← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 44

Sashe 44

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Zama tayi kan stool din mirrorn ta shiga naɗa daurin ɗankwali, cikin kankanin lokaci se gashi ta malkawada shi ya zauna a kanta cif cif yai kyau, gashin gaban goshin ta dake kwance suka kuma ƙawata fuskar tata, powder ta murza tare da wadata idanun ta da kwallin kajol, haka kawai ta samu kan ta da kara maskara kan zara zaran baƙin gashin idon nata ta kuma bi idanun da eyeliner, bakin takuwa sun sha lipgloss me danko nude color se pink lips din nata sukai wani irin sassanyan kyau me fizgar hankali.

Ya subhanallah, ita kanta da ta gama gaba ɗaya ta kalli kanta se da ta zaro golden brown cat eyes din ta cikin tantamar anya ita ce kuwa, irin kyan da ta ga tayi seda ya firgitata, idanun ta a suka fi komai yin kyau a yau, wani irin ɗaukan hankali suke yi dan yadda ƙwayar cikin take ba baka ba ragowar kuwa fari ne tas hakan yasa kwallin da ta saka ya zauna daram, daga saman farar fatar idon kuwa ga nan bakar eyeliner, ga Kuma gashin idon ta da tun ainahi baki zara zara ne ya kuma sha bakar maskara se ya sake yin duhu ya kuma mike sosai.

A hankali ta janye daga jikin madubin tana tasbih a ranta, wai fa komai be ki gyara ba ko, kai gaskiyar hausawa da suka ce ko kana da kyau ka kara da wanka, yanzu dai kalli ita ɗin nan ba wanda zece itace wadda taje aikin nan dazu, duk da dama da kyan ta amma kwalliyar ba ƙaramin sake fito da ita tayi ba.

Falon ta zauna ta kunna wa twins dake shirye cikin gungun wando iya cinya fari da bakar riga me kamar shimi wanasha suna kallan wakokin larabawa ita kuma ta cigaba da karatun novel din da take yi na Ayusher muhd me suna A GIDANA, ba ƙaramin tafiya da ita salon labarin yayi ba, haka ma kuma jarumin ciki wato khaleed, gaba ɗaya se take ganin halin sa na mata kama da na gwarzon mijin ta Abu Aulad, yanayin miskilancin su, Shariya da iya bakar magana se take ganin kamar mijin nata aka suffan ta.

Karatun take tana murmushin dramar khaleed da uwargida kuma amaryar sa zainab lokacin Bayan anyi auren su yadda yake tafiyar da ita, abin se ya ƙayatar da ita ta dinga jin dama nata mijin shima ze bata dama kamar haka duk da kuwa ita zainab ta cika son girma da bata so a ga gazawar ta balle ya raina ta a cewar ta.

Tattausar Muryar sa da yayi sallama ta ratsa dodon kunnen ta ne yasa ta lumshe ido tana gyara zama kana ta É—ago ta dube shi dan har ya shigo falon, yau kam be zauna wajen su Ifty ba ya shige bayan sunyi welcoming nasa.

A gurguje ya shirya ya fito, inda ya bar ta zaune nan ya same ta,

"ÆŠauko mayafin ki kizo, ki tahowa da yaran nan takalman su".

Kallon sa tayi cikin son karin bayani sedai ganin ya tsuke baki yasa ta miƙe dan cika umarnin sa a ranta tana mamakin ina ne zasu da daren nan..................... ✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
Chapter 44 · 0% Book details