Sashe 24
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka Nadiya ta fashe dashi hannu bibbiyu aka tana faÉ—in yayi mata gori yaci zarafin ta, ko kallon ta be yi ba se Hajiya da yake kallo dan yasan komai Nadiya ta faÉ—awa Salma da sanin ta da kuma sa hannun ta shiyasa bata dakatar da ita ba, kuma da biyu yace ze yi Shari'a da wanda ya bashi second hand matsayin budurwa wanda wannan kuma da shuraiha yake shiyasa abin ya hadewa Hajiya, ga bakin ciki ga kuma fargaba da tsoro.
"Kaga baba kayi masa magana akan abinda yake wa yan dakin mu, jibi fa maganar da ya fadawa yaya Nadee kuma in yi magana ace bani da kunya".
Abdulkarim dan autan Hajiya da ta ke kira da jarumi ya faɗa yana harare harare, ba ƙaramin haushin Abdallah yake ji ba sedai yayi kaɗan ya tunkaro shi shiyasa ya saka baba a lamarin dan watarana da ya taɓa kuskuren yi masa rashin kunya wani mari da yayi masa seda ya wuni be san wake kan sa ba, haka hannun sa da ya daga da sunan kai wa Abu Aulad ɗin duka seda aka ɗora shi dan baras ya balla shi shiyasa yake tsoron sa, wannan maganar ma dan kar Hajiya ta balbale shi da fadan matsoraci ne in sun koma part din ta.
"Me kuma ya kawo batun gori cikin maganar nan Abdallah, me kake so ka zama ne, kai ne fa me tare mata in kaga wani na neman tozarta ta amma kai ne ma me yi mata, wace irin rayuwa ce wannan?".
Cikin rashin damuwa ya gyara zaman sa yadda ze fuskanci baba sosai
"Ko mintuna bakwai ba'a yi ba da yarinyar nan ta buɗe ƙazamin bakin ta tana fadawa matata maganganu, shin hakan da tayi daidai ne, martabar matata da mutuncin ta fa ta taɓa a gaban ku duka amma shin wa ya ce mata tayi ba daidai ba?, Babu, shin ba ita ya kamata in taga za'a ci zarafin salma ta tare ba Baba, amma me tayi yanzu?!.
Am sorry to say kayi haƙuri baba Amma tun shekaranjiya na faɗa sedai ko in Kun manta, duk wanda ya taɓa min mutuncin mata ba zan kyale shi ba, kowaye shi kuwa, babba duk girman sa haka karami duk kankantar sa ban cire kowa ba se inda ƙarfi na ya ƙare, kai ne kadai zan iya kau da wa kai a kan ta, dan haka gwara su kiyaye".
Ko sallama be yi wa kowa ba hatta baba dan ya bashi haushi ya ficewar sa zuwa sashen su, falon shiru ba kowa haka ba haske sosai alamun itama ta kwanta kenan, dakin sa ya shige ransa ba daɗi ta wani bangaren kuwa farin ciki ne dan ganin yadda Hajiya Babba ke sharar hawaye haka ta kasa cewa komai alamun ta kai maƙura wajen ɓacin rai kenan.
Acan falon baba kuwa shima baffa sallama yayi musu ya fice zuwa sashen sa dake can da nisa dan wasu É—auka suke ma ba'a cikin gidan part din yake ba saboda nisan sa zuwa na baba.
Shifu falon yayi se tashin ajiyar zuciyar Hajiya Babba, ɗagowa tayi zata yi magana se kuma idanun ta suka sauka kan su Anna da Nuriyya da suka zuba tagumi suna bin kowa da kallo, wata shegiyar harara Hajiya ta watsa musu da tasa Anna janye idon ta daga kan su ta fara yunkurin tashi haka itama Nuriyya ganin Anna na miƙewa itama se ta tashi, sallama suka yi wa baba suka wuce sumi sumi suka fita.
Seda taja tsaki kafin ta maida hankali kan baba dan da zafi zafi zata tafi da komai in ba haka ba kuwa yaron nan dab yake da sa mata ciwon zuciya.
"Banji kayi maganar tariyar yarinyar nan ba Alhaji, kasan fa yadda a kayi auren nan in ba dagewa akayi ba haka auren ze lalace dan kasan dama ba son ta yake ba, ni kuwa ba zan zuba ido ya kare rayuwar sa da yarinyar da bamu san asalin ta ba, ko banza gwara shuraiha mun san iyayen ta mun san sana'ar su dan hatta wasu daga cikin Æ´an uwan su na sani, ga yarinyar akwai tarbiyya ga girmama na gaba, amma ya kace?".
Numfasawa baba yayi kafin cikin sanyin da yayi saboda hayaniya da be fiya so ba yanzu kan sa se ya fara ciwo, ta nan wajen kam shi Abu Aulad ya gado
"Ba matsala, zan sa a gyara side din dake gefen nasa se ta tare ko nan da zuwa sati É—aya ne".
"Har sati Alhaji, be yi yawa ba kuwa?".
"To shikenan, nan da zuwa kwana uku ai nasan yayi ko?".
"Sosai ma, Allah ya kara buÉ—i kaga se in sanar da iyayen ta dan su tanadi komai".
Bece mata komai ba se lumshe ido da yayi dan kansa dake dan ciwo, ganin haka yasa Hajiya miƙewa dan ba ita me da girki ba dama, amarya ce wadda yau kwana uku kenan basu haɗu ba, ta dai ji wai ta fadi kan hannun ta ya karye dan haka taje jiyya gidan wan ta, ita kuma yau ba zata zauna da Alhaji ba dan tana bukatar su tattauna da ƴaƴan ta kan abinda ke gaban su.
★★★★
"Amma Anna yanzu haka zamu zuba ido mun tashi ba mu ga tsuntsu ba mu ga tarko, yanzu ana nufin in zuba ido in kalli yaya Abdun da nake matukar so zaune da wasu matan da babu ni a ciki, eye Anna ki fa ga kallon da hajiya tayi mana yau, da ni matar yaya Abdu ce ta isa tayi?, Kalli dai yanzu yadda ya shigar wa matar sa faÉ—a, wayyo ni Nuriyya na shiga uku".
Nuriyya ta faÉ—a tana fashewa da kuka wanda tun da suka dawo sashen su dama abinda take yi kenan.......................âœðŸ».
Ouummey 📚âœðŸ».
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 017 [ 12/7/2022 1:01 PM ]
★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★
_*PAID BOOK*_
Story/written by Ouummey.
Wattpad @ouummey.
From The author of:
*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*
           Paid page 017
_________________________📖 "Bar kira min shiga uku kinji ko, ba zanga shiga ko daya ba balle uku insha Allah, in ta San wata ai ba ta san wata ba ita Hajiyar, mu zuba ni da ita muga waze nasara".
"Wancan karon ma fa haka kika ce Anna, Kuma ita din tayi nasarar dan gashi ta aura masa waccan shegiyar me goshi kamar jirgi ya doso tasha".
"Wannan karon kuma ki zuba ido ki kalli yadda zan buga wasan, kin san yadda akayi tun farko ya auri yar uwar ki nafisatu?, To shima tsari nane yanzu ma kuma ze aure ki ko be so ba".
Rungume Anna tayi tana yar dariyar farin ciki
"Na gode Anna ta, Allah ya bamu Sa'a, in ya aure ni har Makka zan sa ya kaiki dan ni ba irin yaa nafisa bace".
"Allah ya yarda diyar arziki, ni dama nasan ke É—in ba irin ta ba ce dan ita ta cika sanyin jiki da nawa".
Nan suka cigaba da hirar su kamar basu da wata damuwa yayinda Anna ke ta sake saken neman mafita a ranta.
Can ɓangaren su Hajiya da ƴaƴan ta kuwa sashen ta suka yi masauki cikin babban falon ta da ya lakume set ɗin kujeru biyu, ita dai Nadiya har lokacin sharar hawaye take lokaci zuwa lokaci dan ba kaɗan ba taji ciwon maganganun da Abu Aulad ya faɗa mata hakan yasa ta ƙudiri niyyar bada goyan baya kan dukkan wani tsari na Hajiya wajen fafutukar ƙwatar musu yanci.
"Shi wannan shashashan har yanzu be san me duniya take ciki ba, da anyi magana yace so, son banza son wofi, Kai a yanzu an gaya maka akwai wani so bayan son kuɗi, ai kuɗi sune rayuwa malam, in Basu Kuma babu rayuwa haka ba wanda ze kalle ka har ko ita da kake iqirarin kana so ɗin, duk fafutukar da nake yi domin ku nake yi musamman ma kai, in aka samu nasara zaka daukaka ka shahara har fiye da yadda shi yayi suna, haka ma yan uwan ka zasu fi karfin wulaƙancin namiji da duk wani treats din sa, dan haka nake so duk ku bani hankali da tunanin ku mu haɗu mu hada karfi da karfe mu yaki abokin gabar mu da ba kowa bane face Abdallah".
"Ni dama kin san tuntuni ina bayan ki akan komai, wadannan biyun ne ke neman bamu matsala musamman ma Kareem dan gara Nadiya ita kawai shiga cikin sha'anin ne bata yi".
Sumayya ta faÉ—a tana duban nadiya da idanu suka yi wa jajir kamar an watsa mata barkono
"Yanzu kuma ina ciki yaa sumayya, ina goyon bayan duk wani tsarin Hajiya dan haka ba kuda matsala yanzu dani".
Nadiya ta faÉ—a tana jan hanci, muskutawa Hajiya tayi cikin jin daÉ—in yadda Æ´aÆ´an nata yanzu duk suka hau kan hanya
"Atoh gwara dai ki san ciwon kan ki, yanzu fa jibi maganganun da yaron nan yayi, da akwai bako a wurin yakike gani za'a É—auki maganar, dan haka ba zamu bar abinda yayi a banza ba dole a bi miki kadin hakan, ita ma kuma matar tasa se ta raina kanta, bari dai yarinyar can ta tare".
"Me ya haÉ—a tariyar ta da tsarin mu Hajiya?".
"Aikuwa ita ke da alaka da tsarin mu dan dole muna bukatar makusanci gare shi sosai wanda ba kowa bane face matar sa, aikin mu ze Fara ne daga zarar ta tare, zamu dinga samun information a wajen ta na shige da ficen sa, yanayin kasuwancin sa, takardun kadarorin sa da dai sauran su".
Sosai suka gamsu da kalamai da hangen Hajiyar suka kuma cigaba da tattauna tare da kulla mugayen nufin su.
*********
A hankali ta sauko daga kan gadon tana addu'ar bacci wadda Manzon Allah ya koyar, miƙa tayi a hankali sannan ta sauke tare da nufar toilet dan yin alwala.