Sashe 40
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A karo na farko da Abdallah yayi wa baba turjiya ya rufe idanun sa yayi musu rashin m dan ya fahimci wannan baban ba baban sa bane na da wannan baban wani ne daban da aka sauyo shi, wannan baban ba me son shi bane, wannan baban wani remote control ne na Hajiya dan se yadda tayi dashi kawai shi kuma be shirya sakin ragamar rayuwar sa ga matar da ta nuna masa tsantsan ƙiyayya da tsana ba tun yarinta har zuwa girman sa dan ko da mutuwar twins da maman su ba ta masa gaisuwa ba balle jajen halin da yake ciki hakan yasa ya yarda duk duniya ba shi da makiyi sama da ita domin ta sha faɗa masa ba so daya ba baso biyu ba ta tsane shi, bata son shi bata son bude idanu taga yana rayuwa.
Kamar maganar shuraiha kar ta mutu baba ya dinga kawo masa tallan mata wanda duk zaɓin Hajiya ne dan yace dole se yayi aure baze lalata masa suna a banza ba, sedai ko so daya Abdallah be taɓa bude idanu ya kalli matan ba hasalima da aka kai shi karshe gar da gar ya faɗawa baba be shirya aure ba, kuma ko ya shirya baze taɓa auren matar da ta fito daga tsagin makiyar sa ba.
Kiran Hajiya Babba da yayi da makiyar sa yasa Abdulkarim cike da rashin kunya ya taso wai zai yi faÉ—a da Abdallah sedai yayi babban kuskure musamman a lokacin da zuciyar Abdallahn ke kusa dan bas ya balla masa hannu bayan ya sharara masa marin da yasa yayi mutuwar wucin gadi.
Kukan da hajiya Babba ta fashe dashi yasa jikin baba ya shiga mazari tun bare da take ambatar ya karya wa Abdulkarim hannu, mari mafi kaskanci baba yayi wa kuncin Abu Aulad ma'ana on both cheeks, be iya cewa komai ba se kafe baba da yayi da idanun sa da suka yi mahaukacin jaa kamar wanda aka watsawa dakakken barkono a ciki, irin kallon da yake yi wa baba yasa jikin baban yin sanyi yayinda can cikin zuciyar sa ke masa zafi na ganin tashin hankali da damuwar gudan da mafi soyuwa a zuciyar sa hakan yasa ya É—ago hannun da ya mari Abdallahn Yana kallo fuskar sa cike da wani yanayi me kama da rashin jin dadi.
Juyawa Abu Aulad yayi ya fita zuciyar sa na bushewa da komai ma in da yasha alwashi kome baba ze yi baze taɓa yarda da matar da zata fito ta hannun babbar makiyyar da yake tunanin kaf duniya bashi da kamar ta ba.
Tun da lokacin suke cikin wannan takun sakar wanda ana cikin haka ne kika shigo rayuwar sa, am sorry to say amma na dade ina bibiyar rayuwar ki domin tun a satin ki na farko a ma'aikatar nan na shaida ke ɗin daban ce hakan yasa na shiga bibiyar ki da duk wani motsin ki domin kuwa zuciya ta na faɗa min zaki iya fitar da abokina daga halin sarkakiyar da rayuwar sa ke ciki, ina me baki haƙuri domin kuwa nine na dauki wannan hotunan lokacin da kika nemi faduwa ya tare ki, ban yi dan bata miki suna ba illa na son hada alkhairi sedai bani da wata mafita da ta wuce hakan domin ko nace Abdallah ya aure ki baze taɓa yarda ba dan yace sam babu mace a gaban shi, shi da mace har abada, shiyasa na ɓullo masa ta hanyar da na san dole ze haƙura domin shi ɗin me tausayi ne ba ze so sunan ki ya ɓaci saboda shi ba.
Jaridar duk da kuka gani shiri ce domin makudan kudade na biya aka buga min iya adadin da nake buƙata, ni na aikawa baba da ita haka ni na kawo ta office din Abdallah har guda Ashirin saboda in ɓatar Masa da hankali dan in ya ganta kaɗan yana iya darsa wani abu a ransa domin be da yarda ko kadan amma da ya ganta da yawa ko da zai yi karar gidan jaridar se da nasan yadda nayi na bashi haƙuri tare da bukatar ya bar komai a hannuna zan sa a hukun ta su sedai ba abinda nasa akayi masu dan BA SU DA LAIFI, Ni na zauna na nuna masa faidar auren ki domin ze zamo makamin da SIRRIN BOYE ze bayyana kasancewar akwai abubuwa da yawa da muke zargi a mutuwar nafisa, dole akwai abinda ya faru dan haka kawai ba abinda ze sa nafisa tafiya hanyar barin gari balle har tayi hatsarin da ya dau ranta dana ƴaƴan ta, a yadda akayi reporting motar tayi bindiga ne sedai ko da aka kawo motar gidan manta a rufe yake, ga kuma warin fetur da take yi shaidar akwai wani abu a ƙasa, abubuwa dai da yawa da se yana da aure ne komai ze bude.
Bayan auren ku da na tabbatar nayi nasarar kulla shi na kona jaridun dan amfanin su ya kare dan haka ki cire komai a ranki duniya babu kallon da take miki domin ba wanda yaga hotunan nan.
A takaice dai wannan shine tarihin rayuwar Abdallah, wannan itace rayuwar mijin ki salma!".
Shiru salma tayi kan ta na kasa, kallon agogo Haisam yayi tare da dan zare ido ganin yadda lokaci ya tafi sosai
"Shin kin shirya taimakon mijin ki salma?, Kin shirya daidaita rayuwar mijin ki?, Kin shirya dawo masa da farin cikin da ya rasa na tsawon shekaru biyar?, Kin shirya damarar yakar makiyan dake zagaye dashi?, Shin zaki taimaka masa ya gano BAƘIN ƘULLIn (my next book 💃) dake sarƙe da rayuwar sa? Kin shirya sama masa nutsuwa, kwanciyar hankali da amincin ruhi?, Kin shirya zaman aure da Abdallah salma?, Ki bani amsa salma?, Kin shirya yin yaki domin mijin ki ko a'a?".
Hannun ta dake rawa ta kai kan table ta yagi tissuen dake ajiye ta shiga share hawayen tausayin rayuwa Abdallah da suka kasa tsaya mata, wani irin kwarin gwiwa take ji, wani irin zumma take ji, tausayin sa na ratsa mata zuciya, burin ganin sa cikin farin ciki na dabaibaye nata ruhi haka kuma tsananin zafi da jin haushin Hajiya babba da duk wani makusancin ta na cika ranta, tabbas kome ne ne zata yi akan shi, rayuwar shi da ta ta na kamanceceniya sedai tasa ƙaddarar tafi tata tsauri, ita tasan dukkan iyayen ta mutuwa suka yi, duk da mutuwar da maman ta tayi ba me daɗi bace amma Gara ita akan shi da ya kalli gawar iyalin sa daidai har uku kwance a lokaci daya, bayan babban rashin bango kuma jigon sa da yayi wato Ummu ga kuma WATA ƘADDARAR (shamsiyya manga) ta bangaren baba, lallai yaga jarrabawa shima a rayuwar shi.
"Na shirya ya Haisam, na shirya yin komai da ka ambata dama wanda baka lissafa ba, tsananin tausayin sa da nake ji a raina yasa naji zan iya yin komai a kan sa, ban damu da za'a cutar dani ba, ban da mu da kome ze faru ba, abu ɗaya zuwa biyu na sani shine ina buƙatar farin ciki a rayuwar Daddyn twins haka bana buƙatar duk abinda ze taɓa min yarana, shin ya zan yi?".
Ta faÉ—a tana rushewa da kuka, ada yaran ne kawai rayuwar ta amma a yanzu tana jin ba zata iya rayuwa me kyau batare da Daddyn su a kusa da ita ba, bata ce ya kalle ta ba, bata ce ya so ta ba, bata ce ya kula ta ba ita dai in dai za ta dinga ganin sa to bata da wata damuwa ko kadan.
"Ya Isa salma, kiyi shiru ki daina kuka kinji ko, naji daÉ—i da naji wannan kalaman daga bakin ki haka hankali na ya kwanta na tabbatar na sakawa Abdallah Alkhairan da ya dinga yiwa rayuwa ta ta hanyar sama mishi uwar yaya ta gari.
Batun Æ´aÆ´an ki insha Allah babu abinda ze same su, kina musu addu'a kullum kina kuma kula dasu, na kuma tabbata a yadda na ga Abdallah na son su ze fi ki sa ido akan dukkan lamuran su dan haka hankalin ki ya kwanta insha Allah ba abinda ze Sami babies din mu".
"Allah yasa yaya Haisam, yanzu yaya zan yi kenan ina nufin wace rawa zan fara takawa dan ganin na hau matakin nemo wa Daddyn twins farin ciki?".
"Babban mataki a yanzu shine ki samu kusanci dashi, duk wata hanya da kika san zata kusan ta ki dashi ita zaki bi salma, duk da nasan hakan is not easy dan nasan waye Abu Aulad amma in kika dage kika kiji kika ki ganin duk abinda ze miki na rashin kirki tabbas zamu yi Nasara, dan ko a yanzu haka ina hango ta dan ban yi zaton ze ci abincin ki so soon haka ba".
Sanyi jikin salma yayi da ta tuna yadda yake tsare ta ta fara cin kome ta dafa kafin yaci
"Ai ba dan ni yaci ba, Ifty ce ta dage shiyasa ya hakura yaci kuma se da yasa naci dan ya tabbatar ban zuba komai ba tukunna".
"Ki manta da duk wannan ki maida shi ba komai ba domin nasan yana da dalilin hakan, baze yi dan tozarta ki ko wulakantawa ba sedan yana da ƙwaƙƙwaran hujja, na faɗa miki tun yana University ya daina cin komai na gidan su sedai ya dafa ko yaci kayan leda, duk da be faɗa min dalilin ba amma dole nasan yana da alaka da rashin yarda da cin abincin ki, amma ko ba komai mun yi nasara, abinda nake so dake yanzu shine ki kwantar da hankalin ki ki koya wa kanki rashin ganin laifin sa ko da kuwa laifin yayi dan hakan ne zesa zuciyar ki ba zata dinga zafi ko daukar fushi ba balle har ki ji kina son fasa aikin dan kuwa Abu Aulad na da kayan ban haushi kashi kashi da dole se kin kautar da kai.