Sashe 22
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe ido tayi tare da shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren sa da ya tafi ya bar mata a jikin sa, tsananin daɗin ƙamshin turaren yasa salma tunanin anya ta taɓa jin ƙamshin da ya kai shi daɗi da sanyi tare da ratsa jinin jiki ya sanya nutsuwa da kwanciyar hankali cikin jikin mai shaka kuwa?.
Bata farga daga halin da take ciki ba seda Ibty ta shiga jan hannun ta tana kiran su tafi school kafin jiki a sanyaye ta daukar musu baskets din su taja hannun su suka fita.
Yau ma drivern jiya ne ya kai su wnada alamu suka nuna yanzu aiki su yake, zaman su yake yi.
Bata dawo cikakken hayyacin ta ba seda ta ganta bakin Company sannan yake tuanwa da batun sa na kar ta makara anyi rescheduling meeting.
A hanzarce ta sallami drivern ta shiga Company É—in bayan an caje ta, jakar ta kawai ta ajiye ta nufi office din sa tayi knocking, buÉ—ewar da kofar tayi yasa ta shiga bakin ta É—auke da sallama ta ajiye masa ipad É—in schedules a gaban sa kana ta fita zuwa ragowar ayyukan ta.
Ko minti biyar ba tayi da zama ba ya fito, se yanzu ta sami damar ƙare masa kallo ta kasan ido, shirin nasa ba ƙaramin burge ta yayi ba tun bare ma sumar kansa dake kwance luf luf tasha mayuka ta gyaru tsaf kamar ba kan dan nigeria ba.
"Should we wait for you?".
Da sauri ta miƙe jin bakar maganar da ya dankara mata, kai ita wannan dan kusancin da suka samu ya sa ta san shi ɗin ya ƙware a iya fadar bakar magana.
Meeting ne suka yi kan wani babban contract da suke nema, tsare tsare akayi na yadda za'a tsara hall din da zasu sauki baƙi dan a shekara biyu baya ma basu sami babban contract kamar shi ba shiyasa aka tara manya manyan Company ɗin dake da alaka da hakan.
Ana gama meeting kowa ya koma bakin aikin sa inda ita kam take tare da boss Abdallah kan issue É—in wasu takardu.
Huɗu nayi yau ma ta bar office zuwa makarantar su Ibty ita da drivern su da yace sunan sa Tukur, duk yadda take jin ta a gajiye bata zauna ba seda ta yi girki ta gama ta wa yaranta wanka, yau kam da wuri suka yi bacci saboda Ifty da bata jin dadi su kuma a ƙa'ida in daya be da lafiya dayan ma taya shi yake hakan yasa itama Ibty nan da nan jikin ta ya ɗau dumi shiyasa ta basu magani basu daɗe da sha ba kuma suka yi bacci.
Ganin ita daya ce yasa bata fita falo ba tayi zaman ta a bedroom ta buÉ—e sabon Novel din da ta samo ta shiga karantawa.
Sosai hankalin ta ya dauku ga karatun da har bata san shigowar sa ba se sautin buɗe ƙofar dakin sa da ta ji, da sauri ta ajiye wayar tare da fita sedai tuni ya shige har ya maida ƙofa ya rufe.
Zama tayi a falon ta cigaba da karatun ta har yayi wanka ya canja kaya ya fito, a hankali ta miƙe tare da sunkuyar da kanta tana masa sannu da zuwa, a takaice ya amsa mata da Lafiya.
Ganin ya nufi ƙofar fita daga falon yasa tayi saurin fadin
"Angama abinci fa".
Kamar baze tsaya ba se kuma ya tsaya dan rabon shi da abinci tun na daren jiya har yanzu se ko malt da yasha.
Kujera ta ja masa tare da bashi waje ya zauna ita kuma ta shiga serving din shi, seda ta zuba komai ta juya dan tafiya kafin taji shi cikin bada umarni
"Dawo ki zauna". Duk da bata san dalilin zaman ba amma se bata yi musu ba ta dawo taja kujera ta zauna, abincin ya tura mata gaban ta tare da tsare ta da ido alamun taci.
Ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba da hakan dan tasan me yake nufi, wato taci dan ya tabbatar bata saka komai ba, wallahi ba dan Haisam ba da ba zata ci abincin nan ba sedai yaki cin, mutum se shegen rainin hankalin tsiya, in yaci abincin cikin wa ze ciwa, ina yunwar shi take wahalar wa ba wani ba.
Duk wannan maganganun a ranta take yi yayinda a fili ko alamar ɓacin rai babu a fuskar ta, dama fa duk kuri ne, ita kanta tasan ba dan wani Haisam taci ba, a yadda ya haɗe rai ya bata umarnin ko ita wace bata isa ta saba shi ba dan gaba ɗaya se take jin ya cika falon saboda tsananin kwarjini sa, se take jin ta kamar wata kiyashi a gaban shi.
Se da taci kusan loma huɗu kafin ya ja abincin gaban sa yayi bismilla ya soma ci, kafin kace meye ya tashi da na gaban sa haka yasa ta ƙara masa tare da zuba masa fruit juice din da ta hada naturally a cup.
Shi kan sa rabon da yayi irin wannan cin abincin ya manta , wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali yake ji a tattare dashi, ya dade rufe da ido akan kujera bayan sa jingine da kujerar kafin ya buÉ—e ido ya kalle ta, hankalin ta gaba É—aya yana kan karatun da take yi dan haka bata ma san ya gama ba.
ÆŠauke kan sa yayi
"Ki sako hijab muje".
Ɗagawa tayi daga kallon screen ɗin ta kalle shi amma tuni ya maida idanun sa ya lumshe, bata fahimci komai a maganar tasa ba illa ta sako hijab Dan haka ta mike zuwa ɗaki, mintuna kaɗan ta fito jikin ta sanye da maroon din hijabin da ya haska ta matuƙa.
"Na saka". Ta faɗa a sanyaye kanta a ƙasa hannun ta rike da wayar ta, tashi yayi batare da yace mata komai ba ya nufi kofa, sakin baki tayi tana kallon ikon Allah kafin kuma ta girgiza kai ta bi bayan sa.
Tsaye ta sameshi bakin part É—in su, tana fita yasa mukulli ya kulle part É—in sannan ya matso kusa daf da ita wanda hakan ya haifar mata da rashin numfashi na wasu sakanni kafin ta fisgo shi da kyar, tafin hannun sa masu tsananin taushi kamar ba na namiji ba ya saka ya lalubo nata tare da jimkewa cikin nasa sannan ya shiga tafiya.
Bata da zabi illa bin bayan sa amma gaba É—aya ji take kamar ba ita ba, wasu irin abubuwa ke gudu cikin jinin ta yayinda take jin jikin ta yayi mata nauyi dan hatta tafiyar da take yi kusan shike jan ta.
Yanayin da take ciki ya hanata gane part din baba suka nufa wanda suna zuwa kofa yaja ta jikin sa ya zamana rabin jikin ta na cikin nasa haka shima nasa, a lokacin kam ƙiris ya rage ta zube a wajen dan shi kan sa seda ya fahimci hakan sedai be kula ba ya yi sallama ya shiga falon.
Yau ma kamar kullum falon cike yake da ahalin da suka kasance na gidan har ma fiye da rannan hakan yasa jikin salma daukar rawa fiye da da.
Kasan carpet Abu Aulad ya zaunar da ita kana ya zauna gefen ta har jikin su ma gogar na juna ya kuma sa hannayen sa masu taushi ya ruƙo nata tareda sarƙe yatsun su hankalin sa kwance ba wani kunya ko jin nauyi.
Gyaran murya baffan sa yayi wanda ya kasance cousin din baba haka kuma mafi kusanci dashi duk cikin yan uwa, duk da yaji gyaran muryar ya kuma san dashi ake amma be ko kalli wajen ba balle ya nuna yaji har ila yau yatsun su na sarkeda na juna yana murza tafin hannun ta cikin nasa a hankali.
Murya na ɗan rawa salma ta gaisar da baba kana ragowar mutanen da ta gani cike da dakin dan dukkan su sun girme ta se ƙalilan da ba'a rasa ba, kanta na kasa ta gaishe su irin gaisuwar nan ta jimilla banda baba da ta ware, hakan kuwa ba ƙaramin konawa Hajiya Babba rai yayi ba dan a ganin ta ai Salman bata girmama ta ba haka kuma ta nuna bata ɗauke ta da daraja ba tunda bata haifi mijinta ba sedai sanin irin tsiyar da ta shuka musu yasa ta watsar da wannan batun a ranta.
Baba da baffa kaÉ—ai ya gaisar ya É—auke kan shi gefe tare da gyara zama yana sake matse wa salma waje wadda take dan janye wa.
Kau da kan shi baba yayi dan duk suna ganin meke faruwa, cikin ran sa kuwa mamaki yake na yadda akayi Abu Aulad ya zama fitsararre haka dan shi kam a da yasan ba haka dan shi yake ba sam.
"Ka bude mana taron da addu'a Adam".
Baffa dake amsa sunan Adam ya gabatar da addu'a kamar yadda baba ya umarce shi kafin yayi shiru suka shiga sauraren jawabin da baban yake korowa kamar me karantawa a littafi
"Jiya da safe Abdallah ya zo gidan nan tare da wannan yarinya matsayin matar sa wadda ta taɓa aure har ma da albarkar yaya biyu, a kwanaki uku da suka wuce ne yazo yake sanar da ni ya sami matar da ze aura kuma ba kowa bace face wadda aka buga hotunan su a jarida, duk da jaridar bata yi wani tasiri ba sosai amma na nuna ban amince ba, Abdallah be saurari umarni na ba yaje ya auro ta saboda taƙamar shi namiji ne ze iya yiwa kan sa aure haka kuma yana da kudin da ze yiwa kan sa komai ba tare da ya jira niba.