← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 44

Sashe 29

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan sune ginshikan jin dadi sedai kuma a cikin nasu kuma muhimmin shine kwanciyar hankali, Allah ka wanzar da kwanciyar hankali a zukatan mu, unguwannin mu, garuruwan mu, kasashen mu da ma duniya baki daya.

A hankali salma ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta zo nan a tunanin ta tare da cire tagumin ta wanda bata san sanda tayi ba..................... ✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 021 [ 12/9/2022 12:40 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

                    
                      Paid page 021

_________________________📖 Da kallon banza ta raka bayan Nuriyya tare da jan tsaki kana ta tashi ta sakawa kofar key dan bata bukatar wata hayaniya kuma bayan wadda tayi yanzu su kuma ta fahimci ahalin gidan ba abinda suka fi kwarewa a kai kamar neman rigima da faɗa.

Kan kujerar ta koma ta zauna tana sake bitar kalaman Nuriyya daki daki, wani tsakin ta kara saki ganin wai duk wannan hakilon da zubda mutuncin duka akan wancan miskilin take yi, mutumin da ita banda kyau da iya daukar wanka bata ga abinda ze sa ayi ta wannan haukar akan shi ba da sunan so.

Tasan tayi karya in tace bashi da abinda za'a so shi domin shi dan tasan shi ɗin ko acikin kyawawan maza nasa kyan daban ne, gashi se kyan ya haɗu da iya ado da gayu, basu kadai ba ko ita in har ze shiryo ya fito se tayi dagaske take iya hana kan ta ƙure shi da ido saboda yadda adon ke zauna wa a kyakkyawan jikin sa, mutumin yasan kala haka yasan takan kaya shi yasa ko a can office mata ke hauka a kan sa dan ma Company ɗin na da strict orders and rules da ta tabbata har dambe se an dinga yi a kashi.

To amma banda wannan kyan ai bai da wani abu da ze sa a so shi, shegen miskilancin za'a so ko kuwa wulaƙanci, Shariya da jan aji, ita in Yana wani abun ma har mamaki yake bata dan ko mace ba kowacce ce zata iya jan ajin da yake yi ba.

Kofar shigowa da take fuskanta ta makawa harara saboda tuno wulaƙancin da yayi mata, ƙwafa tayi tana me jin haushin Nuriyya da ta zo ta katse mata baccin ta kan wani can namiji da baya gaban ta kamar yadda tayi imanin shima bata gaban sa.

Da kyar ta samu ta koma baccin ta wanda bata tashi ba seda akayi sallar Asr dan Azahar kam tun sha biyu da rabi tayi abin ta.

Taji daɗin baccin ba kaɗan ba dan ta daɗe bata yi me tsawo kamar sa ba, wanka ta sake ta saka yar shimi da wando ganin ita kadai ce a gidan, yau kam pounded yam take son ci shiyasa ta dauri niyyar yi, nan da nan ta hau ferayar doya ta ɗora kan gas kana ta koma hada miyar da take son ci da ita,  jar miya zata mata saboda Ifty da bata da lafiya ba zata yi taushe ba kar cikin ta ya saki.

Cikin electric pounder ta nike doyar tayi matukar laushi kana ta malmale su a leda ta zuba a warmer, wasa wasa aikin da ta raina se da ya kai ta har magrib dan ana kiran sallar take kwashe farfesun kayan cikin da tayi.

A gurguje ta gyara kitchen din tare da jera a dining, wanka ta sake ta saka milk din Arabian gown tare da daure kan ta dashi, powder da lipstick da kwallon ta saka kana ta tashi tayi sallah.

Turaren ta me sanyin ƙamshi ta fesa a jikin ta sannan ta fita takarawa falon turaren wuta dan har lokacin basu dawo ba, nan tayi zaune tare da kunna Tv ta Kai zee Aflam daidai suna haska tsohon Film ɗin jarumi Amitabh bachan me suna ganga jamuna saraswati, cikin farin ciki ta gyara zama tare da maida hankalin ta kan Film ɗin dan tun da ta fara kallon Tv a ɗakin hajiya da finafinan India ta fara kuma ba ƙaramin burge ta suke ba most especially jaruman Bollywood.

Seda aka yi sallar isha suka dawo lokacin har ta yi tata ta koma gaban Tv dan film din be Kare ba, kallo É—aya tayi musu gaba É—ayan su ta É—auke kai dan taji haushin yadda ya kwashe yaran su kayi tafiyar su suka bar ta ita kadai a gida kamar wata sabuwar mayya.

Ibty ce ta fara zame hannun ta daga nashi ta tafi ta faÉ—a kan ta tare da rungume ta tana faÉ—a mata sun je unguwa, ko kallon ta kin yi salma tayi, yaga abinda tayi amma ko kallon ta be yi ba maimakon zaman da yai niyyar yi se ya hau kiran Ibty dan dama ita Ifty bata sake shi ba.

"Come on babyn daddy zo muje ayi wanka".

Ba musu itama Ibtyn ta tashi ta koma gare shi lamarin da ya tilasta wa salma buÉ—e baki tabi su da kallon mamaki batare da ta san lokacin da tayi hakan ba.

Suna shiga dakin ya kalli yaran tare da ajiye ledan hannun sa yana sakin smirk ganin yadda ta saki baki tana kallon su kamar wata doluwa, to an faɗa mata shi ɗin na wasa ne, ai shi da yara sedai in be so su maƙale Masa ba amma duk kiwar yaro in dai yazo kan shi dole ne ma ya yarda dashi, ko an faɗa mata a banza yaci sunan Abu Aulad ɗin.

Da kan sa ya tube su Ifty yayi musu wanka kowacce ya daura mata kananan towels din sa na goge kai, cream din sa ya shafa musu kana ya bar su cikin dakin ya fita.

Tana nan zaune inda suka bar ta sedai wannan karon kam tagumi ta buga hannu bibbiyu ta na bin kofar dakin nasa da kallo, yana fitowa tayi zumbur ta miƙe sedai ganin babu twins bayan sa yasa ta koma ta zauna, yanzu ma bece mata komai ba ya shiga bedroom din ta ya ɗebo musu night wears ya fito ya koma ɗakin sa.

Tun daga nan bata kuma jin ko motsin su ba duk su ukun, shi kuwa a can daki haka ya saka musu kayan sannan ya zauna kan bed tare da kwantar dasu a jikin sa ya buÉ—e ledar da ya shigo da ita ya É—auko wani bedtime story book ya Fara karanta musu, sannu a hankali tun suna saurara har bacci ya É—auke su.

Nan kan gadon ya gyara musu kwanciya kana shima ya shiga wanka ya canja kaya zuwa na bacci, seda yayi musu addu'a gaba É—aya har shi sannan ya kwanta bayan ya kashe fitila.

Hajiya salma kuwa ana can falo ana baza idon ganin ta inda twins zasu fito, wasa wasa tun tana duban agogo har ta dena ta zubawa kofar dakin ido, bata ankara ba har sha daya tana nan zaune kafin jiki a saluɓe ta tashi zuwa bedroom dan ta gama sadakar da can za su kwana.

Kwata kwata kasa bacci tayi dan tun da ƴaƴan ta suka zo hannun ta har zuwa jiya basu taɓa raba wajen kwanciya ba se yau, gaba ɗaya se taji gadon yayi mata fadi ita kadai, tayi ta juye juye cikin rashin jin dadi kafin dab da asuba barawon ya lallabo ya sace ta.

Ko da asuba da ta farka tayi tsammanin zata gan su kwance kusa da ita sedai wayam ba kowa a dakin se ita kaÉ—ai, alwala tayi ta gabatar da sallah sannan ta fita nema musu abinda zasu yi breakfast da kuma wanda zasu tafi dashi school dan tayi zuciya itama ba zata kuma neman su ba tun da sun samu bare sun manta da ita da take dolen su shiyasa ko da ta fito falo bata kalli ko inda sashen dakin sa yake ba ta wuce kitchen.

Tana cikin juye ruwan tea cikin flask ya dawo daga masallaci, ta ji shigar shi falo amma se ta share ta cigaba da aikin ta duk da tana so tace masa su fito ta shirya su zuwa school se kuma ta yi shiru ta zuba musu ido taga in school É—in ma shi ze musu shiri.

Aikin ta take inda ta bada dukkan hankalin ta shiyasa bata ji shigowar sa ba se karan buɗe fridge da taji, a firgice ta saki stirrer din hannun ta da take kwabin cake da za suje school da, gaba ɗaya ta maƙale jikin bangon kitchen din idanun ta a runtse bata ko ƙwaƙƙwaran motsi, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai tare da daukan fresh yo din da ya kawo shi kana ya sa kai ya fice, seda ya kai bakin ƙofar daze koma falo kana cikin tattausar Muryar sa kamar ko yaushe yayi magana

"Ba zasu je school ba yau, se Angel ta samu sauƙi".

Yana gama isar da sakon sa ya fice, da sauri ta buɗe ido jin Muryar sa sedai kama aljani ta neme shi ta rasa, shiru tayi cikin tantamar anya shine ko ba shi bane, se kuma sassanyan ƙamshin sa da ya mamaye ilahirin kitchen din ya tabbatar mata da shi ne.

Hararar kofar tayi kafin cikin siririyar Muryar ta ta shiga mimicking abinda ya fada

"Ba zasu school ba yau, se Angel ta samu sauƙi".

Mtsww se kuma ta ja tsaki, ƙasa ƙasa ta shiga gunguni, wani wai Angel Kamar yar sa, haka kawai a ga mutum da ƴaƴan sa ba'a san taya ya haife su ko ya same su ba a ringa neman yi masa fin karfi.

Zaro ido tayi lokacin da ya shigo ya aje cup din tangaran din da yayi amfani wajen shan fresh milk din,

'innalillahi, Allah dai yasa be ji me na faɗa ba'. Ta faɗa a ranta, a fili kuwa se ta ringa satar kallon sa kasa ƙasa dan san ganin alamun ya ji ta ko be ji ta ba.
Chapter 29 · 0% Book details