← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 44

Sashe 33

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin yanayi salma ta tsinci kan ta a ciki, yanayin da bata taba jin ko makamancin sa ba a kaf rayuwar ta, a tsayin shekarun ta na 21 bata taɓa jin ko da kaso daya ne cikin goman abinda take ji yanzu ba, idanun ta da ta lumshe kuwa har lokacin suna rufe amma ji take yi har yanzu waɗan nan kaifa dan idanun nasa masu matuƙar kwarjini da sa jikin mutum ya mutu nan take suna kanta, a hankali ta buɗe idanun da suka yi wani maiƙo maiƙo kamar zasu zubda ƙwalla sedai ba kwallan zata yi ba, yanayin da take ciki ne suka haifar da hakan.

Ajiyar zuciya ta saki tare da komawa ta jingina bayan ta da jikin kujerar ganin yanzu kam idanun sa ba ya kan ta haka ma hankalin sa baya tare da ita yana wajen su ibtisam yana kunna musu jirgin sama suna ta dariya ganin yana tashi.

A yadda jikin ta yake mace ji take kamar zaman ma ba zata iya ba , gagarar ta yake son yi dan a yanzu ba abinda tafi bukata kamar ta ji ta kwance kan gado, ita kadai ɗin ta dan so take yi tayi birgima iya yadda zata iya ko taji sauƙin yanayin da take ciki.

Kiran sallar isha da aka yi yasa ya tattare kayan wasan gefe ya riƙe hannun yaran zuwa bedroom din sa, alwala yayi musu yace su tafi wajen momma suyi Sallah kana shima yayi alwala tare da canja suit din jikin sa zuwa jallabiya ya fita Masallaci da kudirin in ya dawo ya gyara dakin sa da ya zubar da kayan ciki kan bed garin dauko kayan da zesa ɗazu da safe.

Ana idarwa yayi azkhar É—in sallah be tsaya yin tasibihan da ya saba ba ya dawo alabasshi in ya gama gyaran dakin yayi su a nutse, tuni su salma suka hallara a dining se shi kaÉ—ai suke jira, har minti biyar shiru be fito ba hakan yasa ata aika Ibty kiran shi bata ade ba ta dawo tace ai Daddy aiki yake yi, mamaki ya kama salma ta tambaye ta aikin me se kuwa ta faÉ—a mata gyaran daki.

Duk da yara ne se taji amma gaba daya ta muzan ta, yanzu da da wani ɗan uwan sa ko wani na waje a nan gurin se fa a ga laifin ta ko, bayan tun ainahi be bata damar shigar masa daki ba, duba shi ma da ta shiga yi be ko gode mata ba se guzurin wulaƙancin da ya biyo baya.

Kai wai dai ita mace duk yadda tayi ba zata fita ba se an ga laifin ta, ta tabbatar da akwai dan uwan sa a nan abinda zasu fara cewa shine ta mallake shi hatta gyaran dakin ma shi yake yi.

Haka dole suka jira ya gama kafin ya fito aka ci abincin, duk da be buÉ—e baki yace mata abincin yayi daÉ—i ba yanayin sa ya nuna, be gode mata ba amma yadda ya cinye tuwon har da kari ma ya shaida mata godiyar sa.

Ko da suka gama ci tuni yaran suka koma falo suka cigaba da wasan su ita kuma ta tasa su kamar Tv tana kallo cikin jin dadi, shi kam har lokacin yana kan kujerar dining idanun sa a rufe.

Yanayin ƙwayar idanun ta ba abu bane da aka fiya gani kasafai cikin jama'a, wasu kan ringa gudu ko tsoron mutanen da ƙwayar idon su bata kasance baka ko brown ba sedai shi tun a karon farko da yaga idanun ta yaji sun burge shi, kalan su da yadda suke yin maiƙo maiƙo lokaci zuwa lokaci shi yafi daukar hankalin sa sedai be nuna ba ma dan kar ta raina shi.

Yanzu haka da ya rufe ido tunani yake yi na daban amma kuma yanayin idanun nata lokacin da suka yi kallon kallo É—azu shike masa shawagi cikin na sa idanun, tunanin sa ba na komai bane illa zuciyar sa da yaji ta fara kwantawa cikin son yarda da yarinyar, ba wai yarda akan komai ba, a'a yarda akan cikin sa wato abincin sa.

Tun ranar da aka ɗaura musu aure ya sassaka CCTV cameras a sashen sa, irin yan ƙananun nan da bakowa ze san akwai su ba, yasha bibiyar ayyukan ta a kitchen musamman lokacin da ta fara aiki masa da tayin cin abinci, a lokacin sam be yarda da ita ba gani yake wani abu ne a ranta shiyasa tayi hakan, wannan dalilin yasa kusan kullum se ya bibiyi moves din ta a sashen tun bare ma ayyukan ta na cikin kitchen sedai har zuwa yau da zata cika she sati ɗaya a tare dashi gobe be kamata da rashin gaskiya ba ko ƙanƙani, a kan komai ma be ga alamun cutarwa ba tattare da ita sedai ba wai ya gama yarda bane ze cigaba da bibiyar ta har nan da zuwa ko watanni nawa ne baze gaza ba har se yaji hankalin sa ya ida kwanciya da ita.

Tun bayan mutuwar Ummu be kuma cin abincin da dandanon sa ya ratsa zuciyar sa ba se shigowar ta rayuwar sa, haka be san ya akayi tasan yana son abincin gargajiya ba sedai shikam hakan yayi masa dadi dan yanzu bashi da fargabar samun wani ciwo dalilin yunwa sedai kuma wani bangaren.

Ajiyar numfashi yayi tare da buɗe idanun sa ya sauke kan yaran dake guje guje suna bin kayan wasan su, fari kal yake jin ransa in Yana duban su, se yake ganin kamar wadancan ne suka dawo, haka cikin ransa matsayin wadancan ya basu shiyasa basu da shamaki cikin ran sa da kuma dukiyar sa haka kuma yayi alƙawarin kulawa dasu tare da basu dukkan soyayya har zuwa ƙarshen nunfashin sa.

"Time for sleep babies".

Ya fada yana miƙa musu hannu, ajiye dolls din su suka yi suka ƙarasa tare da bashi nasu hannun, be yi sanya ba ya ɗauke su zuwa dakin sa a karo na biyu Hajiya salma na zaune.

Sabanin jiya yau kam se ba taji ko ɗigon na bakin ciki ba se ma farin ciki da jin dadi hadi da tsananin girman sa da taji sun mamaye mata ruhi....................✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 024 [ 12/11/2022 12:58 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

                    Paid page 024

_________________________📖 Yau kam bata fita raka su ba shi ya kai su har class sannan ya je wajen principal Wanda bata san me yace masa ba, taga dai sun fito tare suna magana sannan sukai sallama ya dawo mota.

Yau tun kan su kai office ta zare abayar jikin ta tare da gyara zaman ƙaramin hijab din ta ta saka rigar cikin jaka.
Kusan tare suka fito daga motar lokacin da yayi parking, kwana biyu da bata zo ba se take jin matukar kewar companyn kamar an canja shi dan tun da ta fara aiki in ba hutu akayi ba bata taɓa fashin zuwa aiki ba.

Rufe kofar sa yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da zama kan nata kujerar da ta gama goge wa duk da tasan kullum se an share an goge komai dake cikin office din.

Aiki ta fara dan ma taga ba'a ajiye mata ayyuka sosai ba dan bata tarar da files É—in da ta tafi ta bari ba wanda kashegari ya kamata ta tashi aiki a kan su se kuma bata samu zuwa ba.

A hankali ta É—ago kan ta dake kan screen din laptop ta kalli Haisam tare da amsa kiran da yayi mata

"Na'am, Good morning sir".

"Morning Salma, ya jikin angel".

"Ta warware dan suna ma school".

"Allah ya ƙara lafiya ya tsare gaba, dama ina ta neman ki dan ina so muyi discussing a very important issue".

"Ayya in zo office ne?".

"Eh when you less busy ki shigo Ina jiran ki".

"Insha Allah sir".

Daga haka ya ƙarasa officer ɗin Abu Aulad ita kuma ta cigaba da aikin ta without giving much attention kan issue din da yace zasu yi magana akai dan a nata tunanin it's a business issue.

Bata sami saukin ayyuka ba se after zuhr dan haka daga masallaci da tayi sallah se kawai ta wuce office din Haisam.

Zaune yana ta fama da takardu ta tadda shi amma tana shigowa ya ajiye tare da ture su gefe ya nuna mata kujera alamar ta zauna, zaman tayi tana sake gaida shi ya amsa mata cikin sakin fuska kamar yadda ya saba.

Dan shiru yayi cikin tunanin ta inda ya kamata ya fara kafin ya nunfasa ya É—ago ya kalle ta

"Ashe mijin ki ya sake aure kuma?".

Bata san me yasa ba amma se da taji wata yar faduwar gaba duk da kuwa ta sani

"Eh wallahi, Allah ya nufa".

Shiru ya dan sake yi se kuma ya zuba gaba É—aya hannayen sa kan table É—in sa

"Naji an aura masa shuraiha yar aminiyar Hajiya Babba".

Oh ashe yar aminiyar ta ne, to ita ina ta sani ba dan ya faÉ—a ba, shiru tayi masa dan bata san ne zata ce ba, tun da ya sani meye na tambayar ta kuma.

"Tun kafin maganar auren ta fito na so na samu lokaci muyi magana se kuma Allah be nufa ba, yanzu kuma da akayi auren se maganar ta mafi muhimmanci akan da, magana ce nake so muyi akan mijin ki, ina nufin Abdallah".

Jin sunan Abdallah yasa ta sake bashi attention din ta sosai
Chapter 33 · 0% Book details