← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 44

Sashe 20

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Seda aka yi masa ƙarin ruwa leda biyu tare da allurar bacci dan rashin hutu da damuwa ne suka haddasa masa ciwon kan, likitan yace a dena barin shi da yunwa haka kuma ya rage sa damuwa a ran shi da kuma yawan tunani".

Sosai take sauraran maganganun nasa sedai cikin ranta mamakin dalilin faÉ—a mata da yake yi tayi dan bata san ma'anar hakan ba.

"Na faÉ—a miki ne dan ke ya kamata ki sani ki kuma kiyaye dukkan abinda likita yace dan a yanzu ke keda hakkin hakan".

"Amma sir ko da nayi abinci jiya na ajiye masa be ko taɓa ba balle yaci, yau ɗin ma da kyar in ya ci breakfast din da na aje masa, to me zan yi masa nikam?".

"Nasan baze ci ba salma, a sanin da nayi wa Abdallah indai ta tashi ne to baze taɓa cin abincin da zaki dafa ba".

ÆŠagowa tayi ta kalle shi sosai wannan karon

"Amma saboda me sir?".

"Call me Haisam". Sunkuyar da kai tayi alamun bazata iya ba hakan yasa ya É—an yi dariya

"Okay you can call Yaya Haisam dan tuni kika zama ƙanwata".

Gyada kai tayi kafin ta ɗan gyara zama cikin son jin dalilin daze sa Abu Aulad baze ci abincin ta ba........................ ✍🏻.

Ouummey 📚✍🏻.
[12/13, 10:37 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 014 [ 12/6/2022 3:06 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

                       Paid page 014

_________________________📖 "Jiya jiya kika shigo rayuwar sa shiyasa baze ci abinda duk zaki dafa ba dan be gama sanin ki ba har yanzu".

Haisam ya fadi hakan ba wai dan haka yayi niyyar faÉ—a ba se dan tunanin da yayi yasa kawai ya fadi hakan.

Numfashi ta dan ja kafin ta daga kai alamun ta fahimta

"Ke da kanki ya kamata ki sa yaci abincin dan in ba kiyi hakan ba ze ta zama da yunwa ne yana shan juice da cin biscuit dan be iya yawon restaurant ba haka ba komai ma yake ci ba".

"Amma taya zan sa yaci É—in bayan a iya jiya zuwa yau na fahimci shi din wani irin mutum ne da ba'a gane ina ya dosa".

"In kika dafa ba ajiye masa ya kamata kiyi ba, se ki kaima ki kuma sashi a gaba har se yaci kin gani".

Zaro ido tayi jin abinda yake faÉ—a, kamar irin be san halin mutumin da yake tura ta gare shi ba, bayan ko shi da yake É—an uwan sa ba wani sake mata yake ba balle kuma ita.

"Na sani zaki ji wani iri amma dole hakan za'a yi, kinga a mutanen gidan su sam ne yarda da kowa ba balle yaci abinda zasu dafa, haka baze yarda in dinga taho masa da abinci ba balle kuma yaje gidan mu yaci, kinga dai a karshe dole kece last hope din, daurewa zakiyi ki kauda duk wani daridari, nauyi da kuma tsoron sa da kike ji kin ji".

"Bari inje masallaci gashi can ana kiran sallar biyu".

Ya faɗa yana miƙewa da sauri kasancewar yau ɗin juma'a, itama tashi tayi ta fita tana nanata maganar da ya faɗa a ranta.

Aunowa kawai take yi gata ta sashi a gaba da abinci amma kallon banzan da jefa mata yasa jikin ta daukar rawa kamar an watsa mata ruwan sanyi a cikin tsakiyar hunturu.

"Kai haba dai, Bama zan iya ba nikam". Ta faÉ—a a fili tana kaiwa zaune kan kujerar office din ta.

Ban da ma dai ya Haisam da neman magana ya zaice ta wani sa shi a gaba yaci abinci se kace wani karamin yaro, to kar ya ci É—in mana, ba cikin sa bane da har wani shi kuma ze ce wai be yarda da yan gidan su ba, ji wani fa rainin wayo, to in be yarda dasu ba da waye ze yarda.

Ba ma wannan ba be yarda da yan uwan sa ba se ita ce ze yarda da har za'a ce ta bashi abinci salon a ja mata yace wani abu ta saka masa a abincin da take so dole se yaci.

Cikin wannan tunanin ta tashi tayi sallah jin an idar a masallatai.

Ajiye wannan batun tayi a gefe ta shiga ayyukan gaban ta musamman yau da ayyukan suka yi mata yawa dan akwai presentation da za tayi wanda a ƙa'ida shi ya kamata yayi akan tunda baya nan Haisam yace ta gabatar.

Ƙarfe huɗu ta tashi aiki ta haɗa kayayyakin ta ta fita, a compound ta tarda drivern ɗazu yana jiran ta, gaisawa suka yi ta shiga yaja mota suka fita, seda suka fara zuwa makarantar su Ibty suka ɗauke su sannan suka wuce gida.

Tun daga gate din gidan tasan akwai abinda ke faruwa aciki ganin yadda jama'a ke kaiwa da kawo maza da mata kamar dai wanda ake wani sha'ani.

Drivern nayi parking ta fita ta shiga tafiya cikin nutsuwa, shan gaban ta da akayi ne yasa ta ɗago kanta ta sauke kan yan matan gaban ta dan da kanta a ƙasa yake.

Kafe ta da idanun ta da suka yi jajir Nuriyya tayi, wani irin tafarfasa zuciyar ta take yi na tsananin ɓacin rai ga tsananin zafin da take ji saboda matsanancin kishin Salman da ya rufe ta, bata taɓa zaton haka zata ga salma ba, a tunanin ta tunda ance bazawara ce to zata ganta wata ƙatuwar haka mara fasali se gashi ta ganta yarinya danya sharaf kamar ma ta fita ƙuruciya.

Ganin yadda yarinyar ta tsaya a gaban ta tana Binta da wani irin kallo da ta kasa gane ma'anar sa sedai tafi danganta shi da kallon banza yasa ta rabe ta ta yi gaba riƙe da hannun ya'yan ta, cikin sauri itama Nuriyya ta kuma shan gaban ta tana Binta da mugun kallo

"Aikin banza aikin wofi, banda tsabar budurwar zuciya ina hadin ki da yaya Abdu, bazawara har da ya'ya biyu amma ki likewa mijin da zan aura har kika yi kutunkutun kika aure shi har itama waccan banzar taga wuri ko, to wallahi daga ke har ita ku shirya ba zan taba bar muku ya Abdu ba kuma daga lokacin da na shigo gaba É—ayan ku se kun fice kun bar min shi dan ba abinda ze yi da ku, bazawarar aure da bazawarar titi, mtswww".

Sototo ta tsaya tana kallon Nuriyya da kawar ta da suka yi gaba suka bar ta nan tsaye, to ita kuma wannan wacece, ta tambayi kanta dan bata ganta ba jiya da safe da ta tare a gidan ba, lallai Allah me iko, yanzu kam ta fahimci shegun gidan nan da yawa ba wai kaÉ—an bane ya kuma kamata ta san kanta in ba haka ba cin kashin da zata gani ba kaÉ—an bane.

Haka dai taja yaran ta suka ƙarasa part din, da key ɗin hannun ta tayi amfani ta bude kofar suka shiga ta maida ta rufe, kallo ta shiga bin parlon dashi wai ko zata gan shi zaune ko kwance sedai ko alamun sa babu.

Daki ta wuce dasu sukai wanka suka canja kaya sannan ta fita ta hau aikin gyara, duk da parlon ba wani datti yayi ba amma haka ta gyara shi ta sake shara ta sa turare kana ta nufi kitchen.

Seda tayi wanke wanken kayan da suka bata da safe sannan ta hau aikin girki, sanin akwai mara lafiya yasa tayi farfesun hanta da yasha kayan ƙamshi da ganyayyaki ta zuba a wani madaidaicin warmer ta rufe ta shiga ƙarasa girkin da take yi.

Tana gamawa ta haÉ—a gaba É—aya ta kai dining ta koma ta haÉ—a lemon kankana da yasha madara sosai ta sashi a fridge ya dan yi sanyi ba sosai ba sannan ta haÉ—a da cups din acrylic jug din ta Kai table.

Wanka ta koma É—aki ta sake yi daidai ana kiran sallah dan haka ta gabatar da sallar sannan suka fito falon tare da yara, Ifty da ta fi hayaniya ta kalla

"Maza je ki Kira Daddy acikin daki muci abinci".

Da gudu kuwa Iftyn ta nufi hanyar dakin, kwance kan king size bed din sa ta same shi idanun sa a rufe kamar me bacci sedai ba baccin yake yi ba, yayi yayi baccin yazo amma hayaniyar dake tashi a compound din gidan ya hana dole ya hakura ya cigaba da kwanciya.

Duk da yaji alamun shigowa amma be buɗe idon sa ba dan a tunanin sa Haisam ne ya dawo sedai jin Muryar Ifty yasa ya shiga buɗe su a hankali kamar me fargabar yin tozali da abin tsoro har ya buɗe gaba ɗaya ya sauke akan ta, murmushi y ƙaƙalo ganin yadda ta wage haƙora tana yi masa dariyar ta me kyau.

"Daddy ka tashi muci abinci".

Ta faɗa tana jan hannun sa, a hankali ya yunƙura ya tashi zaune tare da jawo ta ya zaunar da ita a gefen sa

"Babyn daddy an dawo school?".

"Yes daddy, kazo muci abinci, momma ta dafa me daÉ—i".

"Awnn babyn Daddy zata ci delicious, maza je ki kici daddy baya jin yunwa".

"No daddy kazo muci kaji".

"Naci abinci tun É—azu angel, maza je kici naki kema".

Duk yadda yaso yayi wa Ifty wayo sam yarinyar taƙi yarda dan dama da biyu salma ta tura ta saboda akan abinda take so akwai ta dagiya.

Ganin tana kara masa ciwon kai dan dama ba wai ya tafi gaba ɗaya bane yasa ya miƙe suka fito dan t-shirt ne a jikin sa da Three quarter, ko da ya biyo ta bawai ze ci bane, yadai fito ne dan ta ƙyaleshi kawai.

DaÉ—i salma taki ganin su sun fito, wato Ifty fa karshe ce, duk da fuskar sa babu ko É—igon annuri amma hakan be dame ta ba, badai ya fito ba?, Dama abinda take so kenan.

Kujera ya ja ya É—ora Ifty akai shima yana daya ya zauna, a É—arare salma ta gaida shi dan presence din shi a wajen yasa duk taji ta takura ba kaÉ—an ba.
Chapter 20 · 0% Book details