← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 44

Sashe 26

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe ido Laila tayi hawaye na gangarowa daga idanun ta zuwa kan kuncin ta, ta sani tabbas gaskiya Umah ta faɗa amma kuma ai ba ita ta ɗorawa kanta son shi ba, akan me za'a dinga ganin laifin ta, ta ina zata fara yakin cire son da ta riga ta bari ya zaga ko ina cikin faɗin zuciyar ta ya kafa rassa?, Tabbas ba zata iya ba!, Bata haƙura ba, haka ba ta fidda rai ba, tana ji a jikin ta watarana zata zo da A A Gamji ze dube ta da duba irin na soyayya har ma su kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya wato aure.

Wannan false assurance din da zuciyar ta ta bata yasa bata kuma saurarar Umah ba tayi gaba zuwa main building tana sake karfafawa kanta gwiwa......................✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 018 [ 12/8/2022 11:46 AM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

Paid page 018

_________________________📖 Yau kam da wuri suka tashi kasancewar Asabar karfe biyu ake tashi, bata san yadda akayi ba se ganin driver tayi yazo daukar ta dan ita a fitowar da tayi niyyar ta taje ta hau adaidaita sahu ne.

Gida ya kai ta saboda weekend su Ibty 3:00 pm suke tashi, akwai ragowar hour daya kenan.

Wanka tayi ta saka riga da wando sakakku sannan ta nufi kitchen dan yin girki.

Tsayuwa tayi a kitchen din tana ƙarewa komai kallo cikin tunanin me ma zata dafa, ta dade tsaye kafin ta fara firfito da kayayyakin da zata buƙata wajen girkin.

Cikin abinda be gaza awa É—aya ba ta gama malmala tuwon ta na shinkafa da yake nan fari tas dashi ta zuba a warmers, a dan kwanakin da yake cin abinci dasu ta fahimci ya fi cin dambun couscous da tayi wanda a nata fahimtar ta gane ya fi son abinciccikan gargajiya.

Tukunyar miyar ta buɗe, lumshe ido tayi saboda ƙamshin da ya daki hancin ta, buɗe wa tayi ta juya miyar dan ganin ta ƙarasa dafuwa ko kuwa, ita kanta tasan miyar ta haɗu ko a iya ido balle kuma ina aroma din ya shiga hancin mutum.

Kashe gas din tayi tare da zuba wa cikin daya warmer din mahaÉ—in na tuwon, cikin jin daÉ—i ta haÉ—a kyakkyawan kunun gyaÉ—a ta juye cikin flasks sannan ta haÉ—a komai takai dining ta jere komai.

Falon ta shiga gyarawa though ba wani datti gare shi ba, tana gama wa kuma ta koma bedroom din ta shi ma tayi masa thorough sanitation, kwata kwata sabida aiki ta manta da lokacin dauko su Ibty yayi, gaba É—aya se ta ringa ganin ai se four Kamar ragowar ranaku.

Wanka tayi tare da sauya kaya zuwa doguwar rigar atamfa pitch color dinkin A shape, sosai rigar ta zauna a jikin ta haka ma kalar ta karɓe ta kai kace purposely dan ita dama akayi ta, ɗankwali ta ɗauka zata daura se kuma ta dakata jin kamar Muryar yaran ta, da sauri ta daga kai ta kalli agogo se taga har hudu saura mintuna biyar, se lokacin ta tuna wai ashe fa three za ah tashi.

Da hanzari ta fito ko ɗankwalin ma bata daura ba yana dai riƙe a hannun ta, so take taga waye ya dauko mata su dan dai bata ce driver ya ɗauko su ba balle tace shine, sam bata son wani na zuwa dauko mata yara dan a kan su bata yarda da kowa ba se kanta kawai.

Ƙamshin sassanyan turaren sa shi ya shaida mata shima yana falon dan ko da ta gama gyara falon turaren wutan da ta ke sawa ya riga ya fara kama falon.

Bata gama tunanin ta ba taji Ibty a jikin ta, durƙusa tayi ta rungume ta cike da ƙaunar ta, janye Ibty tayi daga jikin ta ta miƙe riƙe da hannun ta ta ƙarasa gaban Abu Aulad zaune kan kujera Ifty na kwance a jikin sa, sunkuyawa tayi tana taɓa wuyan yarinyar kafin ta sa hannu ta ɗago ta

"Baby zazzaɓi ne ya dawo ko, sannu bari ayi wanka ko?".

Ta faɗa tana neman daukar ta, riƙe yarinyar yayi yana kauda kan sa gefe saboda yadda gaba ɗaya ƙamshin mayukan dake gashin ta suka cika masa hanci dan sunkuyowar da tayi gashin har taɓa masa fuska yake.

"Kashe ta zaki yi da zaki mata wanka da wannan zazzabin a jikin ta?".

Dakatawa tayi daga daukar nata ta daga kai ta kalle shi, gashin ta da ya rufe mata fuska yasa ta tuna bako É—ankwali a kanta, baya tayi da sauri tare da yafa É—ankwalin a kanta cike da kunyar yaga gashin ta.

"Ki canja musu kaya muje hospital".

Daukan Ifty da ya kwantar kan kujera tayi yayinda Ibty tabi bayan su zuwa bedroom, Shima nashi bedroom din ya shiga dan yayi wanka ya kuma canja kaya.

Falo ta zaunar dasu itama ta zauna bayan ta yafa mayafin da ya hau da kayan, hannun ta riƙe da karamar purse kalan mayafi da takalmin da tasa, sanye da farin yadi kal dashi ya fito dan har ana ganin vest ɗin da yasa sanya a ciki, kansa na sanye da farar hula itama kar da ita ta zauna tayi matukar kyau a kansa yayinda kwantacciyar sumar sa ta fito ta baya se sheki take, takalmin ƙafar s fari ne dam gaba ɗaya shigar farare yayi.

Sosai yayi wa salma kyau a idanu da har seda ta ɗago ta shiga kallon sa batare da ta sani ba, ganin babu shi a wajen yasa ta dawo hankalin ta ashe tuni ya fice ɗauke da Ifty a hannun sa, kama hannun ibtisam tayi wadda ke shirye cikin doguwar riga yar kanti pink color ita da yar uwar ta, kanta kuwa bakin scarf ne haka ma takalmin ta baƙi ne, rufe kofar gidan nasu tayi sannan suka bi bayan sa, gaban wata Black din mota dake ƙyalli ta tadda shi yana buɗewa, zaman ta a gidan har ta gane motocin sa, motoci hudu dake ƙarƙashin wata bakar tempole duk nasa ne.

Gaban wata motar ta buÉ—e ta shiga tare da fita Ibty akan cinyar ta kamar yadda taga yayi wa Ifty, a hankali ya tada motar ya fita daga gidan.

Slowly yake tafiya kan titin kamarw wanda ba shi da lafiya, ita dai kan ta na window tana kallon hanya dan ko so daya bata kalle shi ba tun da suka shiga motar.
Gaban NOOROL HAQ special hospital ya ƙarasa yayinda masu gadi suka buɗe masa gate ya shige, parking yayi tare da bude motar ya fita dauke da iftihal itama ta fita tare da riƙe hannun Ibty dan Allah ya gani ita kam ta gaji da dauke ɗauke nan, yaran tubarkallah gasu da ƙiba daidai gwargwado ai dole ta gaji.

Jerawa suka yi har ciki yayinda jama'ar dake kai kawo a farfajiyar hospital din suke bin su da kallo cike da sha'awa da burgewa, a yadda suke din they make a perfect family, a very perfect ma kuwa.

Gaban office din da ta ga san sa Dr. Habeeb ya tsaya tare da knocking duk da cewa akwai mutane kaÉ—an da suka samu zaune.

Kofar office din ce ta buɗe wata nutse ta fita tare da maida ƙofar ta rufe tana faɗa musu doctor Yana tare da patient, Salma ce kawai ta amsa mata dan shikam wayar sa ya fidda ya kira Dr habeeb ɗin, sam baya son jira a rayuwar sa shi yasa shima baya bari a jira shi, sedai wanda su ka yadda suyi masa hakuri dan shikam baze iya bin layi ba.

Da Fara'a Dr habeeb ya É—au wayar yana masa kirari kamar yadda ya saba wanda ke cike da tsokana kasancewar sa abokin karatun sa tun na primary, be biye masa ba ya sanar dashi gashi a bakin office din sa ya kawo patient, jin haka yasa Dr habeeb kashe wayar ya tashi ya buÉ—e musu kofar da kan sa tare da basu hanya suka shiga.

Kan sofa suka zauna shikuma ya ƙarasa sallamar patient din gaban sa kafin ya maida attention din sa kan su Abu Aulad

"A.A Gamji kunyi wuyar gani".

"Ba wani wuya habeeb B kune dai bakwa neman mutane".

"Aikuwa ba zaka ce haka ba dan ko last haÉ—uwar mu Ni na shige wajen ka a Company kaga kuwa na fika zumunci".

"Kasan ayyukan mu ga kuma jama'a shiyasa ba ma samun wani lokacin hutu".

"Hakane kam, Allah dai ya shige mana gaba, kaga hankali na ya dauku gare ka ko gaisawa bamu yi da Madam ba, Madam Barka da safiya".

"Ina kwana, ya ayyuka".

"Lafiya lau alhamdulillah, Gamji waye patient din anan?".

Dr habeeb ya faÉ—a yana kallon Ibty da ta gaishe shi ya amsa cike da murmushi, ba kaÉ—an ba babyn ta burge shi, gata kyakkyawa ga kuma adon da aka yi mata.

"Ga ta nan, tun jiya take fama da zazzabi, ta bata magana ya sauka amma ya dawo".

"Ayya sannu baby, twins ne amma ko".

"Eh". Abu Aulad ya bashi amsa lokacin da yake miƙa masa Ifty, karɓar ta Dr yayi ya kwantar da ita kan wani gado dake office din ya shiga duba ta, yana gamawa ya maida wa Abu Aulad ita shi kuma ya shiga rubutu kan takarda dake gaban shi, intercom din dake kan table ɗin sa yayi pressing se ga nurse ta bude kofa ta shigo.

Takardar da yayi rubutun ya bata

"Ki karbo min wannan magungunan yanzu".

Amsa masa tayi tare da juya wa ta fita shikuma ya maida hankalin sa kan Abu Aulad

"Malaria ce take damun ta duk da bata yi karfi ba dan haka zan mata injection É—aya se Kuma drugs da zata dinga sha, a kiyaye barin ta cikin sauraye pls".

"Insha Allah". Kawai Abdallah yace masa a ransa yana faÉ—in ba a gidan sa ta samo malaria ba tafiyayya ce daga gidan su dan shi kam gidan sa ko alamar abinda ya danganci sauro ma babu.
Chapter 26 · 0% Book details