← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 44

Sashe 35

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan shine sanadin da Abdallah ya daina zaman office din Baba, shaƙuwar dake tsakanin Abu Aulad da baba ba karama bace dan kafin ya kira sunan Ummu so daya ya ambaci baba so goma, haka shima baba duk ya dawo daga office ba ya taba wucewa sashen sa se ya shiga sashen Ummu yaga Abu Aulad inda yake bata lokaci sosai a wajen sa.

Wannan abun ba ƙaramin ciwa hajiya rai yake ba dan a ganin ta baba ba yasan yar ta saudah dan bata kasance namiji ba shiyasa baya kulawa da ita, tun tana shiru har se da ta kai ta magantu dan ta kasa riƙe abun a ranta.

A lokacin kallon ta kawai Abba yayi sannan ya murmusa kana cikin halin miskilancin sa wanda shi Abu Aulad ya gado ya bata amsa

"Ni ban fi son wani daban ba cikin yarana, dukkan su ina jin su a raina tun da jini na ne, ban fifita Abdallah kan saudah dan nafi son sa ko dan shi namiji ne ba, ina masa komai ne dan shi É—in photocopy nane, halin sa irin nawa ne haka ma kamannin sa shugaban yasa nake ganin sa kamar ni sanda ina yaro, amma ki kwantar da hankalin ki zan gyara".

Tun da ga wannan lokacin baba yake shiga sashen Hajiya Babba dan ganin saudah sedai babu wani shaƙuwa tsakanin su sosai dan ita saudah akwai dafar uwar ta da girman ta amma bata yarda baba ya ɗauke ta sedai kallo daga hannun babar ta..................✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 023 [ 12/10/2022 11:01 AM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

Paid page 023

_________________________📖 Tattare musu kayan wasan tayi ta hade su takai daki kana ta canja kayan ta zuwa na bacci, tana zaune tana addu'a se gasu sun shigo kowanne su sanye da kayan baccin su iri ɗaya hatta ko da kala.

Zama suka yi gefen ta har ta karasa ta shafa musu ta shafa wa kan ta

"Ya akayi yaran Daddy basu kwanta bacci ba har yanzu?".

"Momma ni na cewa Daddy a wajen ki zamu kwanta yau kar kiyi fushi irin na É—azu".

Kallon Ibty da tayi maganar tayi cikin rashin jin dadi, se taji bata so yarinyar ta faÉ—a masa haka ba, bayan duk wahalar da yake yi dasu ai be cancanci ta nuna masa kamar be isa dasu ba.

"Maza ku koma wajen Daddy ku kwanta, yau momma bata so a dame ta".

Kallon ta suka tsaya yi bare ma Ibty, suna son zuwan sedai basa so tayi fushi

"Come on darlings, come and hug momma, ayi min good night hug".
Ta faÉ—a tana buÉ—e hannayen ta dan tayi cheering din su, aikuwa da gudu suka shiga jikin ta suka rungume ta, da É—aiÉ—aya ta bisu ta musu peck a goshi da kunci kana ta sake su

"Oya maza a tafi Daddy yana jira, and acewa Daddy momma tace Masa goodnight".

"Okay Mom".

Suka fada suna ficewa da É—an gudu, ajiyar zuciya ta sauke tare da komawa ta kwanta tana latsa madannin wutar dake gefen bed din ta, take duhu ya cika dakin hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da yin luff a gadon.

Ita kanta bata san me yasa tace a ce masa goodnight ba, kawai ta tsinci kan ta da son yi masa sallamar, tun da kuma baya kusa shine ta bada sako.

Yau ma da kyar bacci ya É—auke ta dan dagaske bata saba bacci ita daya ba tun da yaran suka shigo rayuwar ta.

Bata yi gigin cewa zasu school ba dan a yadda taga uban yana ji da Æ´aÆ´an sa tasan baze bari suje yau ba duk da jikin Iftyn ya warware tas, maybe dai gobe ya iya cewa suje.

Breakfast ta hada musu traditionally, kunun gyada da kosai wanda yaji hadi yayi sutu sutu dashi gwanin kyau da burgewa, tana gama wa ta koma tayi wanka abinta ta shirya sannan ta fito gyaran falo.

Bata neme su ba dan tasan se ya gama shirya su zasu fito, a yadda ta ga ya sa musu sababbin kayan bacci ya tabbatar mata siyayya yayi musu dan haka tasan akwai kayan da zasu iya sawa a dakin sa base yaje dauko musu ba.

Kamar kuwa ta sani shirye suka fito yau kam zam Æ´aÆ´an larabawa, Arabian gowns ne na yara da suka sha adon stones se walwali da É—aukar ido suke yi gaba dayan su bakake, ita kanta da ta gan su seda tace masha Allah saboda tsananin kyan da ta ga sun yi.

Cikin ranta kuwa wani sabon daraja a girma Abu Aulad ɗin ke karawa, dama an ce me da wawa, to haka ne ga salma, ba tun yanzu ba ita duk me son yayan ta yakan zama masoyin ta bare shi da ya karɓe su hannu bibbiyu yake kulawa dasu wanda a ganin ta ko mahaifin su ne iya soyayyar daze gwada musu kenan.

Ita har yanzu fa mamaki yake bata, mamakin ta ba na komai bane illa yadda taga ya iya kula da yara, wankan su da shirya su, gashi ba ya'ya maza ba balle tace ai simple shiri ne

Yanzu kalli dai yadda yayi wa yaran nata rolling, ko iya mace haka zata yi dan wata ma ba zata iya gyara shi yayi kyau haka ba.

Tunanin ta ya katse ne lokacin da Ifty ke jan hannun ta wai suje suci abinci, bata Musa mata ba ta biya kamar raƙumi da alaka har gaban table ɗin, kujerar gefen Iftyn ta zauna wanda suka saka Daddyn nasu a tsakiya, ita tana gefen dama Ibty na hagu.

Kallon plate din gaban sa kawai yake yi cikde da wani irin daÉ—in da ya tsaya iya ran sa be bayyana kan miskilar fuskar sa ba, ya manta rabon sa da ya karya da kunu da kosai, ze iya cewa tun ma kafin Ummu ta rasu dan ita bata shiri da kosai, sedai ta kan daure tayi masa tun da ta fahimci yana so.

Manyan oily and sexy eyes din sa ya waina kafin ya kai hannu ya É—au guda daya ya nufi bakin sa dashi bayan yayi bisimilla, irin yadda taste É—in ya ratsa harshen sa ya wuce zuwa jijiyoyi jikin sa zuwa kwakwalwar sa ya tilasta masa dakatawa daga taunar da ya fara na tsawon sakanni kafin ya cigaba da ci, ita kam salma ganin ya tsaya da ci se take tunani ko bai yi masa daÉ—i bane?, Sedai kuma ganin yadda ya buÉ—e zuciyar sa yake ci da sauri da sauri se ya share mata tantama.

Kafin kace me ya cinye na plate din gaban sa duk da ba laifi da ɗan yawa ta sa masa, flask din da yaga ta ɗebo a ciki yasa hannu ya buɗe da niyyar karawa sedai wayam babu komai se ƙamshin kosan dake tashi.

Be san me yasa yaji haushi ba amma har se da ya É—ago ya wurga mata harara lamarin da ya sa salma zaro ido tare da buÉ—e baki tana kallon sa, hararar ta ya kuma yi tare da janye idanun sa se kuma ya sauke ganin sa kan plate din ta dake É—auke da kosai kusan bakwai da bata kai ga cinye wa ba, be tsaya wani tunani ba yasa hannu ya janye shi zuwa gaban sa ya cigaba da ci, tagumi kawai salma tayi tana bin sa da ido har ya cinye mata kosan a gaban idanun ta, tissue tas aya goge bakin sa sannan ya wuce ta zuwa falo dan tuni twins har sun Gama nasu break É—in.

Zama yayi cikin su suna maganar da bata san meye suke cewa ba sedai tana hango yadda yaran ke dariya tare da sake shigewa jikin sa, a lokacin itama ji tayi kamar taje ayi maganar da ita sedai sanin she's not welcome yasa bata ko daga daga kujerar ta ba har suka gama ya mike bayan yayi musu peck sun masa , hannu ya daga musu tare da nufar ƙofa alamun ze tafi aiki.

Se lokacin ta samu damar kallon shi dan in Yana zaune ko tsaye kuma yana fuskantar ta bata iya daga kai ta kalle shi dan ji take yi gana ɗaya ya cika wajen har bata iya shaƙar iska sosai.

Dark blue din Armani suits ne a jiki sa da suka karɓe shi kamar dama dan shi aka kirkiri kayan, daga yadda ya juya ya na tafiya kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar ya cika cikakken namiji dan iya takun sa ya shaida maka hakan.

Taki ne yake yi cike da karfi da jarumta hadi da isa ga kuma yar sassarfar da yake yi kaɗan da ta kara ƙawata tafiyar tasa da har tasa salma shagala wajen kallon sa batare da ta sani ba se neman sa tayi ta rasa, ya fita!.

Hannu yasa ta shafa fuskar ta tana ɗan jujjuya kai kafin kuma ta tallafi haɓar ta cikin tunani

..'meke damun ki ne salma?'...

Haka ta tambayi kanta, eh mana dole ta tuntubi kan ta dan daga juya zuwa yau gaba ɗaya indai zata kalle shi se yanayin ta ya sauya, duk ƙarfin da ta tashi dashi se taji ya zagwanye kasa ta lulluɓe ta, ita kuwa in bata tambayi kanta meke damun ta ba wa zata tambaya.

Yau kam su Ifty kawai ta bari suka yi wasan su su kaÉ—ai batare da aya shiga cikin su ba dan gaba É—aya ji take kamar bata da lafiya, hakan yasa ta wuni a kwance har bacci ya sadado ya sace ta.

Ba ita ta farka ba se dab da magriba, sosai ta rude da tambayar yaran me suka ci suka ce mata sun sha fresh milk hakan yasa hankalin ta dan kwanciya.

Da ruwan zafi sosai tayi wanka dan ta watsar da kasalar baccin da tayi kana ta saka Pakistan ruwan kasa ta wuce kitchen bayan ta É—aure kan ta da mayafin kayan dake siriri ne baze yafu ba.
Chapter 35 · 0% Book details