← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 44

Sashe 31

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin gaggawa ta janye nata idon dan se taji kamar ana É—aÉ—É—aure mata jiki da ta kalli idanun sa da har yanzu basu koma launin su na ainahi ba sedai sun rage jajir É—in da suka yi, shi kam ido kawai ya zuba mata yana kallo cikin ran sa yana ayyana wane irin sakaci yayi da har yarinyar nan ke neman raina shi, raini mana tunda gashi har ta kai su ga ta fara shigo masa daki nan gaba kuma ai se kan bed din sa daga nan kuma Allah kaÉ—ai yasan me zata so yi masa.

Wani irin haɗe rai yayi wanda bata taɓa ganin haka daga gare shi ba kira sunan ta karo na farko tun sanin ta da shi dan hatta a office baya kiran ta da sunan ta sedai miss.

"Salma". Da gaggawa ta ɗago tare da ƙure su da golden brown eyes din ta dake wani maiƙo maiƙo kamar wadda ke neman tara hawaye sedai ba hawayen ba ne a haka idanun ta suke, wannan karon shi yayi azamar janye nasa kafin ita ta sunkuyar da kai, seda ya kausasa har she da Muryar sa kafin ya fara magana

"Ko da wasa kar in Kuma ji balle gani, wannan ya zamo na farko kuma na karshe da zaki shigo min bedroom, bana buƙatar sake ganin ko da alamun ki ne a daki na balle ke da kan ki, kome kike bukata ko son sanar da ni zaki iya jira har in Fito".

Ƙasa ma tunanin komai salma tayi cikin ran ta, me wannan mutumin yake nufi da maganganun sa, ko me take buƙata ta jira har ya fito, to wa ya faɗa masa ita akwai abinda tazo nema ko bukata a wajen sa?, Ita ɗin ba me roko bace balle yace kudi ko wani abu tazo tambayar sa, ita ba cusa kanta take wajen sa ba balle ya nemi faɗa mata magana, dan haka cikin muryar dake nuna taji zafin kalaman sa batare da ta kalle shi ba tace

"Ni ba abinda nazo nema ko bukata a wajen ka, na ga tun da ka shiga ne tun jiya da magrib baka fito ko yin Sallah ba shiyasa nazo duba ko lafiya dan sauke hakkin da Allah ya dora min, amma kayi haƙuri insha Allah ba zaka kuna gani na ko a bakin kofar dakin ba balle cikin sa".

Tana gama faɗa ta fita daga ɗakin da sauri idanun ta na kawo ruwa, ita kam ta tsani wulaƙanci da disgi abinda shikuma ta lura ya fi kwarewa akai kenan dan haka daga yau zata nuna masa ita ɗin macece me daraja, in ya Saba mata na bin sa yake tunanin itama haka to tabbas yayi kuskure dan ita ɗin da darajar ta da ajin ta ba zata bari ya wulaƙanta ta ba.

A fusace ta zauna kan gadon tana hararar bedsheet din dake shimfiɗar kamar shi yayi mata laifin kafin kuma ta tashi ta shiga ayyukan da ya kamata, se da ta gama breakfast ta jera kafin ta shiga ƙwalawa su Ibty kira tana hararar bakin kofar dakin nasa cikin ranta kuwa se gunguni take yi, yace kar ta kuma zuwa masa daki yanzu kuma ya wani riƙe mata yara a ciki, ai dai ya'yan ta ne ba na wani ba dan haka se suma ya bar mata abin ta.

Cikin haka ya fito hannun sa riƙe da kowacce, yayi wanka har ya shata kaya zuwa three quarter da farar body hug na zaman gida, ya riga ya saba da zaman sa haka cikin sashen sa dan haka zuwan ta baze sa ya sauya komai ba dan shikam ba zata takura masa ba a kawai.

Kan table É—in ya zaunar da twins kana shima ya zauna, kamar ta share shi se kuma taga be kamata ba dan haka ta yi serving din su ta zauna ta cigaba da cin nata dan lokacin da suka fito har ta fara cin nata ganin sun ki fitowa.

Yau kam su ukun suke ci tare, in ya bawa Ibty se ya bawa Ifty su ma se duk su bashi, gaba É—aya se yaji zaman wajen ya ishe ta ganin yadda suka ware ta ita kadai uwa mayya, a ranta har haushin twins din duka take ji ganin yau har Ibty suka wani manta da ita.

Bata tsaya sauraren su ba tana gamawa ta wucewar ta bedroom cikin ranta tana faÉ—in Allah ma dai yasa su Æ´an biyun ya'yan ta ne ba nasa ba da ya tura mata haushi ai duk da yanzu ma ta shaka.

Bata san fitar su ba se fitowa tayi ta tarar basa nan, duk yadda tace ba zata kuma zuwa kofar dakin sa ba kasawa tayi da taga har sha biyu bata ji motsin su ba, a hankali ta buɗe ƙofar tare da dan zura kan ta ciki sedai wayam ba kowa, har ta juya zata fita se kuma ta kuma kallon dakin, a gyare yake sedai ba tsaf ba, kamar ta gyara se kuma ta tuna gargaɗin wulaƙancin da yayi mata ɗazu dan haka taja tsaki tare da rufe masa ta koma falo.

Wato dai dagaske yaran nan sun manta da ita tun da gashi har sun fita batare da sun sanar da ita ba, aikuwa zasu sani dan se ta zane su zasu dawo su same ta ne.

Bacci ta kwanta abinta dan ta gama gyara komai tun da safe dan haka ba aikin da zata yi kuwa, abincin rana kuwa ba ma zata fara ba tunda masu ci É—in ba sa nan, ita kuma bata jin yunwa bare ta dafa.

Nan kan sofa tayi baccin ta cikin kwanciyar hankali batare da fargaba ko tunanin wani abu ba da har aka bude kofar aka shigo bata sani ba saboda kofofin sa ba irin masu muguwar karar nan bane.

Tsaye Nuriyya tayi a kan ta tana bin ta da mugun kallo idanun ta cike da tsantsan kishi, ƙyashi hadi da hassada ganin yadda take baccin da kallo ɗaya zaka mata kasan hankalin ta a kwance yake ba ta tare da ko wace irin damuwa.

Cikin fushin zuciyar da ya tuko ta ta ƙarasa tare da sa hannu ta finciko ta, hakan yasa ta fado kasan kujerar dan bacci take bata san meke faruwa ba balle ta kare kanta.

Cikin baccin da yayi matukar mata daɗi taji an wani kwashe ta an watsar hakan yasa ata shiga ƙoƙarin buɗe idanun ta, bata gama dawowa hayyacin ta ba zafin buguwar da kanta yayi da carpet ya ratsa kwnayar ta da ya tilasta mata wartsakewa nan take.

Ganin mace tsaye a gaban ta yasa ta miƙe da sauri tana bin Nuriyya da kallon Lafiya?, Ke kuma wace kafin bakin ta ya furta abinda ke ranta

"Baiwar Allah lafiya zaki shigo min gida ba neman izini ki kuma zo ki min tsaye akai kamar kin bani ajiya ko naci miki bashi ban biya ba?".

Tana sane ta fadi haka dan ta gane Nuriyya, itace suka tare ta ita da wata yarinya lokacin da ta dawo daga aiki, itace ta nemi zagin ta koma tace ta zage ta a fakaice da kalaman ga masu harshen damo dan haka ta sake ɗaure fuska kamar bata taɓa sanin kalmar dariya ba dan kar ma Nuriyyar ta kawo mata wani iskanci ko raini.

"Baiwar Allah tana ƙauye, lafiya kuma to babu dan baki biyo hanyar lafiyar ba balle har ki tambaye ta, bashi kuwa ai base na faɗa ba kema kin san akwai shi kuma dalilin shi ya kawo ni har nan gurin, haɗe rai ko wani abu da zakiyi baze sa na fasa isar da sakona gare ki ba duk da na fahimci karamar ƙwaƙwalwa gare ki da har kika kasa fahimtar sako na tun a karon farko, well, ba damuwa zan sake maimaita miki amma fa for the last time dan in har kika bari na kuma zuwa sashen nan ba gargadi zan yi ba cika aiki zan yi".

Kallon sama da ƙasa salma tayi mata kafin ta koma kujerar ta zauna abin ta

"Allah ya baki lafiya". Abinda ta faÉ—a kenan wanda ya kular da Nuriyya ya kuma fusata ta to the core bata ma tsaya wani tunani ba ta daga hannun ta da nufin kashe fuskar salmar da mummunan marin da ze tafi da gani da jin ta yadda ko ance gaba ta sake mata irin wannan iskancin ba zata kuma ba.

Sedai tuni Salman tayi zafin nama da azamar riƙe mata hannu batare da ko kusa da fuskar ta ya kai ba, kyakkyawan murmushin ta ta sake da yake ƙara bayyana tsantsar kyan da Allah ya bata ya ke kuma ƙara mata kwarjini, dayan hannun ta da baya rike da na Nuriyya ta daga ta kai daidai fuskar Nuriyyar ta shiga kada shi

"Kar ki fara wasan da baki ko tanadi players ba a cikin sa, kar ki ɓallo ruwan da baki da abin tare shi balle sa ma masa matsuguni haka kar ki sake ki yi tunkari mayunwaci namijin zaƙin da ya daɗe a yunwace dan yin hakan tamkar wasa da rayuwar ki ne dan kin san in wannan zaƙin ya riƙe ki da iya faratan hannu da kafar sa tabbas sedai wata ba ke ba, to kamar wannan namijin zakin mijina yake komawa duk in akayi yunkurin taɓa ni, yi tunani ki auna meze yi in aka tabani in har se zama kamar wancan zakin saboda kawai anyi yunkuri.

Ke ɗin shashasha ce da har yau dakikiyar kwakwalwar ki ta kasa baki cewa mijina baze taɓa auren ki ba domin baya cikin tsari da layin irin matan da yake so yake kuma bukatar rayuwa dasu, in ke me tunani ce se ki lissafa shekarar ku nawa cikin gida ɗaya amma be taɓa daga ido ya kalle ki da wata manufa ba, ke in ƙarƙare miki zance in za'a ɗorawa Abu Aulad wuka a maƙoshin ace ya siffan to ki sedai a kar shi, the sooner you realise the bitter truth the better for your life lady".
Chapter 31 · 0% Book details