← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 44

Sashe 39

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi ya sauke me nauyi kafin karon farko again ya furta mata kalaman da bata taɓa tsammanin jin su ba daga bakin shi, kalaman da ta sawa ranta har abada ba zasu taɓa fitowa daga bakin Abdallah zuwa kunnen ta ba.

"I love You too Mom twins, so very much, pls take care".

Yana fadar haka ya juya da sauri ya shige, haka muma muka juya na maida su gida.

Ban san me ya faru ko ya akayi ba, kwana biyu da tafiyar sa ya kira ni a rikice wai ina nafisa, me ya sami yaran sa, sam se ban gane inda kalaman sa suka nufa ba, da kyar yayi min bayanin wai yana ta kiran ta tun jiya da dare har zuwa yammacin yau amma be same ta ba.

Haka yasa na tafi estate din dan duba masa su, sedai abinda aka sanar dani yasa naji jiri na shirin jefar da ni da dole na nemi waje na zauna ina ambaton Allah a raina.

Wai nafisa ta fita unguwa tun jiyan da rana amma har yau ba ta dawo ba, an bi bayan ta gidan kawar ta da taje yiwa barka tace ai tun jiyan suka yi sallama ta koma. Yanzu dai an sanar da jami'an tsaro kuma suna kan aikin neman su amma har yanzu ba'a gan ta ba, abin tashin hankalin wai gaba É—aya cikin gari ko alamar motar ta babu balle kuma su.

Ban iya na fadawa Abdallah wannan bakin labarin ba domin bani da karfin halin hakan, ina ji ina gani na kasa daukan duk kiran da yake min wanda ya kira nin yafi so hamsin daga ƙarshe ma se kashe wayar nayi.

Kashegari kawai se ganin mutum muka yi ya shigo lokacin muna estate din nasu muna shawarar a fara bin ƙauyukan garin ko za'a dace, hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba dan kwasar sa akayi zuwa asibiti ya yanki jiki ya fadi, dukkan mu bamu yi mamaki ba da likita ke sanar da mu jinin sa ne yayi mugun tashi irin wanda ba'a so na farar ɗayar nan ga kuma faduwar da yayi wanda ba dan Allah ya kare ba se ya samu stroke.

Baba muka bari wajen sa muka shiga neman nafisa da yaran ta ido rufe sedai har dare ya rufa ba wani alamu na za'a gan ta, washegari na haka muka kuma bazuwa, bamu ba ba jami'an ba.

Se bayan kwana uku jami'ai suka samo motar ta da kusan rabin ta ke kone a can hanyar barin gari, gaba ɗaya ita da yaran sun kone dan ba'a gane kamannin su musamman ita traces na wasu sassan jikin ta da basu gama ƙonewa ba kawai aka samu, lambar motar tata ce, wayar ta ma an samo ta amma ta kone sosai, takalmin kafar ta, mayafin ta har da ragowar atamfar jikin ta se rabin fuskar ta, yaran kuwa sun kone sosai da ba'a gane ko fuskar su, Bama su da kyan ganin da mutum ze so yi sake kallon su, haka aka yayyafa musu ruwa aka nannaɗe su cikin likkafani.

Iya tashin hankali mun shiga a lokacin saboda baba dagewa yayi se Abu Aulad yazo kan gawar matar sa da Æ´aÆ´an sa haka dole aka dauko shi daga hospital zuwa gida, sedai a kallon farko da yayi musu sumewa yayi a tsaye sedai gani akayi ya tafi ze fadi hakan yasan nayi azamar tare shi, ruwa aka dinga zuba masa da yasa yaja dogon numfashi, yana buÉ—e ido ya zabura tare da fincikewa daga jikina ya koma gaban gawar, ba wai mutuwar ce tasa yake neman haukacewa ba a'a irin yadda yaga yaran sa da matar sa ne yake birkita masa kwanya.

Wani irin ja baya yayi kamar wanda wuta taja saboda fuskar yaran da yayi arba da ita, durƙushewa yayi ya fara fisgan numfashi saboda katsewa da yayi daga huhun sa sedai ya kasa nan take ya kuma zubewa, in takaice miki dai daga ƙarshe janye shi akayi daga kan gawar dan ba abinda yake se sumewa, suman karshe kuwa da yayi har an saddakar dashi ma ya tafi kafin ya farfaɗo, Abdallah be taɓa bani tausayi ba kamar na lokacin, gaba ɗaya ya birkice bashi da abin yi illa kuka hakan yasa jikin sa sake birkicewa dole akayi asibiti dashi, daga ƙarshe dai dole fitar dashi akayi waje saboda kullum jinin sa sake hawa yake ba sauka ba ga kuma zuciyar sa da ta kumbura, abinda ya bawa likitocin tsoro shine irin bugun da zuciyar ke yi ga kuma kumbura da take yi kullum sama da baya, watan sa uku a can kafin ya farfaɗo daga comar da ya shiga, seda ya dauki wata biyu kafin ya fara responding to maganar mutane ya Kuma fara magana, at least dai Abdallah se da ya bata shekara a kasar Jamus saboda likitocin sun rike shi, da taimakon Allah da taimakon addu'ar baba da ta masoya ya fara dawowa daidai saidai duk sanda abin ya dawo masa haka idanun sa ke yin jajir kamar su fitar da jini, kan sa kuwa ya dinga tsananin ciwo yayinda ƙirjin sa ma ke amsawa, dole ba yadda likitoci zasu yi su hana shi tuna bayan sa hakan yasa muka tattaro muka dawo tare da tulin magungunan da aka dora shi akai.

Dawowar mu muka tarar da wani sabon tashin hankali domin dai wata karuwa ce da tayi suna da kuma fice ta makalewa baba, duk yadda baba yaso yakice ta daga jikin sa ta kiya gashi har duniya ta fara sanin shi da ita dan duk ƙasar da yaje tana biye dashi, ko ina bin sa take shi kuma baban ya kasa mata rashin mutuncin da zata bar shi ko kuma ya haɗa ta da security, lokacin da Abdallah ya tunkare shi a batun budar bakin sa se cewa yayi son ta yake, wannan furucin ya sake sa Abu Aulad cikin wani hali dan gaba ɗaya baba ya Fara bata musu reputation, ba wai yana biye mata suna sabon Allah bane, ba kuma kama su akayi tare ba haka ba ganin su a kayi a gurin da bai dace ba sedai kasancewar sa babban mutum sananne kuma nagartacce yasa ganin ta tare dashi ya zama abin surutu ga jama'a tare da zargi da sharri ga maƙiya.

Shekara kusan biyu ana abu ɗaya kafin daga ƙarshe baba ya aure ta wanda shine ya kawo karshen wannan rikicin, se sabon matsala da ta bullo tsakanin Abdallah da amaryar baba wadda ba zan ce miki komai akai ba domin wannan magana ce tsakanin ku, shi zai miki bayanin komai duk da bana tunanin nan kusa amma nasan ko be miki ba tabbas watarana idanun ki zasu gane miki.

Shigowar Hajar wato amaryar baba rayuwar estate din ta Fara canja salo dan kam iya shegen ta take salo salo, Hajiya babba ba ƙaramin wahalar ta tasha ba dan cikakkiyar yar bariki ce da ke juya baba cike da kissa da kisisina ta hanyar da bazai taba ganin laifin ta ba, salon ta be dore sosai ba tashi ɗaya muka ga baba ya dawo se abinda Hajiya Babba ta ce masa yake aikatawa, duk kuwa abinda tace me kyau ko akasin sa to fa wajen baban me kyau ne tar...........................✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 027 [ 12/12/2022 11:29 AM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

Paid page 027

_________________________📖 Tun daga lokacin Abu Aulad ba shi da wani sakat dan komai yayi cikin laifi yake wajen baba haka zata zuga shi yasa shi a gaba da faɗa da zagi, akwai wani lokaci da tace yayi mata rashin kunya haka baba ya sashi gaba da zagi da cin mutunci har dasu mari abinda kaf a rayuwar sa tun daga yarinta har zuwa girman sa baba be taɓa daga hannun sa ya kai jikin sa da sunan duka ba.

Hatta Ummu watarana da ta taɓa marin shi haka baba yasa ta gaba da faɗa kamar ze ari Baki dan ban da Allah ya rufa asiri Abdallah dan ta ne ba da har rama masa ze iya cewa ze yi, se gashi da kan sa ranar ya daga hannu ya kai fuskar Abdallah da sunan mari wanda a lokacin shekarun sa na haihuwa 34 ne.

Rayuwar Abdallah ta sake yin zafi dan yanzu bashi da wajen da ze raba yaji daÉ—i, kullum cikin damuwa da tunani yake ga kuma Hajar da ta sako shi gaba itama da nata sharrin hakan yasa dole ya kaura ya bar musu estate din ya koma É—aya daga cikin gidajen sa da rayuwa.

Barin sa gidan ma be tsira ba dan haka Hajiya ta zauna ta tsara baba kan ya koma gidan sa ne dan su daina sa masa ido yayi irin rayuwar da ya ga dama, wai an faÉ—a mata ya fara biyewa abokan banza yana bin mata shiyasa ya gujewa idanun su haka kuma shine dalilin da yasa yaki aure har yanzu.

Irin cin mutuncin da baba yayi wa Abdallah a lokacin maƙura ne dan ko makiyin sa iya jifan sa da mugayen kalaman da ze yi kenan, ranar se da ciwon sa ya tashi amma baba ko a jikinnsa haka ya tsallake shi ya bar shi kwance baya ko cikin hayyacin sa.

Jin shiru be zo ba bayan yace min akwai takardun daze kawo min yasa na bishi gidan shine fa na tarar dashi cikin wannan halin har na nemo likita ya duba shi.
Bisa umarnin baba dole ya rufe gidan ya koma estate da rayuwa inda Hajiya Babba ta kuma ɓullo da sabon jidalin auren shuraiha da take so yayi.
Chapter 39 · 0% Book details