Sashe 23
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsaurin ido irin nashi ya zo min da ita gidan nan matsayin ya dauko matar sa ta tare, a gabanin ayi haka da sati É—aya babar sa wato Hajiya gata nan ta same ni kan batun rashin auren nasa da yadda abun ke damun ranta har ma take sanar da ni in ba damuwa ta yiwa iyayen wannan yarinya shuraiha magana kan hakan domin yarinyar ta daÉ—e tana son shi, nayi farin ciki da maganar domin mahaifin yarinyar sananne ne a wajena dan haka bana da ko dar kan tarbiyyar ta, bayan haka kuma nima zaman sa hakan yana damu na, wannan dalili yasa na yiwa mahaifin nata magana aka san da batun duk da ba sa rana akayi ko something officially ba, a bisa laifin da Abdallah yayi min na aure batare da yarda ta ba yasa na aura masa ita shuraiha a yau juma'a bayan an sauko masallaci.
Ba zan ce dole se ya zauna da shuraiha ba amma zan faÉ—a masa dole in har baze zauna da ita ba to fa itama zaÉ“in sa sedai ya hakura da ita, zaman zaÉ“in sa daidai yake da zaman shuraiha haka ma fitar ta gidan daidai yake da fitar wannan yarinya da ya kawo, wannan shine hukunci na a matsayin na na mahaifin Abdallah, akasin umarni na kuwa sedai ya nemi wani uban ba Abdulsalam Gamji ba".............................âœðŸ».
Ouummey 📚âœðŸ».
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 016 [ 12/7/2022 12:42 PM ]
★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★
_*PAID BOOK*_
Story/written by Ouummey.
Wattpad @ouummey.
From The author of:
*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*
            Paid page 016
_________________________📖 Shiru falon yayi baka jin komai se fitar numfashin mutanen cikin sa seko shessheƙar kukan Nuriyya da ta fara fitowa a hankali, ba wanda ya kalle ta balle ya nuna yasan me take wanda hakan ya dada tunzura ta ta kifa jikin mahaifiyar ta Anna ta fashe da kuka sedai bame sauti bane.
Baffa ne da ya lura Abu Aulad bashi da niyyar cewa komai se kallon su kawai da yake yi, in ya kalli baba se ya kalle shi kamar wanda yake son ganin wani abu na daban a jikin su
"Baka ce komai ba Abdallah bayan kuma kaji bayan nan mahaifin ka".
"Me zance baffa, ina an riga an daura auren, kuma yace umarni ne ko, to kar ku damu na karba, bashi kenan ba?".
Tsira masa ido Hajiya Babba da baffa suka yi dan jin yayi saurin amincewa abinda basu taɓa zato ba, sedai ita Hajiya Babba sam bata yarda da wannan kalaman nasa ba, dole cikin ransa ta san akwai abinda ya shirya, tabbas akwai abinda yake tsarawa.
Takaici ne ya cika ta na sanin bata yadda za'a yi ta iya sanin abinda ya ɓoye cikin ransa, wannan damar kam har abada ba zata taɓa samun ta ba, amma ba komai shima har yanzu be gama sanin ta bane sedai yana gab da sanin nata matuka har ma ya bawa wani labari in yayi ƙarkon kwana fa kenan.
Dogon tsakin da yaja ne yasa Hajiya farga da cewa har yanzu fa yana nan, da sauri ta juya wajen sa tare da riƙe hannun sa biyu tana masa magana da ido dan tasan sarai waye dan ta, be ki ya fallasa komai asirin uban kowa ma ya tonu ba.
ÆŠauke kan sa yayi daga gare ta yana ciccin magani kamar wanda ya haÉ—iyi madaci, abu É—aya ne yasa ya yarda da plan din su, ba kuma komai bane illa son cimma manufar sa, hakan na samuwa kuwa dole ya kwace abinda ya kasance nasa ne mallakin sa shi shi kaÉ—ai batare da uban kowa ba, a wannan lokacin kuwa baze saurari kowa ba ciki kuwa har da ita Hajiyar dake amsa sunan mahaifiyar sa.
Mabiyar sumaya mai suna Nadiya ce ta kalli salma cikin rainin hankali da son tusawa mutum haushi ta shiga fadar maganar da ta san farkon fadin ta amma bata da masaniyar abinda ka iya biyo baya
"To uwargida se ayi haƙuri a dangana a taya miji biyayya ga iyaye dan kin san ana iya canja mata amma iyaye kam ko makwafin su ba a samu, saboda adalci irin na iyayen mu ki kalla fa basu tilasta shi sakin ki ba duk da cewa har wa yau bamu tabbatar da asalin ki ba, auren ki na farko gaskiya ne ko suna?, Yaran sunna ne ko akasin haka amma duk suka kau da kai, aka yi aure ba'a ga ko dangi naki daya ya rako ki ba asalima ni labarin da naji wai zaman kan ki kike, kin ga kuwa ai dole iyayen mu su zaba masa mata mai cikakken asali, tarbiyya da nagarta, ko ba haka ba?".
Wani irin damƙe hannun Abu Aulad dake cikin tafin hannun ta tayi jikin ta na daukar rawa gaf gaf gaf ba dan komai ba se najin ana neman tozarta nasabar ya'yan ta, ana neman shegan ta mata ƴaƴan ta, ƴaƴan da zata iya dafa Alkur'ani ta rantse na sunna ne, ko da ita kanta bata san asalin su ba amma meze kawo maƙiya son hallaka ƴaƴan shege alhalin su masu farin ciki ne in abin kunya ya sami wanda basa so?, Tabbas ma ƴaƴan ta na halak ne kuma wallahi ko daga wajen waye ba zata lamunci a bata mata nasabar su ba ko da kuwa shi wanda ke amsa sunan miji a gare ta ne da kansa.
"Hmm adai bar maganar kawai Nadiya, yara se shegen kyau kamar su suka yi kansu, kin san fa dama ance shegu sun fi ya'yan halak kyau".
Ba zata iya cigaba da zama tana sauraren waɗan nan munanan kalaman a kan yayan ta ba, abu ɗaya ya hanata ramawa da mai da martani wato darajar baba dake zaune a wajen, sedai rantsuwa ce tayi na bashi suka ci kuma se sun biya, biyan ma da abu mafi raɗaɗi, tabbas zata nuna musu wannan salman ta yanzu ba ta da bace, salmar kauye tuni ta dade da mutuwa, wannan kuwa sabuwa ce mara ɗaukar wulaƙanci daga wajen kowa, wannan me yakin kare mutunci da martabar ta da ta ƴaƴan ta ce, wannan salmar da ta kauye kamar gabas da yamma ne da ba zasu taɓa haduwa ba.
Duk da yaji sanda ta zare hannun ta cikin nashi be hana ta ko riƙe ta ba dan shi ma ze fi son ta fitan, baba kawai ta kalla cikin danne bacin ran ta tayi wa sallama ta fice, wannan ma ya Kuma konawa Hajiya Babba rai tare da kara hura wutar tsanar Salman a ranta, ita kuwa salma tana sane tayi hakan dan bata ga abin da zesa ta yi musu magana ba daga ita har baffa alhalin suna zaune ake zagi da cin mutuncin ta amma ba wanda yayi ko alamar tsawatar wa ga yaran dan haka gare ta sam basu da wani daraja bare girma, shi kan sa baban ta daure ne saboda darajar dan sa amma zuwa gaba in haka ta cigaba da faruwa bata san me zata aikata ba ko da kuwa a gaban nasa ne.
Seda ya tabbatar ta wuce kafin ya tashi daga kan rug din da yake ya koma kan one sitter ya zauna sosai, irin zaman nan na isa da iko dan kafar sa daya na kan É—aya ne yana girgiza ta a hankali
"a gani na da auren bazawarar titi so dubu adadin da za'a sake bani zaɓi gara auren bazawarar da tayi aure ta raya sunna har ta haihu kana qaddara ta raba ta mijin auren, baffa a wannan zamanin yan mata da yawa lillibin biri ne, akace kura da fatar ajiya, to haka suke, a zahiri gasu dai yan mata ne da ko auren fari basu yi ba, a badini kuwa ko matar auren da ta shekara biyar a gidan miji ba zata nuna musu komai ba akan sanin da namiji, ayi ciki a zubar, ayi ciki a zubar se ayi yafi nawa kafin auren, shiyasa da yawa Allah yake hana su haihuwa a gidan auren kuma kaga su zo suna ta neman ta ido rufe, to taya ma zasu samu bayan an gama tambadar da ƙwayayen tun a waje?!.
Nikam in har na auri budurwa na same ta a bazawara, ba ita dake matata ba hatta iyayen ta se nayi Shari'a dasu dan sun cuce ni sun ha'ince ni da suka bani second hand ko ma multiple hand ne a matsayin sabo".
Wani irin gau Hajiya Babba taji maganganun nasa kamar ya kwaɗa mata mafi zafin mari, tsananin raɗaɗin da take ji a ranta da zuciyar ta kuwa ya kasa ɓuya dan lokaci guda idanun ta suka canja launi zuwa ja sosai, jikin ta har wani dan barin ɓacin rai yake yi.
Ba ita kadai ba kowa na falon seda ya ɗauke numfashi na wasu sakanni domin dai maganganun sa a bayyane suke cewa da Nadiya yake saboda ita ce ta taɓa rashin ji lokacin da tana budurwa, abin babu dadin ji dan so biyu tana cire ciki ban da kuma magungunan planning din da ta sha wanda an sha kamata dasu ba so daya ba, kai da abin yayi tsanani ma har barin gida take ta kwana waje, da taimakon sa na jajircewa wajen sa mata ido da bibiyar ta da kuma na addu'ar da ake yi da rubutun da ake bata aka samu komai ya wuce kamar ba'a yi ba, sedai babban kuskuren da suka yi shine basu fadawa wanda ze aure ta komai kan abinda ta aikata ba aka lulluɓe aka kai ta, ba irin yadda be yi da baba a faɗa masa ba amma Hajiya ta fututtuke ta hana dole ya hakura ya zuba musu ido.
Ba kuwa ƙaramin tashin hankali aka kwasa da mijin ba dan yace an ha'ince shi, shi da sun faɗa masa gaskiya shi me iya haƙura ne ya karbi ƙaddara amma boyewar da suka yi shine ɓacin ran sa, abu dai yaki daɗi haka dai auren ya mutu ta dawo gida, se bayan shekara sannan ta sake wannan auren da take dashi.