0% Book details