Sashe 36
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau kam tayi daren girki dan haka farar shinkafa ta dafa musu da jar miya, salad ta duba a freezer se taga babu , dole haka ta hakura ta yanka ita cabbage da carrot ta haÉ—a musu coslow dan cin farar shinkafa tsura se dole.
Wanka tayi musu dan sun bata kayan jikin su, guntun wando da ya wuce cinya da kadan ta saka musu se shimi wanda a cikin kayan da Daddyn su ya siyo Ifty ta dauko.
Se da ta gama jera komai sannan hankalin ta ya kwanta ta koma ta sake kwanciya cikin sofa sedai wannan karon ba bacci take yi ba, sunna Tv ta kunna se ta tadda sun saka karatun Alkur'ani dan haka ta rufe ido take bi ƙasa ƙasa.
Yau be dawo da wuri ba dan a waje tayi isha, ganin dare nayi yaran har suna neman yin bacci basu ci komai ba se ta zuba musu suka ci, addu'ar bacci tayi musu bayan sun gama kana tace su tafi dakin Daddy su kwanta ita kuma ta cigaba da zama.
Se ƙarfe tara da kusan rabi sannan ya shigo falon, coat din sa a hannu yar cikin ma ya ɓalle maɓallayen saman, dukkan alamun gajiya su gama nuna kan su a tattare dashi.
Sannu da zuwa tayi masa ya amsa ta ta hanyar daga hannu ya shige É—akin sa, hararar kofar tayi ganin yadda ya wani daga mata hannu kamar kurman da be da bakin amsa mata.
Shiru shiru taji fitowar bawan Allahn har ta haƙura ta cire rai, abincin ta taje taci ta bar masa nasa cikin warmer da tunanin in yazo ci ya zubawa kan sa.
Ko da ta tashi da asuba ta a idar da sallah abincin ta fara dubawa dan dashi ta kwana a ranta, ganin be wani ci da yawa ba se bata ji dadi ba, haka dai ta kwashe ta kai kitchen ta shuga hidimar haka breakfast, tana aikin ya dawo daga masallaci, yadda hankalin ta ya dauku ga aikin yasa bata na ji shigowar saba se maganar sa da taji daga bakin ƙofar kitchen din
"A hada musu basket zasu je school".
Kai ta gyada masa alamun amsawa ya juya ze fita
"Ina kwana an tashi lafiya".
Ta gaida shi, yau É—in ma dai kamar kullum da lafiya ya amsa mata ya fice ita kuma ta cigaba da aikin ta.
Kamar yadda ya faɗa haka ta haɗa basket ta shirya dining sannan ta wuce da niyyar zuwa shirya su sedai tsaf ta tarar dasu cikin gogaggen uniform din su da clean white neat socks din su ƙafafun su sanye da white canvas din su me kyau.
..'lallai Daddyn su Ibty matar sa tayi Sa'a'...
Ta faÉ—a cikin ranta se kuma ta É—an yi turus lokacin da wani sashe ya tuna mata
..' wace matar tasa kuma bayan ke?'...
"No bani ba, amarya dai".
Ta faÉ—a a fili se kuma ta yamutsa fuska tare da rungume yaran ta suna gaisawa.
Kan dining din ta kai su tare da hada musu tea din su tare da zuba musu chips din da ta siya da kwai ta ajiye musu bread a tsakiyar su ta maza ta koma É—aki dan yin nata shirin.
Seda ta sake wanka saboda ƙamshin girki da take yi sannan ta zura farar rigar ta da blue ɗin wando, yau kam golden din after dress ta dora kan uniform din sedai Kamar ko yaushe bata ɗauki mayafin rigar ba kasancewar da hijab din ta a jikin ta.
Golden slippers me kyau kirar Dubai ta sake a kafar ta tare da ciro handbag din ta kalar sa ta zuba abubuwan da zata buƙata ta fita.
Kan sofa ta ajiye jakar sannan ta ƙarasa dining, ba kowa a dining din shiyasa ta maza ta karya a gurguje ta dawo wajen twins dake zaune, Daddy fa tambaye su suka ce yana daki.
Sake tambayar su tayi in yayi break suka ce mata eh dan haka itama ta zauna jiran shi.
Be daÉ—e ba ya fito a shiryen sa kamar kullum sanye da suits sedai yau ja ne kuma ba zata iya cewa ga Companyn su ba sedai daga kallo É—aya kasan masu tsada ne saboda yadda suke daukan eyes, É—aga iya Ido kadai ana iya gane taushin su ga kuma yadda zaren su ya saku ya kwanta kamar haka aka halicce su ba yin su aka yi ba.
Bakin cover ne a ƙafarsa dake shekin tsada da ƙyalli, gaba dayan sa kana ganin sa kaga cikakken wayayyen namiji da yasan takan duniya da kaya, ado kuwa sedai a koya a wajen shi dan ta wannan fannin shi ɗin ya zarce matakin Farfesa.
Da kyar da sidin goshi ta janye idanun ta daga kanshi tana lumshe su cike da shauƙin da bata san daga ina yake tahowa ba, me ya assasa shi duk bata sani ba , abu ɗaya ta sani shine taji daɗin ganin sa cikin koshin lafiya ba dan komai ba se dan yadda shima take kula da lafiya da walwalar ya'yan ta.
Ganin sun nufi kofa shi da twins da suka rike masa hannaye yasa itama ta tashi tare da daukan handbag din ta ta mara musu baya tana cigaba da kallon su yadda suka yi kyau kamar uban gaske da Æ´aÆ´an sa.
Kofar sashen ta rufe sannan ta yi parking lot din sa da ta gane nasa be shi kadai tun kwanan ta biyu a gidan, tun da ga nesa ta hango jar motar dake ta ƙyallin wanki da sabunta dan daga ganin ta ba'a wani hau ta sosai ba, tana hango yadda ya saka su Ibty a baya cikin kula da takatsantsan kamar wasu sabbin jarirai kana ya shiga side din driver ya zauna.
Tana ƙarasowa ta buɗe gaban motar da bisimillan da yaji ta sosai sannan ta zauna tare da rufe motar, hankalin sa yaji yana daɗa kwanciya da ita dan yana son mutum me addini da kiyayewa wanda tun a irin tambayoyin da yake wasu Ibty kan makaranta ya tabbatar da tana da ilimi gwargwado dan komai in ya tambayi kan suka iya se suce momma ce ta koya musu.
Addu'ar fita da abin hawa yayi sannan ya tashi motar ya nufi gate tare da ficewa daga gidan...........................âœðŸ».
Ouummey 📚âœðŸ».
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 025 [ 12/11/2022 1:00 PM ]
★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★
_*PAID BOOK*_
Story/written by Ouummey.
Wattpad @ouummey.
From The author of:
*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*
           Paid page 025
_________________________📖 Rayuwa ta cigaba da tafiya yara na girma har Abdallah yakai shekaru shida sannan Allah ya kara bawa Hajiya Babba ciki, wannan karon kam irin addu'ar da tayi kan Allah ya sa ta haifi namiji ba kaɗan bane, sedai Allah yafi kowa sanin abinda ya dace da bayin sa shiyasa ya kuma bata mace a karo na biyu.
Irin kukan da Hajiya Babba ta yi a haihuwar Nadiya Kai kace mutuwa akayi mata, yarinyar kuwa seda baba yayi mata jan ido sannan ta haƙura take shayar da ita, bori kuwa irin wanda tayi baze fadu ba, shikam baba har mamakin raunin imanin ta yake yi dan kirikiri tace wai yafi son Ummu dama shiyasa yayi mata cikin namiji ita kuma da baya son ta yake mata na maata.
A lokacin be iya ce mata komai ba dan ya fahimci bata hayyacin ta, shidai yayi murna da ƙaruwar da ya samu na wannan kyauta da Allah ya bashi, ya kashe kuɗi kamar me, kayan jaririya kam kamar za'a bude store amma duk hakan be dada hajiya Babba da kasa b, ita da burin ta ta haifi namiji.
Haihuwar Nadiya yasa Abdallah ya makalewa sashen Hajiya saboda Allah ya zuba masa son yara wanda tun kafin ya kai haka Ummu ta gane dan in taje barka da shi da kyar ake karbar jaririn a hannun sa dan rigima yake sawa dole se an basu sun tafi dashi gidan su.
Hajiya wadda tsanar Abu Aulad ta gama ginawa a ran ta tun ta uwar sa da kuma son da baba ke.masa se ta samu damar mammake shi in ya shigo wajen Baby nadee Kamar yadda yake kiran Nadiya.
Duk dukan da zata yi mishi baya hana ya gama kuka kuma ya koma anjima, tun Ummu na damuwa har ta zuba ido kawai ta ƙyale shi dan akan yara kam baya ji baya gani.
Duk wani kuɗin break ɗin sa akan Baby nadee yake ƙarar dasu lokacin, daga ƙarshe saboda dukan da Hajiya ke masa se yake dauke yarinyar ya tafi da ita sashen su, haka Hajiya zata bishi ta karewa Ummu zagi ta karɓe yarta a wajen shi bayan tsarabar dukan da ze Sha Amma Ummu bata taɓa ce mata komai ba dan akwai ta da kawaici da ɗauke kai.
Wata rana da yaje daukar nadiya Hajiya ta ganshi ta kwace ta tare da tankade shi har ya kai ga faduwa ya fasa kai ne Ummu ta tanka hajiya Dan seda ta sille ta tas ta kuma zane Abdallah da ya fara amsa sunan Abu Aulad tun a lokacin dan ya bata mata rai, a cewar ta da be je ba ai ba za'a ji masa ciwo a cuce ta ba.
Tun daga ranar Ummu take kulle Abu Aulad a sashen su ta kuma sa baba ya siyo Masa kayan wasa na yara maza masu yawa, daki guda ta ware masa ta shirya masa su wanda hakan ya sata samu sauƙin kuncin da ya fara shiga kwana biyu.