← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 44

Sashe 21

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Plate ta ja ta zuba masa couscous din da tayi wa hadi kamar dambu yasha kayan lambu se ta zuba masa miyar hantan a gefe ta aje masa a gaban sa ta kuma zuba masa hantan da yawa a wani ƙaramin bowl shima ta aje masa, lemon kankanan dama a gaban shi yake dan haka cup kawai ta sake turawa gaban sa in ze Sha ya zuba.

Su Ifty ta zubawa kowa nasa suma duk da ba haka ta saba musu ba, sun saba a tare suke cin abincin su su uku, aikuwa kamar yada ta tsammata Ibty kinci tayi s kallon ta da take yi tana narai narai da idanu zata yi kuka.

Ganin haka yasa salma ta hade nata da na Ibty dan yarinyar akwai kawa zuci haka kuma shaƙuwar dake tsakanin su sanin ta se Allah, ita kanta ta sani tana matsanancin son yarinyar har fiye da yar uwar ta sedai bata nunawa, ba komai yaja take son ta haka ba se yadda yarinyar ke son ta, komai ba zata ci ba se da ita, ko yaushe yana nanike da ita, duk abinda take so to shi yarinyar ke so haka in dai tace ta bar abu so daga to fa ba zata maimaita so biyu ba ba kamar Ifty dake da ƙiriniya da rashin ji ba sometimes.

Tare suka shiga ci ita da Ibty tana ci tana bata a baki, ganin haka itama Ifty se ta matsa kusa dashi ta saka spoon din ta cikin abincin sa dabe ko kalla ba bare ya fara ci duk kuwa da yadda aroma din ya cika masa hanci, yunwa yake ji kamar yaci babu amma baze iya taba abinda ke gaban sa ba saboda rashin yarda.

Sam be yarda da yarinyar ba ba kuma dan tayi wani abu na zargi ko kuwa rashin dacewa ba se dan yasan halin mata yayi kuma encountering din shi har kusan so uku, a yadda yake zaune cikin tsakiyar maƙiya da mahada yasani za'a iya amfani da kowa dan ganin an yake shi an kai shi ƙasa ciki kuwa harda ita, ba kowa ne ze iya tsallake tayi makudan kudade kan abinda yake ganin kankani bane balle kuma mace, macen ma irin ta dake struggling kula da kanta da ƴaƴan ta, duk da cewa ba wai tana cikin rashi bane amma mutanen zamani ba abinda ba zasu iya yi kan kudi ba.

Abincin da yaji adaidai saitin bakin sa yasa ya buÉ—e idon sa ya sauke kan fuskar Ifty da takai masa spoon din baki tana murmushi, daga masa gira tayi tana sake maimaita masa statement din ta da tunani be bar shi yaji ba tun farko

"Daddy haaa".

Ɗan zaro ido yayi kafin ya girgiza kai ya sa hannun ya karbi spoon din a hannun ta ya maida abincin saitin bakin ta yayi mata alamar ta karba da ido, make kafaɗa tayi tare da kauda Kai ta karɓe spoon din ta maida masa baki tare da kwaɓe fuska zata yi kuka tana masa pointing wajen su salma da hannu.

A hankali ya juya wajen su ya kalle su yadda suke cin abincin gwanin sha'awa, in Ibty ta bawa Salma se itama ta karba ta bawa Ibtyn, juyowa yayi ya kalli Ifty yana mata alamar ya gani meye, sake ɗebowa tayi ta kai masa bakin sa, duk da ya fahimci me take nufi se ya kawar da kai ya amshi spoon din ya juye abincin sannan ya miƙa hannu yaja plate din gaban salma dake gefen sa ya tura musu nashi sannan ya saka spoon din ya sa ya dibi abincin ya kai bakin sa bayan yayi bismilla.

Lumshe idon sa yayi lokacin da abincin ya sauka akan harshen sa, sosai taste din abincin yayi masa ya da yasa yaji kamar kar ya buÉ—e ido, ya dade be ci abincin da yaji taste din sa ya kaima sa kamar wannan ba, kai in ba dan kar yayi karya ba tun Ummu na raye.

Da sauri ya buÉ—e idon dan kar yarinyar nan tace santi yake, ba komai yasa ya janye plate din ta ba sedan ganin shi yake ci haka ba zata sa abin cutarwa ciki nata abincin ba haka kuma ze gani in zata ci nasa, in har taci to bata sa komai ba in Kuma taki tabbas da matsala.

Yana buÉ—e idon ya sauke akan ta lokacin da ta Kai spoon na biyu bakin ta tana sakewa Ibty murmushi, kauda idon sa yayi ya bawa Ifty a baki, haka suka cigaba da cin abincin cikin nutsuwa hankali kwance.

Abu Aulad be ankara ba se ganin plate din su yayi ba komai, gashi dama ba cikakke bane su salma sun riga sun fara ci, tabbas abincin yayi masa daɗi haka kuma be ishe shi ba amma baze ce akara ko ya kara ba, a yadda ya dinga nuna be san ci taga kuma ya ƙara ai da kunya dan haka se kawai ya kai hannu ya zuba juice din kankanar ya Kai wa Ifty baki tasha har ta ƙoshi sannan ya zuba shima yasha.

Idea É—in a cikin hakan dan shima lemon ya tabbatar da babu komai acikin sa tunda yasan ba zata cutar da Æ´aÆ´an ta ba.

Tissue yasa ya goge bakin sa haka ma Ifty sannan ya mike tare da ranƙwafawa yayi mata peck a goshi, kujerar Ibty itama ya karasa yayi mata kana ya nufi hanyar dakin sa ya shige.

Ajiyar zuciya ta sauke na samun relief dan duk abinda take yi a wajen karfin hali ne amma ji take kamar ta zura da gudu saboda tsabar yadda kwarjinin sa ya cika ko'ina, abincin ma da kyar ta iya daurewa taci wanda hakan dan kore masa shakku da kokwanto ne dam bata manta sentence din Haisam na É—azu ba ....."be gama sanin ki ba".....

Ita ba yarinya bace da zece wai ne gama sanin ta ba shiyasa baze ci abincin ba, kawai magana ɗaya ce be yarda da ita ba shiyasa aya share masa dukkan shakkun sa.................✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 015 [ 12/6/2022 10:54 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

                     Paid page 015

_________________________📖 suna gama cin nasu ta kwashe ragowar da suka bari taje ta aaje inda ba zasu lalace ba sannan ta koma falo ta kunna wa twins MBC 3, ƙarfe takwas da rabi ta kashe komai suka wuce bedroom suka yi shirin bacci suka kwanta.

Yau ma shi ya tashe ta daga bacci kamar jiya haka kuma bata gan shi ba, da alamu yana mata knocking yake tafiya yabar wajen.

Breakfast ta haÉ—a ta gyara inda ya kamata kafin ta koma ta shirya yan biyu itama ta shirya, yau kam a hanyar fita daga falon suka same shi, da alama office ze tafi dan a shirye yake cikin Armani suits din sa coffe color da ya amshi skin din shi ya haska shi sosai, a yadda yayi kyau ba wanda zece wai yayi rashin lafiya sedai wanda suka san shi sosai.

Ifty da ta dane shi ne yasa ya juyo daga fitar da ze yi duk da ya riga ya bude kofar, É—aga ta yayi rungume tana gaida shi yana amsawa dadai lokacin da Nuriyya ta sako kai zata shige zuwa compound dan daga part É—in su se an biyo ta wajen part É—in sa za'a kai compound.

Tsayawa tayi tana kallon su batare da ta wuce ɗin ba, fahimta da yayi akwai wani a tsaye yasa ya shiga takawa cikin takun sa na ƙasaita da yar sassarfar sa ya kai gaban salma dake shirin dukewa da niyyar gaishe shi.

Sauke Ifty yayi ya miƙa dogayen hannayen sa dake cike da gargasa fatar sa luwai luwai kamar baya shiga rana ya jawo ta jikin sa ya rungume tare da kai bakin sa ya sumbaci kan ta.
Tsayin mintuna biyu sannan ya zare ta daga jikin sa amma har lokacin yana rike da hannun ta, ƙasa ƙasa yayi magana yadda ko su Ifty ba suji me yace ba balle Nuriyya dake can da ɗan nisa

"Anyi rescheduling general meeting zuwa 8:00am dot, make sure baki makara ba".

Yana gama faÉ—in haka ya sake pecking goshin ta sannan ya saki hannun ta ya juya yayi pecking twins ya fita.

Tun da ya saki hannun salma Nuriyya tayi gaggawar juya zuwa sashen su dan ta ma hakura da fitar, tsananin É—acin da zuciyar ta ke mata baze bar ta ta iya fita ba.

Tafiya kawai take yi bata ko sanin ina take jefe ƙafarta yayinda zuciyar ta ta kasa dena hango mata yanayin da ta riske su, tsananin soyayyar da ta gani tsakanin su shike shirin hallaka ruhin ta, yaya Abdun da take matuƙar so, yaya Abdun da ta daɗe tana burin mallaka, yaya Abdun da tayi wa kanta tanadi tsawon shekaru yau shine take gani cikin yanayi na shaukin so da kauna da wata mace, wata da ba ita ba, watan ma bazawara.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka balle kan kuncin Nuriyya da yasa ta kasa cigaba da tafiyar da take yi se kawai kwasa tayi da gudu zuwa part din su.

Ita kam salma se bayan fitar sa da kusan mintuna uku kafin ta iya jan numfashi tare da fara kikkifta idanu kamar sabuwar kamun hauka, zare ido kawai take yayinda zuciyar ke tsananin bugu kamar ta fito daga ramin ta, kwata kwata kwakwalwar ta ta kasa lissafin abin da ya faru mintuna uku baya, did he just hug her, ya Allah, he hug her, wallahi he hug her in his broad warm chest.

Hannun ta dake rawa tasa ta shafo saman hijab din ta da yayi pecking ta gangaro zuwa gaban goshin ta da shima ya samu kason sa, ya gaffar wannan mutumin ze haukatar da ita.
Chapter 21 · 0% Book details