← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 44

Sashe 17

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata iya jayayya da na gaba da ita ba shiyasa se kawai ta miƙe ta hau tattara komai kamar yadda yace tana ajiyewa inda ya kamata, sassanyan ƙamshin sa me sa nutsuwa da kwantar da hankali ne ya ratso wajen yana shaida musu isowar sa kafin kuma cikakken takun sa ya sake bayyana shi ɗin.

Juyawa Haisam yayi yana kallon shi yayin da ita kam ta cigaba da abin da take yi tana sake kai kanta ƙasa.

Musabaha suka yi da Haisam sannan ya wuce office É—in sa Haisam na rufa masa baya.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama haÉ—a komai se kuma ta É—auka ipad É—in da take kai masa schedules ta fara takawa zuwa office din.

Knocking biyu Haisam ya amsa mata ta shiga a hankali bakin ta É—auke da sallama, gefe dashi ta dan rusuna ta gaida shi kamar yadda ta saba kana ta aje masa ipad É—in a gaban sa ta shiga yi masa bayani, seda ta kammala kafin ya ja wayar gaban sa yana sake duba komai, da hannu yayi mata alamar komai yayi dan haka ta juya zata fita

"Be kamata ta zauna a office ba bayan jiyan nan tayi aure yau kuma ta tare dan haka nace ta koma gida".

Tsayawa da duba takardun gaban sa yayi batare da ya É—ago ba kafin cikin Muryar sa ne amo ya bawa Haisam É—in amsa

"Shi kuma aikin waye ze to mata, kar ta sake take ko ina se lokacin tashi".

Iya nan ta tsaya ta saurara so tana jin abinda yace ta fice tare da komawa wajen zaman ta ta fara daidaita kayan aikin ta, seda ya tabbatar ta rufe kofar kafin ya kalle shi cikin jin haushi

"Kai dai wallahi baka iya abin arziƙi ba, fisabilillah wane irin aiki zata zauna tayi ita dake matsayin amarya, a ƙa'ida kamata yayi tana gidan ta tana hutawa kai kuma kana mata hidima, duk wannan be samu ba kuma se ka kasa barin ta a gida se ta zo wani aiki?, Mtsww".

Be ce masa komai ba se da ya gama duba takardar hannun sa ya ajiye sannan ya daga kansa tare da wurga amsa banzan kallo.................. ✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 012 [ 12/5/2022 10:24 AM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

                        Paid page 012

_________________________📖 "sedai kallon amma a buge dai bazan bugu ba, ayi bawa da shegen baƙin hali".

Haisam ya faɗa yana hararar Abu Aulad sbd mugun kallon da yayi masa, banza Abu Aulad ɗin yayi masa ya cigaba da aikin sa dan yasan in ya biye wa Haisam ba zasu tsinana wani abun arziki ba  yau ɗin bayan ayyuka ne zokar ke jiran su.

Kwana ukun da suka yi basu zauna ba sosai ayyuka suka taran musu barin ma da ya kasance dashi da Haisam É—in gaba É—aya ke ciki busy ba wai mutum É—aya ba.

Ganin fa dagaske ba kula shi zeyi ba yasa Haisam ficewa daga office din Yana maganganu ƙasa ƙasa na haushin Abu Aulad na hana salma komawa gida ga kuma baƙin halin sa na Shariya da yayi masa duk da inda sabo yaci ace ya saba.

Hankali kwance take ayyukan ta kamar koyaushe dan ita kam taji daɗin zaman ta anan, Allah ya sani cikin ranta fargaba ne da tsoro na irin zaman da zata yi da mutan gidan da ƙaddara ta jefa ta rayuwa cikin su.

Ba wai kanta kaÉ—ai ba, hatta Æ´aÆ´anta tana da fargaba akan su, su É—in sune mahimman ginshiki kuma katangun rayuwar ta da bata jin zata iya standing wani abu ya same su komai kankantar sa kuwa.

Ji take yi akan su tana iya komai ko da kuwa za'a kashe ta ne, tana iya bada rayuwar ta domin tasu dan a gare ta rayuwa babu su gwara ace itama babu ita.

Kiran Sallar zuhur dake tashi cikin daddaÉ—ar Muryar ladanin madaidaicin Masallacin dake cikin Company É—in yasa ta dakatar da aikin da take yi cikin system ta danna mata sleep.

A nutse kamar yadda ya zame mata jiki ta nufi masallacin dan a can take alwala ta gabatar da sallar ta sannan ta dawo.
Gaisawa ta shiga yi da duk ma'aikaciyar da suka haɗu cikin kiyaye mutuncin kai da kuma mutunta jama'a, wasu dama ta sani ba dan Allah suka ringa gaisawa da ita ba a yau dan da yawa basa ko yi mata magana saboda ganin yadda ta samu kusanci me girma da boss din su, muƙamin ta na secretary ɗin sa ba ƙaramin bata musu rai yake yi ba hadi da assasa hassada da ƙyashin ta a ran su dan da yawa wannan matsayin suke nema ido rufe sedai basu samu ba.

Scarf din ta da ta cire dan shafar kai ta ke kokarin daurawa shafi bisa tilas ta dakata dan jin wasu maganganu da tayi

"Aikin banza da wofi, meye abin wani daga kai da wani budawa kan auren da mun san duk yadda akayi kutunkutun har aka yi shi, auren da ba'a gina shi kan gaskiya ba".

"Ke Laila, kiji tsoron Allah fa, waye ya faÉ—a miki ba'a yi shi kan gaskiya ba".

Matashiyar da aka kira da Laila ta yamutsa fuska kafin cikin yanayin da yake nuna tabbacin abinda take faÉ—a ta shiga bawa dayar amsa

"An faÉ—a miki kowa ma irin ki ne da baya wani zurfafa tunani yake yadda da komai da ya gani haka kawai, nifa ba irin tsarin mu É—aya ba Umah, ke wai ko abinda ya faru yau be isa nuna miki cewa auren ba shi da wata manufa ba, haka kuma akwai wata makarkashiya a cikin sa ba?".

Dan ƙifta idanu Umah wadda asalin sunan ta umahmatu ne tayi

"Ni banga komai ba haka banyi sensing komai ba, in Zaki faÉ—a min kawai ki faÉ—a".

"Amma wallahi kin ban mamaki, ban ɗauka rashin tunanin naki ya kai can ba, ke yanzu kin taɓa ganin inda amaryar jiya jiya tarewar ɗazu ɗazu ta fita aiki?, Amaryar da ya kamata ace tana can gidan ta cikin farin ciki yayinda mijinta ze kasance kusa da ita suna shan soyayya, se ga amarya ta buge da zuwa office, haka shima angon har wa yau kuma fuskar sa a haɗe cif ba alamar yana farin ciki karewa ma se sabon kunci da yake yi".

Shiru Umah tayi kafin kuma ta gyada kai a sanyaye

"Kuma fa hakane Laila, amma kuma me yasa ya aure ta in har baya son ta, ni wallahi har ta bani tausayi dan maza irin su boss wuyar sha'ani gare su, ita kuma gata da kirki, ba ruwan ta wallahi, nikam ta dade tana burge ni".
                      
"Kirkin munafukai ba, ke irin su fa wallahi da zaki tona cikin su se kinyi mamaki, Ni bama wannan ba, a wajena da auren su da babu duk ɗaya ne kuma yanzu ne ma na ɗaura sabuwar ɗamarar so da ƙaunar boss".

"Amma wallahi kin daura aure da wahala kuma in bakiyi hankali ba tsaf kin kusa barin aikin nan, gwara kiyi haƙuri ƙi sawa kanki salama dan ke kanki kin san yafi ƙarfin ki".

Yamutsa fuska Laila tayi cikin jin haushin kalaman Umah

"Banda rainin hankalin ki a ina kika taɓa ganin namiji yafi ƙarfin mace, aiki kuma da kike magana an gaya miki Ni mahaukaciya ce da zan tare su in ce ina son sa balle har ya kore ni, ki zuba ido kiyi kallon yadda zan buga wasa na kuma ya tafi cikin tsari, so kuma na maimaita miki yanzu na fara haka in kika ga ban aure boss ba to mutuwa nayi".

Tana gama faɗa tayi gaba cikin jin haushin wai ita Umah zata cewa tayi haƙuri ta cire boss a ranta ya fi karfin ta, aikuwa zata bata mamaki.

Itama Umahn fita tayi daga wajen dan dama wanke fuska ta shigo yi ba sallah zata yi ba.

Jiki a matuƙar sanyaye salma ta daura scarf din ta tare da maida hijab din ta wuce cikin masallaci, kauda komai tayi daga ranta ta gabatar da sallar ta cikin nutsuwa yayinda cikin kowace sujud take kaiwa Allah kukan ta.

Bata san ta ina zata fara da wannan yakin da yake tunkaro ta ba, ita ɗin me rauni ce, bata da gatan kowa bayan Allah da Manzon sa, rayuwar ta ba irin ta kowa bace haka salon labarin ta yasha bambam da na kowa, ita kwallin ƙwal ce cikin filin yakin yayinda mahara suka yi mata zobe gabas da yamma, kudu da arewa suka sata a tsakiya.

Ta ina zata fara ne?, Da waye ya kamata ta fara?, Dashi mijin da ya aure ta dan kare mutuncin ta kamar yadda ya faÉ—a ko kuwa da salon pretending din sa na nuna yana son ta gaban jama'a kamar yadda taga yayi a dazun, a'a ko kuwa da mutanen gidan da zata fara sabuwar rayuwa dasu wanda alamu suka nuna in har baya jajirce ta kwaci kanta ba tabbas zata sha bakar wahala, a'a ko kuwa rayuwar ta da ta Æ´aÆ´anta zata fuskanta, bata damu da irin su Laila ba dan bata da damuwa da su, ba so da kauna ba ko haÉ—iye shi zata yi bata da matsala da hakan.

Ta daÉ—e da idar da sallar sedai bata tashi ba seda ta ji bata da sauran basirar yin addu'a sannan ta shafa, sake gyara zama tayi ta shiga tunani wanda ya É—auke ta lokaci me É—an tsawo kafin ta farga ta mike ta fita.

Deliveryn da ta saba siyan abincin restaurant din su tuni ya kawo mata abinci ya ajiye kan table É—in ta ganin be gan ta ba, sanin ta riga da ta biya kuÉ—in yasa ya ajiye mata ya tafi.

A hankali ta ringa tsakurar abinci wanda bata wani ci da yawa ba saboda damuwa da ta cushe mata ciki, haka dole ta tattara ta ture shi gefe ta cigaba da aiki.
Chapter 17 · 0% Book details