← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 44

Sashe 38

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da baba ya tuntuɓi Abu Aulad da maganar nuna masa yayi babu mace yanzu a gaban sa yayinda shi kuma baban ya dage dan a ganin sa a shekarun Abu Aulad 28 a lokacin ya kai minzalin da ze yi aure dan yana buƙatar ganin zuri'ar sa kafin shima lokacin sa yayi.

Farin cikin da Hajiya ta shiga lokacin ba kaɗan bane dan jin za'a aura masa yarinya mara galihu me kwana ƙarƙashin gada hakan yasa ta shiga zuga baba cikin kissa har se da ta tabbatar an yi auren.

Rayuwar Abu Aulad tare da nafisa ba wata abar ƙarar wa bace dan be saki jiki da ita ba kasancewar tun yana University ya daina ci da shan komai na gidan nasu bisa wani al'amari da ya faru da har yau be sanar dani ba sedai abun ya taba shi sosai ya kuma saka masa rashin yarda da mutanen duniya har ma da wanda ke amsa sunan ahali a gare shi.

Shekarar su biyu da nafisa batare da ya kalle ta a matsayin mata ba kafin Allah ya karkato da hankalin sa kanta ya ke mu'amalantar ta kadaran kadahan dan duk wanda ke tare dasu ze gane sam babu soyayyar nafisah tare da Abdallah, yana dai zaune da ita ne saboda baba, Shekara biyu da rabi da auren su ta sami ciki, cikin da sanadin sa nafisa ta san waye Abdallah saboda tsananin kula da tarairaiyar ta da yake yi, soyayya da kaunar da yake wa cikin tun kan yazo duniya daban ce hakan yasa ta dinga jin kamar kar ta haihu dan tasan wannan soyayyar ba tata bace ta cikin ce.

Ranar da ta haihu kuwa anga fara'a da dariyar Abdallah kamar baze daina ba, karin farin cikin sa da ta haifi yan biyu duka mataaa..............✍🏻.

Kwana biyu bana editing ku karba da har pls👏.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 026 [12/12/2022 11:13 AM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

                      Paid page 026

_________________________📖 Tun da akayi haihuwar Abu Aulad ya tare a wajen ya'yan sa, ba ruwan sa da yan barka haka ze yu zaune a daki riƙe da ƴaƴan yayi ta kallo yana murmushi kamar wanda ya sami tabin hankali, yan barka kuwa da ƙyar yake bada yaran a kai musu wasu ma sedai suyi Barka batare da sun ga ya'ya ba suna wajen uban su.

Sunan da akayi a lokacin seda duk faɗin ƙasar nan ya amsa saboda yadda ya kashe kuɗi yayi wadaƙa, sutturar yaran iya wadda ya siyo musu se an bude madaidaicin shago dan daki guda aka cika da kaya, hatta uwar yaran seda ta san ta haifi ƴaƴan gata dan akwati Ashirin da hudu yayi mata na haihuwa abinda ko a lefen ta be yi rabin sa ba.

Raguna kam akori kura aka ciki da su aka dinga yankawa kawai, kar ki ce ƙananan raguna, sam irin wnada suka ci suka koshi har kamar zasu fashe dan kiba, banda shanu uku da aka yanka.

Kai hidimar da Abdallah yayi a haihuwar yaran nan ba zata fadu duka ba dan se mu cinye dan Lokacin da muke dashi ban gama wassafa miki ba.

Wani abin jin dadin kuma kwanan su biyu a duniya ya ajiye aikin da yake yi a Companyn baba sabida ya gama ginin nasa na kan sa budewa kawai ya rage dan hatta ma'aikata an gama diba, ranar suna mata na bikin suna a gida mu kuma muka yi namu bikin bude Company É—in wanda ke amsa sunan A.A GAMJI CONSTRUCTIONS.

Ko ban faÉ—a ba nasan kin fahimci wannan Company É—in nake nufi, cikin hikima da taimakon Ubangiji muka fara aiki tukuru domin dai Abdallah bai yarda ya dauki unqualified workers ba, duk wanda kika gani a Companyn nan sai da ya tabbatar da cancantar sa kafin ya bashi aiki.

Kafin kice me A.A GAMJI CONSTRUCTIONS yayi suna a faÉ—in garin nan saboda nagartar aikin sa, sannu a hankali ya fara zama well recognize sabida kwazon ma'aikatan, ban ga laifin wanda suke yabon Abdallah kan yadda ayyukan Company ke tafiya ba dan a rubuce yake da ba'a sami jajirtaccen shugaba ba kamar sa ko da kuwa an iya ba lallai ayi mai karko kamar yadda ake yi yanzu ba, sedai Abdallah ba me sakaci ko wasa ne akan duk abinda ya shafi aiki ba, tsayayyen mutum ne me ra'ayi da akida dan baya shakkar hukunta duk wanda ya taka doka, hukuncin da ko da kuwa kora ce ta kama dan yace duk maaikacin da yake tunanin ba za'a iya sallamar sa ko hukunta shi saboda wani baiwa nasa, ilimi ko kwarewa ba to ya gwada taka É—aya daga cikin dokokin aiki.

Da taimakon baba muka kai matsayin da Companyn yake a yanzu wato sananne a kasa baki daya domin kuwa ya shiga ya fita ya haÉ—a mu da manyan mutane sosai, mu kuwa kokarin mu shine yi musu aiki ne inganci ta yadda gobe su da kan su zasu bukaci service É—in mu kuma mun yi Nasara domin hatta da shugaban kasa yana bamu kwangilar gine gine ban da kuma yan siyasa.

Ina nace zan zauna lissafa miki nasarar da Companyn nan ya samu daga shekarar buÉ—e shi zuwa yanzu tabbas zamu iya wuni bamu gama ba sedai koma me ya zama kokarin Abdallah ne sannan a zo kan mu da ragowar ma'aikata.

Nasan zaki ce me yasa kai baka nemi aiki a wani wajen ba se karkashin Abdallah bayan matakin ilimin ku daya ne haka kuma kwalin ku, ba komai ne ya zaunar da ni tare da Abdallah ba face shaƙuwa, ƙauna da kuma halin sa domin nima mahaifi na da nasa dukiyar daidai gwargwado, nasan ba zaki rasa jin As-saif motors ba, to ire iren su duk na babana ne.

A haka zaki yi wa Abdallah kallon baudadden mutum, miskili mara dadin sha'ani, me girman kai da wulakanta mutane ko kuma me É—agawa ko?, To sam wannan ba Abdallah kika suffan ta ba.

Shi ɗin mutum ne me sauƙin kai, nagartacce me hakuri da kau da kai, ba shi da wulaƙanci sedai yana da miskilam ci wanda wannan kuma dabi'a ce kuma halayya tasa da har abada ba Wada ya isa ya sauya masa domin haka me kowa ya yo shi, Abdallah bashi da girman kai sedai yana da gudun wulaƙanci, ya tsani rashin kunya haka kuma yana raba hanya da duk me yin ta, matsala ɗaya a halin shi itane rashin yarda wanda zan iya ce miki ba halin sa bane rayuwa ce ta koya masa bisa tilas haka kuma in dai kika kiyaye abinda duk ze yi zargi ki ka zama me gaskiya da riƙon amana da sannu zaki rabashi da ita dan ba halin sa bane koya yayi.

Mu dawo ga labarin mu salma, bayan haihuwar twins sosai budi yake sake shigowa rayuwar Abdallah dan cikin wata ɗaya da buɗe A.A Gamji constructions ya buɗe GAMJI SHOPPING MALL Wanda ake wa lakabi da GSM inji mutane, bayan shi kuma ya fara ƙoƙarin buɗe shagon sai da wayoyi sedai hakan be samu ba saboda ƙaddarar da ta faɗo rayuwar sa a lokacin, ƙaddarar da ita ce ta tafi da sauran fata, buri, jin dadi, walwala, hadi da kwanciyar hankalin Abdallah.

Kamar yadda muka saba in ze yi tafiya to dole ni ya kasance ina nan saboda kula da harkokin kamfani, in Kuma Ni zan tafi to shi ze zauna.

A wannan karon tafiyar tasa ce dan nine nayi ta karshe kasancewar kamar shifting muke, wannan karon in naje, next shi kuma se yaje, ba komai yasa tafiyar ta zama me mahimmanci ba sedan zeje ya gana da Companyn infinix, Samsung, iPhone, Huawei da ragowar manyan kamfanonin waya saboda shagon da ze buɗe, kar dan nace shago ki ɗauka wai ƙaramin waje ne, no babban estate ko ince miki complex muka gina wanda gaba ɗaya ze zam ba harkallar da ake yi cikin sa face wireless business, ciki shine y hada da wayoyi, computers, manyan headphone, da dai duk abinda ya shafi hakan.

Wannan tafiya itace ta zame masa bakar tafiya shiyasa ko daga baya be kuma sha'awar harkar ba se ma Saida complex din da yayi.

Har airport na kai su shida twins da maman su, tun da muka shiga Mota yaran na hannun sa har muka kai airport ɗin, ko da muka je ba'a fara diban passengers din da zasu tashi ba saboda ana servicing jirgin, haka ya zauna a kan kujera ya ƙanƙame yaran duka biyu a ƙirjin sa kafin ya ciro su ya zubawa fuskar su ido, kallon su yake yi ba ko ƙiftawa fuskar sa cike da wani yanayi, hakan ba bakon abu bane gare mu ni da maman yaran sabida in ze yi tafiya haka ze ta kallon yaran kamar yayi kuka dan baya son yin nesa da su ko kadan.

Ko da aka fara kiran mutane be bada yaran ba har aka dinga kiran sunan sa kafin da ƙyar na amshe su a hannun sa na mikawa nafisa, idanun sa cike da ƙwalla ya juya ze shige nafisa ta kira shi cikin wani murya me rauni wadda tasa dole y dakata tare da juyowa, kallon ta ya tsaya yi kafin da ɗan sauri ya dawo wajen su ya haɗa da ita da yaran ya rungume gaba ɗaya har tsayin mintuna kusan uku kafin ta fara janye wa jin ana sake kiran sa, hannun sa yasa ya riko fuskar ta karo na farko ya fara share mata hawayen da ke gudu kan kuncin ta sannan yayi pecking goshin ta

"Na yafe miki mom twins".

Ya faÉ—a dan yasan se ta nemi tafiyar sa dan haka take masa duk lokacin da ze yi tafiya, lumshe ido tayi hawaye na sake gangaro mata

"I love You Abdallah, ina son ka Daddyn twins".
Chapter 38 · 0% Book details