← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 44

Sashe 10

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nayi aure ina secondary school batare da sanin su ba inda na haifi ƴaƴana biyu, bayan mun gama WAEC muna shirin zuwa gida mijin ya gudu se ni kaɗai na koma da ƴaƴan shine suka shegan ta su suka buƙaci in ba da su akai inda ban sani ba dan gujewa abin kunya acewar da naƙi shine suka bani zaɓin bada yaran ko kuwa barin su nikuma na zaɓi ƴaƴana".

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Haisam da Abdallah inda kowa da abinda yake kitsawa a ransa, ture komai dake ransa Haisam yayi

"Ina ce dai Æ´an garin ku sun san wannan labarin in Kuma na faÉ—a za'a gane ke nake nufi?".

"Sosai ma kuwa".

"Shikenan za ki iya tafiya yadda ake ciki kuma zan sanar dake".

Miƙewa tayi zata fita ya dakatar da ita

"Ji nan, rabon ki da garin naku shekara nawa yanzu?".

"Shekara biyar da watanni".

Da kika shigo garin nan a ina kika fara zama, ko kuwa kuna da Æ´an uwa ne?".

"Sam ban san kowa ba a nan, na fara zama a gidan haya da nake zaune har yanzu".

"Waye yayi sponsoring karatun ki".

"Ni na É—au nayin kaina da sana'ar haÉ—a turaren wuta da na dinga yiwa wata Æ´ar Maiduguri tana rarrabawa a faÉ—in Nigeria gaba É—aya".

"Sunan product É—in fa?".

"Ƙamshin amarya".

"You can go". Fita tayi tana sauke ajiyar zuciya jin wasu tambayoyi daga boss ɗin ta kamar wani ɗan jarida, bata taɓa sanin yana magana haka me tsayi ba se yau, ita bata ga wani point ba a auren ta da suka ce ze yi, ita da sun ƙyale ta dan sam ita aure baya gaban ta balle mazan gaba ɗaya sedai dole saboda ƴaƴan ta da suka kasance mata tana buƙatar garkuwa irin ta ɗa namiji wanda ba ta inda zata sama musu ita se ta hanyar auren.

"Amma meye point a tambayoyin da ka dinga yiwa yarinyar?, Beside Ina cewa kayi bayan komai ya lafa zaka sake ta?".

"In shi kuma yaje ya jiyo abinda mu bamu sani ba a kanta ya riƙe matsayin makamin hana auren fa?".

"You so stupid man, ya Ina tambayar ka kana maida min tambaya matsayin amsa?".

"And what did I say wrong?".
Dunƙule hannu Haisam yayi ya kai masa duka a kafaɗa shi kuma ya goce yana sakin silent smile na ganin yadda ya harzuƙa Haisam ɗin wanda ba wanda ke iya tolerating halin sa se shi kaɗai da Allah ya sallaɗawa so da ƙaunar sa.

"Please bawan Allah let's be serious, kaga wannan auren ina so ya faru at all cost ko banda hatsaniyar jaridar nan har ma da jama'ar gidan ku, na rasa gane wace irin cukurkuɗaɗɗiyar rayuwa ce ke faruwa a gidan ku, da na zauna nayi tunani dole se da mace a tare da kai zamu fahimci kome ke tafiya dan na tabbatar wanda suka farmaki nafisa zasu sake yunƙurowa tun bare ma in ya zama kai ka samo matar da kanka".

"Rayuwar gidan mu bahaguwar rayuwa ce da hatta ni da nake cikin ta ba komai nake fahimta ba, abu ɗaya na sani shine kowa mara gaskiya ne, kowa macuci ne haka kuma kowa mugu ne shiyasa na zaɓi na rayu on my own haka kuma bana don shigar da kowace ƴa cikin haɗarin dake tattare da rayuwa ta dan maharana suna da yawa Haisam, dalilin kenan da na haƙura da aure amma for now ya zama dole in miƙe in har zata shiga rayuwa ta ko da na kwanaki ne kuwa".

"Me kake gani, mu bata hutu zuwa lokacin da komai ze tabbata ta fara amsa sunan matar ka ko yaya?".

Relaxing yayi cikin kujerar da yake kai yana lumshe ido

"Kasan meye damuwa ta?, Ƴaƴan ta, bana san a cutar da kowanne saboda ni, bana a ringa cutar da yaran da basu ji ba basu gani ba saboda wani ƙiyayya da ake min".

Ya ƙarashe yana buɗe idanun sa da lokaci guda suka canja kala zuwa jajaja brownish

"It hurts, it deeply hurt Haisam".

Ya faɗa yana dafe ƙirjin sa ɓangaren hagun sa alamun yana masa ciwo

"Calm down Abu Aulad, calm down insha Allah ba abinda ze same su".

Rufe idon sa yayi tare da kife kan sa kan table ɗin gaban sa ya shiga ajiyar zuciya akai akai tare da haɗiye wani ƙullutu me matuƙar ɗaci da ke taso masa duk sanda ya tuno yara, yana matuƙar san yara a rayuwar sa hakan yasa ake masa Indiya da Abu Aulad tun yana saurayi, da ya zama magidanci kuwa yayi aure burin sa da fatan sa ya haihu ne kawai, lokacin da Allah ya bawa matar sa ciki irin murnar da yayi ba me misaltuwa bace sedai Allah be nufa rayayyu bane daga uwar har ƴaƴan.

Miƙewa yayi ya zafi key ɗin sa ya fice da sauri kamar ze tashi sama haka ma Haisam ya bi bayan sa, yau dai kam ba abinda suka tsinana....................✍🏻.

©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️ Ote, Comment and share fisabilillah.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 09 [ 12/1/2022 1:04 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

                     FREE PAGE 009

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

_________________________📖 tafiya ce sosai daga Gamji kafin a kai ƙauyen Ba muni dan har se dasu Ibty suka gaji da kwaramniya suka yi bacci a jikin Haisam dake baya a tare dasu.

Ita kam salma wani irin nervousness da faɗuwar gaba ne ya sarƙe ta, after good five years da barin ta gida yau gashi zata koma kan mau'idin da bata san wanne bane, abu ɗaya ta sani shine akan maganar auren ta ne aka tashi tafiyar.

Motar shiru baka jin tashin komai se numfashin su a hankali a hankali da kuma gudun Ac dake tashi, Haisam kam wayar sa yake pressing hankalin sa kwance yana chat abinsa da budurwar sa yayinda a ta gaban motar kuwa tamkar wasu kurame ko saƙaguna haka suke zaune.

Shi tuƙin sa kawai yake ita kuwa ba abinda take se bin hanya da kallo kamar me irga bishiyun da suke wucewa, tunanin yadda zata riski garin bayan shekara biyar da tayi bata cikin sa take, maganar tarba kuwa tasan ba wata tarba da zata samu a wajen ƴan uwan mahaifin nata.

Abu ne ba ɓoyayye ba cewa murna da jin daɗi suka yi lokacin da ta zaɓi barin su saboda ƴaƴan ta, irin wulaƙancin da suka yi mata na ƙin barin ta ta ɗau ko tsinke a gidan be bar kanta ba kuma bata jin ze barin har nan da gaban abada.

Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta saki lokacin da suka shiga garin tana me lumshe ido cikin kiran sunan Allah a ranta, a kaikaice ya kalle ta dan sosai ajiyar numfashin nata ya fito fili.

Gidan maigari ya nufa kamar jiya, seda duk suka fita daga motar suka barta dan ji tayi gaba É—aya kamar bata da wani sauran laka a jikin ta, jikin yayi mata nauyi kamar baya tare da ita, Haisam da ya lura bata biyo su bane ya juya ya tabbatar sannan ya maida kallon sa kan Abu Aulad

"Madam fa bata fito ba, ina ganin kaje kaji ko da damuwa ne ni Bari in ƙarasa ciki". Ya faɗa yana yin gaba da sauri dan yasan kaɗan daga aikin bawan Allah yace shi yaje ya duba.

Ganin yadda ya tafi yabar shi a wajen yasa cikin takaicin abinda tayi kamar wata ƙaramar yarinya ya koma wajen motar, murfin ɓangaren da take zaune ya kama ya buɗe da ɗan ƙarfi dan ransa ya ɓaci da abinda tayi, ya zata wani nemi waje ta zauna a mota bayan tasan suna da abubuwan yi da yawa a gaban su.

A ɗan firgice ta buɗe idon ta da ke lumshe hakan yasa suka yi wani walai kafin suka shige cikin nasa da ya tsare ta dasu, da sauri ya kau da kan sa dan jin wani dam da gaban sa yayi ganin ƙwayar idon ta, be taɓa sanin haka ƙwayar idon ta take ba se yau,

"Kina jira a É—auke ki ne kafin ki fito?".

Tsam tayi jin abinda ya faÉ—a dan bata gane me yake nufi ba

"Malama ki fito mu yi abinda ya kawo mu dan ba kwana zamu yi ba kin sani ko?".

Ƙafarta dake ajiye gaban motar ta ɗaga a hankali ta fitar waje kafin ta fara ƙoƙarin fitar da gangar jikin ta hakan yasa aya matsa daga tsayuwar da yayi jikin motar, seda ta gyara mayafin kanta sannan ta yi gaba shi kuma ya kulle motar da mukulli bayan ya buɗe glass ɗin baya kaɗan saboda su Ibty dake kwance suna bacci.

Gaba ɗaya ido mutanen wajen suka zuba mata suna kallo yayinda ƙananan maganganu ke tashi dan jiya da yawa da suka san abinda ya faru da ita da suka ji batun ɗaurin auren ta ba ƙaramin tu'ajjabi suka yi ba barin ma da suka ga zuƙeƙen mijin da Allah ya bata.

Yanzu kuwa ba wai sun gane ta bane maganganun kan irin kyan ta da kuma na kayan jikin ta ne, Æ´an gayu irin ta dasu Haisam ba kasafai suke shigowa garin ba shiyasa duk sanda suka shigo suke zama abin kallo da sha'awa ga jama'ar garin.

A hankali ta saluɓe brown heel shoe ɗin dake ƙafarta ta kai zaune kan shimfiɗar fadar maigari kafin cikin sanyayyar Muryar ta ta shiga gaida shi kamar yadda suke yi a al'adance.
Chapter 10 · 0% Book details