Sashe 18
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarfe huɗu daidai ta tashi aiki, office din sa ta shiga ta ajiye masa file ɗin da ya sata aiki a kan shi tare da yi masa sallama ta fice, seda tayi signing out sannan ta fita.
Doguwar rigar ta ta maida jikin ta sannan ta shiga neman napep, sosai yau ta sha wahala kafin ta samu hakan yasa koda taje makarantar twins kusan kowa ya watse saura yan kaÉ—an da ba akai ga É—auka ba.
Da gudu suka rungume ta kamar yadda suka saba itama ta sake ƙanƙame su kafin ta ja hannun su suka nufi gate tana musu tambayoyi kan karatun su.
Yanzu kam basu sha wahala ba suka samu napep, tun da suka É—au hanyar gidan gaban ta ya shiga dokawa saboda firgici da tsoro sedai bata bari yanayin ta ya nuna hakan ba har suka sauka bakin gate.
Kuɗin sa ta bashi tare da ɗaukar basket ɗin yaran ta saka su gaba karasa gaban gate ɗin, a hankali ta shiga ƙwanƙwasawa cikin ɗari ɗari, seda maigadin ya leka ya ga itace kafin ya buɗe musu su shiga.
Tun da ta saka ƙafarta cikin compound tasa addu'ar ta bata amsa ba dan shuraiha da wata mata da ta samu zaune kan fararen kujeru suna magana, kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kan ta batare da ta sake ba, cikin nutsuwar ta suka nufi part din su batare da ta musu magana ba dan nuna wa tayi sam bata lura akwai mutane a ta wajen ba.
Ba wai rashin girmama manya bane, abinda duk ze hada ta da yan gidan ne bata so dan ta fahimci she's not welcomed a cikin su, bare kuma a kallon farko da tayi wa su shuraiha suka yi mata ta ankare da kallon banzan da suke yi musu.
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da suka shiga falon ta maida ƙofar ta rufe, bedroom ta wuce dasu ta musu wanka tare da canja musu kaya zuwa simple gowns na zaman gida da shan iska sannan itama tayi nata.
Kamar su itama gown me saukin nauyi ta zura ta saka hijab suka gabatar da sallar Asr tare da Æ´aÆ´an ta.
Bata tsaya yin wasu dogayen addu'a kamar É—azu ba saboda aikin da zata yi, cartoon din two letter words ta kunnawa twins yayinda ta fice dan fara aikin ta.
Da falo ta fara, duk da ba wani datti ne dashi ba seda ta gyara shi ta share tare da canja fasalin zaman kujerun ta saka turaren wuta me matuƙar ƙamshi irin wanda suka dinga haɗawa suna saidawa dan da wannan sana'ar tayi sponsoring karatun ta.
ÆŠan tsam tayi cikin tunanin ta shiga bedroom din sa ta gyara ne ko kuwa,
'ki tsaya iya matsayin ki salma, ke bawai kamar kowace mace bace a wajen mijin ta dan haka kar ki zarme balle har ki kai kan ki inda Allah ne kai ki ba'.
Cikin yarda da batun da zuciyar ta tayi mata ta wuce kitchen inda ta iske kayan abinci kamar zasu yi magana a cikin store yayinda ragowar kayan haÉ—in ke ajiye a tsakiyar kitchen din cikin manya manyan ledoji.
Ba bata lokaci ta shiga fitar dasu tana ajiye komai a wajen da ya dace, kayan miya da su nama da kifi duk ta haɗa su cikin deep freezer dake kitchen din, seda ta gama adana komai cikin inda ya dace sannan ta koma kan refreshments ta zuzzuba su ya cika manyan fridges biyu dake kitchen dan ba ƙarya kitchen din babba ne dan in bata yi karya ba zata iya cewa ya kai ko ya kusa girman falon.
Jin kiran sallah yasa ta shiga ƙoƙarin sama musu abinci mara nauyi a maimakon da alkubus ɗin da tayi niyyar yi.
Jallof sphagetti tayi da ta Wadata da veggies da fresh prawns, ba tun yau ba take sha'awar yin ire iren waɗan nan girke girken ba sedai dake bata da abun yi dole ta haƙura sedai so da yawa ita take yiwa Hajiya abinci in suna aikin hadin turare hakan yasa ta kware sosai kamar dama shi ta sa bayi kullum.
Cikin plates masu kyau ta zuba musu ita da twins shi kuma cikin wani kyakkyawan warmer me kyau ta Kai dining ta ajiye masa tare da frutta juice.
Seda ta Kai musu abincin daki sannan ta sake alwala suka gabatar da magrib, ba ƙaramin daɗi abincin yayi mata ba dan dama yunwa take ji kamar tayi yaya, da safe bata samu ta karya ba yazo tafiya dasu, da rana kuwa damuwa bata barta ta ci yadda ya kamata ba ga kuma aiki da ta dawo tasha duk ya gajiyar da ita yunwar ta karu shiyasa yanzu ta zage ta cika cikin ta.
Suna gamawa ta maida plate din ta dawo suka shiga bitar karatun da akayi wa su twins, wannan sabo ne da tayi musu tun da suka fara zuwa school, kullum da daddare se sun maimaita karatun da akayi musu biyu boko da Arabia inda take kara fahimtar dasu da kuma yi masu gyara inda ya kamata.
Hadith ta Kara musu guda daya dan sun iya na shekaranjiya da tayi musu, wannan special care da take bawa karatun su yasa suke cikin most talented students na ajin su dan duk wuyar karatu nan da nan suke daukewa, to dama an koya musu ana kuma kan kara koya musu dole ya zo musu da sauki.
Kiran sallar Isha ne yasa suka rufe littafin suka tashi, suna idar da sallah taja su falo ta kunna musu National geography Abu Dhabi saboda Ifty da ta dame ta wai a kunna musu lion.
Sosai itama program din ya burge ta yadda ake haska dabbobin daji kala kala ana kuma highlighting yanayin rayuwar su da abubuwan da suke ci matsayin abinci, gaba ɗaya hankalin ta ta maida kan Tvn dan wasu dabbobin bata ma taɓa sanin akwai su ba se gashi yau ta gan su a Tv.
Yadda hankalin su yayi nisa ne yasa basu ji buɗe ƙofar da aka yi ba balle shigowar sa, ƙamshin sa da ya shige hancin salma ne ya tilasta mata rufe ido tana shaƙar shi sosai kafin kuma a ɗan razane ta maza ta buɗe idon tana rarraba su cikin son ganin inda mamallakin ƙamshin yake.
Kan bayan sa ta sauke idanun ta daidai lokacin da yake dab da isa kofar dakin sa batare da ya kalli ko twins ba balle ita, a ɗan daburce ta gyara zama tare da ɗaukar remote tana rage volume din Tvn sannan ta miƙe tsaye tare da sunkuyar da kai tana faɗin
"Sannu da zuwa"...........................âœðŸ»
Ouummey 📚âœðŸ».
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 013 [ 12/6/2022 11:51 AM ]
★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★
_*PAID BOOK*_
Story/written by Ouummey.
Wattpad @ouummey.
From The author of:
*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*
           Paid page 013
_________________________📖Ba tare da ya kalle ta ba ya amsa tare da shigewa ɗakin ya maida ƙofa ya rufe.
Kau da kanta tayi lokacin da ya rufe ƙofa tana mamakin ko wane irin mutum ne shi kuma oho.
Yanzu kenan da bata lura da shigowar sa ba haka ze shige bece musu komai ba, lallai Allah me halitta.
Kashe Tvn tayi tana hannun su Ibty suka shige ɗaki dan bata san ranar su ta farko ya zama na sun takurawa me gidan, kaya ta canja musu zuwa na bacci ta canja nata itama, fitila ta kashe musu tare da lulluɓe su da spread kasancewar ana ɗan sanyi kaɗan.
Ta daÉ—e bata amu bacci ba yayin da tayi nisa cikin duniyar tunani, ba na komai ba se na makomar rayuwar ta da ta Æ´aÆ´an ta, zuwa yanzu tuni tayi yaki da zuciyar ta ta nemo dakiya ta sawa ranta haka kuma ta fatattaki tsoron da ke ranta akan mutanen gidan.
Ta sawa ranta yin rayuwa da su a duk yadda suka zo mata, zata tsaya ta fahimci kowa ne sannan ta tafiyar dashi ta yadda ya biyo.
Se kusan karfe ɗaya da rabi kafin ɓarawo bacci ya salallabo ya sace ta kamar yadda shi ba ruwan sa da damuwa ko tashin hankali, farin ciki ko wani abu makamancin haka, a kowane yanayi mutum ya kasance to fa bacci ya ƙware a iya sata.
Adaidai wannan lokacin Abu Aulad na kan praymat a dakin sa yana kai kukan sa wajen me kowa me komai me duka, kwata kwata ran sa a bace yake, ba kuma dan komai ba se wata sabuwar tatsuniya da baba ya karanta masa ɗazu, be taɓa jin yana matsanancin kewar mahaifiyar sa ba se yau, ya sani in da tana raye se tayi iyakacin kokarin ta wajen ganin rayuwar sa bata kasance a bigiren da take ba a yanzu.
Duk da yanayin da rayuwar sa ke ciki abu ne rubutacce cikin littafin kaddarar sa da ba makawa se ya faru amma fa tabbas akwai son zuciya da kuma rashin tsoron Allah.
Baze iya cewa ga tsawon lokacin da ya kwashe be yi kuka ba sedai ya tabbatar daga lokacin mutuwar Ummu be kuma kuka irin wanda yayi ba yau, wani irin rauni zuciyar sa tayi lokacin da yake gaban mahaliccin sa, raunin da zece be taɓa jin irin sa ba a rayuwar sa, a yanzu ba shi da kowa se Allah da Manzonsa, mutum ɗaya ce iya nuna wa da kwarin gwiwa cewa nasa ne sedai a yanzu shima ɗin ya zama ba nasa ba, ya zama nasu Hajiya Babba kaɗai da ƴaƴan su.
Baba Ada tsayayyen miji ne a gidan sa haka kuma jajirtaccen uba ne ga yayan sa sedai a yanzu dashi da babu kusan babu bambanci, matan abinda suke so shi suke yi yayinda uwargidan sa Hajiya Babba take abinda taga dama, take shimfida iko da mulkin ta iya iyawa ta kuma ba wanda ya isa ya daga kai ya kalle ta yace dan me se mutum biyu.
Na farko shine se kuma amaryar da baba ya aura wadda bata ko rufa shekara biyu ba a gidan, cikakkiyar yar duniya ce dan zaman kanta take yi har zuwa lokacin da baba ya aure ta.