← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 44

Sashe 34

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Auren ku da Abu Aulad aure ne da yazo cikin wata siga da ba haka aka saba gani ba, aure ne da ya wanzu bisa tsarin ubangiji, baki taɓa sanin Abdallah ba se da kika fara aiki dashi haka shima be san ki a wani matsayi ba face na ma'aikaciyar sa sedai tashi ɗaya Allah ya canja komai bisa hikmar sa ya juya lamura yada ba'a taɓa zato ba yanzu ga ku a matsayin mutane mafiya kusanci da juna, wato ma'aurata, shin salma kin taɓa tunanin yaya rayuwar mijin ki kafin yanzu?, Ma'ana kin taɓa sanin tarihin mijin ki?, Waye shi?, Yaya rayuwar sa take tun daga yarinta har zuwa bigiren matashi ko ince magidanci da yake kai?".

A hankali salma ta girgiza kan ta alamun a'a.

"Ba zance mijin ki be tashi cikin farin ciki ba, ba zance mijin ki be ji dadin rayuwa a baya ba sedai Zan ce mijina yanzu mijin ki na yin wata bahaguwar rayuwa ne da babu ki dison farin ciki a cikin ta, babu kwanciyar hankali balle ayi maganar jin dadi.

Mutane ko ince makiyan dake kewaye dashi sun haddasa masa wani ciwo a ransa, ciwon da yasa rayuwar sa take tafiya a baibai, ba komai ban face ciwon rashin yarda wanda shekaru biyar baya be yi girman na yanzu ba sedai faruwar wani al'amari ne girma ya sake juya rayuwar sa zuwa matakin da yake kai yau, mijin ki be yarda da kowa ba ciki kuwa har da Ni, so da yawa yakan yi kamar ya yadda sani sedai in yayi wani abun se ki ga akasin haka.

A halin da ake ciki ba shida wata rai mafi kusanci dashi da ta sanshi ciki da bai kamar ni sedai yardar dake tsakanin mu ba wai ta kai ta kawo bane, a baya nace miki baze ci abincin ki ba yanzu dan be gama sanin ki ba sedai ba haka bane, be yarda da kowa bane balle har ya aminta ya ci abinda ya fito hannun ki.

Wani sa'in yakan bani haushi sedai in na zauna nayi nazarin irin rayuwar sa da mutanen da ke zagaye dashi se inga be yi laifi ba, kar in jaki da nisa a yanzu zaki san wane ne mijin ki ABDALLAH ABDULSALAM GAMJI.

kamar yadda kika ji na faÉ—a yanzu wannan shine cikakken sunan sa, mahaifin sa Alh Abdulsalam haifaffen gari ko ince local government É—in Gamji ne dake garin nan.

Tun ainahin kakannin Abu Aulad masu rufin asiri ne ko ma ince masu kudin da ne dan suna da arzikin su sosai wannan yasa magidan su ba ɓoyayyen gida bane, ko yanzu kika tari ne napep kika ce masa gidan Ahmad Gamji har kofar gidan za'a kaiki duk da babu kakannin nasa se yan uwan su dan duk sun mutu.

Abdulsalam Gamji baban Abdallah dan kasuwa ne cikakke wanda ke tafi da kasuwancin nasa da zamani dan tayi ilimin sa har matakin Masters, tun yana matashin sa sunan sa yayi fice a garin nan dan a lokacin babu matashin da yakai shi kudi da suna.

Be yi aure ba se da yakai shekaru talatin da hudu saboda tsaikon da aka samu, manya da yara a lokacin ba wanda be san irin so da kaunar da Abdulsalam ya gwada wa Fahima ba wato mahaifiyar Abu Aulad dan a kan hidimar ta barin komai yake yaje gare ta, be yadda ta shiga motar haya ba haka be yarda da samar nata drivern ba, shine yake tuka ta duk inda zata ya kuma maida ita gida.

Tsaikon da aka samu ba komai bane illa Hajiya Rahma babar sa wato kakar Abu Aulad da ta yi tsalle ta dire tace Bata San zance ba dan ta baze auri wadda ba'a san asalin ta ba dan Fahima marainiya ce dake rayuwa cikin gidan marayun garin nan, duk yadda Abdulsalam ze yi dan ganin mahaifiyar sa ta sauka daga kan ra'ayin ta yayi amma ta ki, mahaifin sa Ahmad ba mutum ne me zafi ba shiyasa kullum tsakanin sa da haka Rahma nasiha ce amma hak ta kafe taki sauraren kowa inda a ƙarshe se hakuri mahaifin nasa ya bashi kan yayi wa mahaifiyar sa biyayya.

Hajiya Rahma da kanta ta nemo wa Abdulsalam aure a can dangin ta, duk da Abdulsalam be so ba haka ya hakura ya aura Safiyya dake amsa sunan Hajiya Babba a yanzu, auren Safiyya da Abdulsalam seda yayi kusan shekaru huɗu amma bata taɓa ko batan wata ba balle a sa rai da samun ciki, wannan ya tashi hankalin Hajiya Rahma ta fara nuna ita fa ta gaji da jira kawai ya ƙara aure, anyi tashin hankali sosai inda Hajiya Babba ta murje idanun ta ta fesawa Hajiya Rahma rashin kunyar da ba wanda ya taɓa zaton zata yi wanda hakan yasa Hajiya Rahma ƙudure niyyar se ta nuna mata tana da cikakken iko da ɗan ta.

Bisa wannan alwashi nata Hajiya Rahma ta bawa baba izinin auren masoyiyar sa Fahima, dake abinda dama zuciyar sa bata taɓa fidda rai ba ne baba be bata lokaci ba wajen tunkarar shugabannin gidan marayun dan har lokacin Ummu wato Fahima bata yi aure ba.

Cikin kankanin lokaci aka yi komai da ya kamata ciki har da daurin aure Ummu ta tabbata mata ga baba, hajiya Babba bata raina kan ta ba se da Ummu ta tare, irin rawar jikin da baba yake a kan ta dole ya tabbatar wa duk wanda ke kuwa irin matsanancin so da kaunar da yake mata hakan kuma shi ya assasa matsanancin kishin Ummu a ran Hajiya Babba kishin da ya dinga rikidewa har ya koma tsananin tsana da ƙiyayya.

Tsananin ƙiyayyar da Hajiya Babba ke wa Ummu yasa ba abinda take burin gani face mutuwar Ummu sedai dake Allah ba'a masa dole kullum Ummu kara lafiya take yi dan ko ciwon kai bata taɓa yi ba har ta shekara a gidan.

Shekara daya da rabi ciki ya wanzu a jikin Ummu, cikin da ya siyo mata matsananciyar soyayya da ƙauna wajen Hajiya Rahma dan ba abinda take burin gani face zuri'ar dan ta tilo wato baba.

Afuwan a farko ban sanar dake ba, baba su biyu ne a wajen mahaifin su, shi daga wajen Hajiya Rahma se baffa wato Usman daga wajen abokiyar zaman ta.

Irin yadda kowa ke so da daukin cikin Ummu yasa seda Hajiya Babba tayi iya yinta wajen ganin yabi rariya ma'ana ya bare, bakin cikin da ahalin suka shiga saboda barewar cikin bane bayyana bane.

A takaice dai tun daga wannan cikin Ummu seda tayi bari sau uku a jere wanda a karshe likita ya bayyana musu ai a abinci take cin maganin zubar da cikin, bincike na sosai baba yayi inda daga ƙarshe ya gano ba kowa ne da wannan aikin ba face Hajiya Babba.

A bisa wannan dalilin har sakin ta baba yayi , seda tayi watanni biyu a gida kafin ya dawo da ita bisa umarnin babansa Alh Ahmad dan iyayen ta kullum se sun kira shi suna bada haƙuri.

Komawar Hajiya Babba gidan be sa ta rage komai na bakin halin ta ba sema karuwa da yayi, sedai ba kamar baya ba yanzu tana ɗan ɓoyewa.

Dawowar ta da yan watanni ta samu ciki, abinda ya dadada mata kenan dan lokacin Ummu shiru kake ji ba labari.

Duk wani iyayi da feleƙe da take yi Ummu bata taɓa ko kallon ta ba balle ta kula ta sema taya baba kulawa da ita tare da nuna son abun dake cikin da tayi hakan yasa daraja da kimar ta karuwa a idanun baba.

Cikin ikon Allah ciki yakai watan haihuwa inda ranar haihuwa nayi ta haifi yar ta mace me tsananin kama da ita , sam Hajiya Babba batayi wani murna da haihuwar Saudah ba dan ita kam ba mace taso haifa ba namiji taso yadda zata mulki kowa yadda take so tun da ta haifa magajin family.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya Saudah na girma har ta fara tafiya kafin ciki ya sake ɓullo wa jikin Ummu, irin murnar da baba yayi zaka ce ba'a taba masa haihuwa ba, bakin cikin Hajiya Babba ya dawo sabo domin tun fitowar cikin Hajiya Rahma ta sa baba ya dawo da Ummu wajen ta dan tace ba zata kuma yadda a salwantar mata da jika ba.

Allah Al- baseer se ya bawa Ummu haihuwar namijin da Hajiya Babba ke kulafucin haifa, yaron ya zo da tsananin kyau da kwarjini kamar baban sa, farin jini kuwa se wanda ya gani dama kun san jarirai da farin jini to nasa kam na daban ne.

Seda Ummu tayi arba'in kafin Hajiya Rahma ta yadda ta koma gidan ta inda ta cigaba da kulawa da Abdallah, soyayyar da baba ke nunawa Abdallah a fili take kuma a bayyane, fita dubu shiga dubu se ya kawowa Abdallah tsaraba, magana dari in se yi se kaji sunan Abdallah hamsin, son kuma ya samo asali ne da yadda yaron yake tamkar photocopy din sa, ga kuma kula da yake samu daga mahaifiyar sa Ummu da yasa yayi bulbul kullum cikin ƙamshi da ado.

Lokacin da Abdallah ya shekara biyu kuwa se ya zama duk inda baba zashi Abdallah na tare dashi, hatta office kuwa da Abdallah yake tafiya, ko da Ummu ta faÉ—a wa Hajiya Rahma dan tayi masa magana ba ta yin ba se ma Ummun da ta rufe da fadan in be fita da É—an sa ba wa ze É—auka ya fita da, dole haka Ummu ta hakura ta zuba ido.

Baba be daina fita da Abdallah ba se da ya kai minzalin shiga makaranta, shima kuma kullum shi ke kai shi driver Kuma ya É—auko shi, in aka dauko shin maimakon gida sedai a wuce dashi wajen sa a office, a wannan karon kam Alh Ahmad ne yayi magana ya tsawata masa kan hakan da fadin ya bar yaro yayi karatu sosai.
Chapter 34 · 0% Book details