← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 44

Sashe 25

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta daÉ—e tana addu'a cikin sujjada da kuma bayan ta idar, kukan ta take kaiwa wajen da zata sami magani musamman yanzu da matsalar ta suka karu dan ta tabbata wannan auren da aka yi masa ba iya shi kaÉ—ai ze zamewa matsala ba har da ita.

Bata san wace yarinyar da ake batun an aura masa É—in ba sedai tasan tun da ta biyo ta bangaren Hajiya mutunci kam se in Allah ne yayi tana da rabo, kwana biyu da tayi cikin gidan sosai ta fahimci matar bata san wata kalma da ta danganci mutunci ba ko kadan haka ma kuma Æ´aÆ´an ta dan duk sun gwada mata hali ta gani, namijin ne kawai shi kuma ba abinda ya haÉ—a ta dashi balle taga nashi kalar rashin darajar.

Praymat É—in ta ninke tare da maida ta inda ya kamata kana ta shiga ayyukan gidan kamar yadda ta saba, tana gamawa ta shiga hidimar É—ora breakfast Shima ta jera sannan a gurguje ta shiga ta tashi yan biyu tayi musu wanka tare da shirya su ta bar su kan suyi sallah ita ma ta shiga nata wankan.

Cikin gogaggun uniform din ta set uku ta dau ɗaya ta zura tare da jawo Ash and black ɗin kimono ta ɗora kan kayan, ba ƙaramin kyau tayi ba haka kuma zagayayyar fuskar ta ta fito sosai.

Bata ga su Ibty a dakin ba tasan sun fita falo ne dan haka ta dau handbag din da zata tafi da ita kalar silvern takalmin ƙafarta wedge me fuskan slipper.

Kamar yadda tayi hasashe kuwa falon ta same su zaune kan sofa Ifty kwance kan cinyar Ibty dan har yanzu jikin ta ba wani kwari sosai, zama tayi gefen su ta dau Iftyn ta maida kan cinyar ta tare da duban Ibty

"Maza je ki kira Daddy yazo muyi breakfast".

Tashi yarinyar tayi zuwa dakin daddyn nasu dadai yana bude kofar ze fito, murmushi ya sake mata tare da tsugunnnawa ya buÉ—e mata hannun sa ta shige jikin sa ya mike da ita,

"Good morning Daddy".

"Good morning babyn Daddy, hope kin tashi lafiya".

"Lafiya lau Daddy Amma Ifty Bata da lafiya".

"Soobhanallah, me ya same ta?, tana ina?".

Ya tambaya a rude dan kwana ukun da suka yi tare ba ƙaramin shiga ran sa yaran suka yi ba tun bare ma Iftyn dan ita tafi shige masa ita Ibty ya fahimci momma's girl ce.

"Fever ne Daddy, tana wajen momma a parlor".

Falon ya shiga takawa yana ƙarasawa kuwa idanun sa suka sauka kan su har lokacin suna zaune kan sofar Salma rungume da Iftyn a ƙirjin ta.

Sauke Ibty yayi ya ƙarasa gaban Salman tare da duƙawa yasa hannu ya cire Ifty a jikin ta sannan ya nemi waje ya zauna ɗauke da ita ya shiga tattaba jikin ta wai ko zeji zafi sedai babu se dan dumi Wanda normal ne a jikin kowa.

"Sannu Angel, how are you feeling?".

A hankali ta bashi amsa da
"Fine Daddy, good morning".

"Taci abinci ne?".

Kallon sa salma tayi jin abinda ya faÉ—a sedai se taga hankalin sa da idon sa baya kanta yana ga Ifty ne, kamar tayi masa shiru se kuma ta bashi amsa

"Dama kai muke jira muje muci".

Bece komai ba ya tashi zuwa dining ɗauke da yarinyar a ƙirjin sa, kujera ya sa kafa yaja ya zauna itama ya gyara mata zama kan cinyar sa, itama salma miƙewa tayi tare da riƙe hannun Ibty suka ƙarasa dining ta ja mata kujera ta zauna sannan ta shiga serving din su.

A hankali yake bawa Ifty shima yana ci dan yau salma bata jira ya bata umarnin dandanwa ba, tun kafin ta zuba wa kowa tayi spoon uku a gaban sa Sannan ta zuba masa ta zubawa kanta haÉ—e da Ibty.

Itama kan cinyar ta ta ɗora Ibty tana bata tana ci har suka gama, sun riga su Abu Aulad gamawa saboda rarrashi da lallaɓa iftihal da ya zauna yi, ba kaɗan ba girma da darajar sa suka karu a idanun salma ganin wannan special care din da yake bawa yarta, aka ce me da wawa to gare ta itama haka ne.

A kafada ya saba iftihal tare da ɗaukar basket ɗin ta yayi waje itama suna rufa musu baya hannun ta riƙe dana ibtisam dayan kuma basket din Ibtyn da handbag.

Ita ta rufe part din dan shi har sun É—an yi nisa, itama daukan ibtisam tayi dan kar yarinyar taji ba daÉ—i duk da ma dai ba ruwan ta amma dai ai yan biyu ne.

Mugun tsaki sumayya da ta fito zata tafi wajen aiki ta saki kafin ta bi bayan sa da

"An dai yi asara, duk jiji da kai da takama da dukiya aka kare a bazawara me yaya biyu, mijin tace kawai".

Be ko kalle ta ba balle ya nuna ya san tana yi dan ita kam ya san bata ƙi a zauna ayi ta hayaniya ba shikuma sam hakan ba dabiar sa bace, wanda yake yi ma yanzu kure shi suka yi.

Bayan motar ya buɗe yasa Ifty tare da basket din ta daidai lokacin da su salma suka ƙaraso ya karbi Ibty a hannun ta itama ya sata sannan ya rufe, zagayawa yayi ya buɗe ma salma front seat, wani dindirindindin haka taji lamarin a ranta, yau ita ake budewa mota, kuma wai Mr Gamji ke buɗe matan, lallai Allah me iko.

"Shiga muje mana".

Da sauri ta dawo hayyacin ta jin maganar sa cikin kunne ta ta shiga shi kuma ya mai da kofar ya rufe sannan ya koma masa side din na driver ya shiga.

Mamaki take yi ganin shi ze tuka motar da kansa abinda ta san ko shi driver ke kai shi office dan ban da ranar da suka je BA MUNI bata taɓa ganin yayi tuƙi da kansa ba tun da take Company ɗin.

A hankali ya kunna motar tare da yin addu'ar shiga abin hawa kana ya juya ta suka nufi gate, tun kan su karasa aka buÉ—e masa kofar dan haka yana zuwa ya fice tare da hawa kan titi.

Hankali kwance yake tuka motar yana yi yana receiving call har suka kai a school ɗin twins, parking lot ya kashe motar tare da budewa ya fito, back seat ya buɗe ya dauki Ifty ya riƙe a ƙafaɗar sa tare da daukan basket din da other hand, ya maida ƙofar da kafar sa ya rufe.

Itama salma budewa tayi ta É—au Ibty da abincin ta ta rufe bangaren suka yi arean class din, har kan chair ya aje iftihal yayi pecking kuncin ta haka ma ibtisam da salma ta aje sannan ya juya ya fita itama tabi bayan sa.

Seda suka hau kan titi sosai sannan yayi magana idanun sa a kan kwalta

"Makarantar ta zama dole ne da se an je ta ko ba'a da lafiya?".

Tasan da ita yake tun da su biyu ne a motar

"Babu inda zan aje ta in bata je school din ba".

Bece komai ba ya maida hankalin sa ga tuƙin da yake yi har suka kai Company, parking yayi aka gama bincike motar sannan ya shige, inda aka saba parking motar shi ya kai motar tare da kashewa sannan ya fita.

Har ya danyi gaba ya dawo side din ta yasa hannu ya buÉ—e mata daidai lokacin da ta gama tusa kimono din ta cikin jaka dan dama abinda ya tsaida ta kenan bata fito ba lokacin da ya gama parking.

Akan idanun Laila da Umah komai ya faru dan fitowar su kenan daga mota suma dake maƙota ne tare suke tahowa a motar Umah dan iyayen ta masu rufin asiri ne akasin Laila da ita ke kula da gidan su dan mahaifin ta bashi da karfi.

Zaro ido Umah tayi ta kalli Laila da ta daskare a wajen, ta gaban su suka wuce batare da kowacce ta iya ƙwaƙƙwaran motsi ba tun balle Laila da tayi mutuwar tsaye, a kusan tare suke tafiya duk da ya ɗan zarta ta kadan dan takun namiji da mace ba ɗaya bane har suka shige main building.

Jijjiga Laila umah ta shiga yi ganin bata ko kyafta idanu, dogon numfashi taja tare da juyowa ta kalli umahmatun

"Da gaske ne abinda ido na ya gane min ko mafarki nake Umah?".

"Aikuwa dai gaske ne Laila dan nima na gani, akan ido na boss ya buÉ—ewa miss Salma mota ta fito ya maida ya rufe kuma suka jera zuwa cikin building".

Laila bata iya cewa komai ba se aniyar zuciya da ta dinga sauke wa akai akai, tsayin lokaci kafin ta É—ago ta kalli Umah a raunane

"Hakan na nufin yana son ta kenan?".

Kau da kai Umah tayi dan a yanayin da lailan tayi magana dole ne ta baka tausayi, sedai ya zama dole ta haƙura ta farka daga mafarkin da take yi wanda take da 99% assurance baze faru ba

"Kin taɓa ganin namiji ya kashe kudin sa ya auri matar da ba ya so, balle kuma mata irin su miss Salma da ba kowa ne namiji ne ze iya tunkarar su ba, kiyi haƙuri ki sawa zuciyar ki salama laila, ki buɗe ido ki kalli zahiri rayuwa ba bandini ba, kina da masu son ki dadai gwargwado kuma dukkan su suna da rufin asiri, akan me zaki zauna kina ɓatawa kan ki lokaci kan wanda be san kina yi ba, na tabbatar miki in da za'a tsare boss da bindiga kan ya suffan taki wallahi sedai a harbe shi dan baze iya ba, kai ko gaban sa aka kawo ki aka ce ya fadi sunan ki na tabbata baze iya faɗa ba dan be sani ba".
Chapter 25 · 0% Book details