← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 44

Sashe 11

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rawar jiki maigari ya amsa duk da bai shaida cewa Salame bace, a tunanin sa wata ce daga dangin su É—an birni suka zo da ita tare maybe dan taga mahaifar matar da ya aura ko wani abu.

"Ala gafarta malam, ga Salman nan gaban ka mun zo da ita dan kayi mata bayanin yadda auren ya ƙullu jiya a kuma bata sadakin ta dan ta shaida".

"Ikon Allah, yaro kana nufin nan Salame ce a gabana, lallai Allah mai iko, sannu Salame, sannu kinji".

Maigari ya faɗa cikin ruɗewar jin wai wannan tsaleliyar budurwar ce Salame da suka kora da goyon ƴaƴa biyu shekara biyar da suka gabata, yarinyar da ko da ta bar garin ba komai gare ta se tarin tsumma dan hatta takalmi babu a ƙafarta ranar.

"Nice baba maigari, fatan mun same ku lafiya".

"Lafiya lau salamatu, ya yaran naki? Ko kin bar su a gida ne?".

"A'a baba suna mota bacci suka yi shiyasa ba'a É—auko su ba".

"Allah Sarkin hikima, yanzu sun girma abin su ko, hekara biyar ai ba nan bace dole yanzu sun girma".

"Aikuwa dai". Ta faɗa tare da jan bakin ta ta tsuke ganin surutun na maigari bame ƙare wa bane ita kuma ta zaƙu taji bayanin da aka ce yayi mata da in ba kunnuwan ta ne basu jiyo daidai ba kamar taji ana batun an ɗaura mata aure ne tun jiya

"Wato salamatu jiya yaran nan suka zo nan suka same Ni da batun neman auren ki, duk da ko a Shari'a ni me bayar da auren ki ne amma se na bawa iyayen ki haƙƙin su ta hanyar sawa a ka kira su na shaida musu abinda ke shirin aukuwa sedai dake Habibu ba ɗan bana da arziƙi bane se yace shi sam babu shi a lamarin ki haka ma iro, se Adamu ne shi dake wani sa'in yana da tunani ya saurari yaran nan amma yace sedai in a ɗaura auren a jiyan dan baze juri a Kuma tado shi daga wajen sana'ar sa domin ki ba wannan yasa dole aka ɗaura auren bisa sadakin da shi mijin ki ya biya wato dubu hamsin gashi nan a zaune, yanzu bari in tashi in ɗauko su gare ki, kin ji yadda batun ya kasance".

Wani irin suya zuciyar ta ta shiga yi cikin ƙirjin ta jin irin cin kashin da ƴan uwan mahaifin ta suka aikata yayin neman auren ta, shin me ta kashewa mutanen nan ne da suke neman se sun wulaƙanta ta ido rufe?, Shin akwai ɓoyayyen dabi ne tsakanin mahaifin ta dasu ko kuwa, su dai ba ƴan uba ba balle tace ƴan ubanci suke gwada mata, ko kuwa duk ƙiyayyar mahaifiyar ta ce ta shafe ta har haka.

Hannu tasa ta goge hawayen da suka gangaro kan kuncin ta daidai lokacin da maigari ya miƙawa Abu Aulad sadakin ta shikuma ya ajiye mata kan cinyar ta, murya na rawa ta shiga magana

"Nagode sosai baba, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma sedai Ina son ganin su baba habibun game da gado na dake wajen su".

"Babu komai salamatu, ke ɗin ai ɗiya ce gare ni, abinda ya faru a baya ma saɓanin fahimta da kuma zugar iyayen ki ne, yanzu bari in aika su zo se ayi batun gadon naki".

Ɗaya daga cikin dogaran sa ya aika azo dasu baba Habibu dukan su, ba'a jima ba dogarin ya dawo tare dasu suna bin shi abaya se ƙunƙuni suke na yadda ake shiga rayuwar su kan wata banza can Salame da suka daɗe da tsamewa matsayin jinin su.

Gaban maigari suka zube suka yi gaisuwa, salma ya nuna musu bayan ya amsa ya shiga kora musu bayani

"Ga Salame nan mijin ta ya kawo ta na mata bayanin auren su da aka É—aura jiya se kuma gashi tazo da batun gadon ta dake hannun ku tana neman a bata kason ta".

Maigari ya ƙarashe yana gyara saɓa hannun babbar rigar jikin sa tare da furzar da tiƙar goran dake bakin sa, ido waje baba Habibu da ƴan uwan sa ke kallon tsaleliyar budurwar da aka nuna musu wai Salame, cikin rashin yarda baba Habibu ya furta sunan ta

"Salame".

"Na'am baba barka da rana".

Ta faɗa tana buɗe idanun ta sosai a kan su dan su san fa yanzu ba da bane da take shakka da tsoran su, cikin sanyin jiki baba iro yai gyara zama dan ƙwayar idon ta kawai ya kalla ya shaida ita ce.

"Dama nace gadon baba na dake hannun ku nake buƙata baba dan Ina son yin amfani dashi".

"Eh to, gado ko, tabbas kam kamisu ya bar gado sedai yana wajen Adamu ai bani ba".

Da sauri baba Adamu da yaji baba Habibu na neman zame wa ya bar shi a ciki ya buÉ—e baki

"Ina ce gona ce kawai a wajena Habibu?".

"Ai dama ita nake nufi, am ke Salame sedai fa kiyi haƙuri dan kiwon da ya bari tuni babu su, da su ne mukai ta amfani wajen ciyar dake har zuwa lokacin da kika bar wajen mu dan haka gona dai tana nan ban da ita kuma babu komai". Ya faɗa yana kai da kai gefe cikin rashin gaskiya.

Girgiza kai akwai tayi dan tasan ba wani an ciyar da ita an cinye ne kawai babu su yanzu, gonar ma tasan ban da albarkacin yanayin da ya ganta na wadata da kuma waÉ—anda ke tare da ita da baze bayar ba itama cewa ze yi an siyar an kula da ita.

"Allah ya amfana gonar, sedai ina da buƙatar ta ujila zan yi amfani da ita".

"Amma ina ce kinji ance tana hannun Adamu, shima amfani yake da ita dan haka sedai kiyi haƙuri, gona na mazaunin taki amma ya riga yayi shuka dan haka se yayi girbi se ki karɓa".

Cikin rashin tsoro ko shakka ta dubi baba Habibu dake maganar cikin hatsari da gadara

"Zan bar tane sabida a hannun baba Adamu take banda haka bana jin da wani ne ba shuka ba kome yayi se dai ya kwashe ya kai inda yake dashi tun da dai gona mallaki nace".

Daga baba Habibu har baba iro tsumu suka yi cikin kunya dan sun san da su take, wato da ba Adamu bane dole a bata a bar ta, lallai yarinyar nan ta goge.

Abu Aulad da yaji an kawo matsaya ya miƙe dan tuni yake kallon agogon hannun sa, baya san suyi dare kamar jiya dan a tsarin sa a yau yake son ta tare a gidan su dan ya nuna wa duk wani dake tunanin ce iya juya shi ko iko dashi ƙarya yake, be isa ba kuma be kai ba, anyi a da amma banda yanzu!.

"Mungode sosai, ga wannan a siya horo, Allah ya ƙara girma, ku tashi ku tafi ko?".

Ya faɗa yana ajiye wa maigari bundle ɗin ɗari bibbiyu, miƙewa tayi tana adjusting pin ɗin mayafin ta da taji ya ɗan matse ta, har bakin mota maigari ya raka su inda su baba Habibu suka zama ƴan kallo, Haisam ne ma yayi tunanin basu ƴan canjika dan shi uban gayya ko kallo biyu basu samu daga gare shi ba.

Tun jiya mutuncin su ya zube tsaf a idanun sa saboda abinda suka yi, me É—an daman cikin su ne baba Adamu dan shine kawai ya samu gaisuwa daga gare shi.

Haisam na buɗe bayan motar Ibty ta fito tana mutsittsika ido tare da tura baki gaba cikin son fashewa da kukan rashin ganin Mamman ta, da sauri Salma ta riƙo hannun ta tare da jawo ta gaban ta.

Duƙawa tayi zuwa tsayin yarinyar ta cire mata hannun ta dake kan fuskar ta, ɗaga mata gira tayi tare da jan kumatunta tana sakin mata murmushi itama yarinyar ta maida mata sannan ta shige jikin ta tana sakin ajiyar zuciya, seda ta tabbatar ta dawo daidai sannan ta kama hannun ta ta buɗe gaban motar zata shiga baba maigari dake kallon su ya magantu

"Masha Allah, tubarkallah, hala wannan É—aya daga cikin yaran ne salamatu?".

"Eh baba, Hassana ce Ussaina na bacci bata tashi ba".

"Allah Sarkin hikima da buwaya, tubarkallah yarinya kyakkyawa kamar Æ´ar turawa, Allah ya raya yayi musu Albarka, Allahu Akbar da girma yake".

Da Ameen ta amsa masa tare da shigewa motar dan shima tasan borin kunya ne ya ke yi na abinda yayi mata lokacin da tafi buƙatar taimakon su shiyasa duk wani rawar ƙafar sa be ɗaɗata da ƙasa ba.

Numfashi ta sauke na samun relief lokacin da motar su ta fara tafiya kan burjin har ƙasar dake garin, tasbih tare da godiya kawai take yi cikin ranta wa Ubangiji da ya canja mata rayuwa daga wata mara ma'ana zuwa wadda take ciki yanzu.

Nauyi taji ƙirjin ta yayi mata lokacin da ta tuna cewa yanzu fa ita ɗin matar aure ce, matar Abdallah Abdulsalam Gamji shugaban fitacaccen kuma shahararren kamfanin A.A Gamji.

Bata san wace irin rayuwa ce kuma ke jiran ta nan gaba ba a gidan auren ta sedai tana fata koma wace irin ce ta zo mata da sauƙi, akasin haka kuma Allah ya bata wuyan ɗauka ya kuma yi riƙo da hannun ta wajen ganin ta samu mafita akan dukkan matsalar da zata tunkaro ta.

Ta daÉ—e da sanin ita rayuwar gaba É—aya jarrabawa ce, gwaji ce da bawa ba zai daina samun shi ba har se lokacin da rai yayi bankwana da gangar jiki wadda ranar ce ba wanda ya sani tunda ita mutuwa ba sallama take ba haka kuma ba wai notice take bayarwa ba bakuna allo ne da ake rubuta jadawalin sunayen mutanen da zasu tafi yau, gobe jibi da ma kullum ba.

Cikin wannan tunanin suka shigo garin Gamji, tafiyar ba kamar ta É—azu ba yanzu kam hira ce suke yi shida Haisam jefi jefi yayinda ita tayi nisa cikin duniyar tunanin da take yi tana daga zaune rungume da Ibty a jikin ta.

Haisam É—in suka fara saukewa inda suka yi sallama da abokin nasa kuma shugaban sa kan se sun yi waya yayinda cikin nutsuwa ya cigaba da driving motar har zuwa gaban gidan su da bata san yaushe ya sani ba kuma ya wa ya sanar dashi ba.
Chapter 11 · 0% Book details