← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 44

Sashe 6

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iya ƙauna da mutuntaka baba Husaila da ƴan uwan ta sun gwada mata, Abinci da abin sha bata taɓa rashin su ba, ga kula da ita da ƴaƴan ta da suke yi tun bare baba dan ko rigimar Ussaina ce ta tashi da dare bata bari ta tashi cewa take ta koma tayi kwanciyar ta ita kuma tayi ta fama har se tayi bacci tukunna hankalin ta ze kwanta.

Ruwan wankan su kuwa kullum se ta sa musu magani shiyasa alhamdulillah jikin su yayi ƙwari se fatar su da ta ɗan dafe saboda zafin ruwa da kuma kalar magani duk da yanzu sun fara sabawa da zafin ruwan.

Sannu a hankali har ta cinye wata ɗaya tare dasu basu ankara ba saboda zama da yayi daɗi, jakar ta kuwa baba ta adana mata dan ce mata tayi da su ne za'a bar ta ta shiga makarantar in taje, yadda ƴan uwan baba ke son ta ita abin har mamaki yake bata, wai yau ita Salame da kowa ke gudu itace yau ake so ko da yake ai ba ita ake so ba ƙaunar ƴaƴan ta ce ta shafe ta dan haka be kamata tayi wani kauɗi ba.

Mace ɗaya ce ta taɓa son ta a Karan kanta yadda take wato Hajiya Hadiza principal ɗin su, Allah ya sani tana son matar a ranta irin son da bata san yadda zata kwatanta shi ba.

Ta so ta a lokacin da kowa ya ƙi ta, ta bata gatan da bata taɓa zaton samu ba, a bayyane yake badan ita ba da ba zata taɓa samun damar karatun da take so ba, ita ta ɗau ɗawainiyar komai na makarantar ta, kuɗin PTA, uniform, littattafai, takalmi, Safa, abinci da komai da zata buƙata a makaranta tun da ta fara kuwa bata gaza ba har wata ɗaya da kwanaki baya da ta gama, ita kuwa ai sedai tace da ita Allah ya saka da kuma ya zame mata wajibi ta so ta.

Kallon baba Husaila dake zaune gaban ta tana mata lissafi kawai take yi yayin da idanun ta suka tara ƙwalla, kuɗi ne daga kan ƙwandala zuwa na takarda wai wanda aka haɗa mata dan tafiya makarantar su da zata yi duba mijin ta in yazo (kamar yadda tace musu).

Hannu ta sa ta share hawayen

"Dan Allah baba ki maida musu kuɗin nan kin ji, zan fa iya zuwa da ƙafa".ta faɗa murya na rawa

"Amma dai salamatu baki da kirki, ya za'a yi mutum yayi alkhairi a maida masa, to kul kar in Kuma ji ko ke kin yi hakan kin ji ko?".

Da kai ta amsa wa baba kafin ta shiga yi musu godiya da addu'a kamar Allah ne ya aiko ta har se da baban ta gaji ta fice ta bar mata É—akin.

Tuhumar kanta take kan me yasa tayi masu ƙarya gashi su kuma sun yarda da ita sun zauna da ita da zuciya ɗaya, jaddada wa kanta take Allah ma ya sani ba'a san ran ta tayi ƙaryar ba, bata so a raba ta da yaranta ne kawai.

Da wannan ta tattara kuɗin da suka tasamma dubu ɗaya ta zuba cikin jakar makarantar ta, ta kuma haɗe kayan ƴan biyu ta ninke ta zuba cikin jakar su ta rakuɓa nata kala huɗu da take dashi.

Kashegari tayi sallama dasu cikin rashin daɗin rai dan har da kukan ta haka ma baba Husaila da ta zauna wajen ta, ji take kamar yarinyar ta dawwama tare da ita dan bata da matsala sam, yarinya ce me kirki ga ladabi da biyayya, gata ba har dama, ga nutsuwa da rashin ƙyuya, duk sanda taga ta tashi aiki bata bari tayi komai se karɓe ta shiga yi shiyasa so da yawa ma bata tashi yi saboda tasan ba zata bari tayi ba.

Su kuwa ragowar ƴan gari da matasan su ƴaƴan ne suke jin kamar su ƙwace ta tafi ita kaɗai dan sun shiga zuciyoyin su barin ma Hassana da bata da rigima, in aka fita da ita har se an tausaya an dawo da ita dan bata kuka se dai in ko Bata da lafiya ko kuwa ta kai maƙura wajen jin yunwa, toh haka dai aka rabu kowa na mararin kowa, rayuwar kenan!

Ganin tana da isassun kuÉ—i a hannu se kawai ta tare mota bayan ta fita sarari, sunan Makarantar su ta faÉ—a masa suka yi ciniki ta hau ya kai ta har bakin gare kuwa.

Wajen baba megadi ta bada ajiyar jakar kayan su ta wuce office ɗin Hajiya Hadiza wato principal, ba abinda ya dawo da ita makarantar illa son karɓar sakamakon ta tare da certificate ɗin kammala karatun ta dan tana so a duk inda taje ta ɗora karatun ta dan shine burin ta tun bata san ze iya cika ba ko kuwa ze rushe ne har zuwa lokacin da ta fara hasashen cikar sa wato da maigari ya sanya baki a kan karatun.

Ba kaɗan ba Hajiya Hadiza taji daɗin ganin Salame wadda ke amsa sunan Salama kamisu a makarantar, cikin nutsuwa ta bata takardun ta da WAEC result ɗin ta dan dama alƙawari ne tayi mata ana sakin result zata bada a ciro mata nata.

Cikin ikon Allah tana da credit bakwai da excellent biyu, Salame kam har dasu kukan godiya ga Allah dan ta san shi yayi mata komai ba wai ita ba haka kuma ta sanadin wannan matar me kyakkyawar zuciya ne wato Hajiya Hadiza, godiya kam haka ta dinga zuba ta tana yi tana hawaye lokacin da take faɗa mata ga Form nan na College of Education ƴan gora, wata local government a babban garin da ƙauyen su yake ta cike ta mata submission in tana so ita Kuma zata biya mata komai, da ƙyar ta iya tsayar da kukan ta sukai sallama ta tafi.

Se da ta tsaya ta karɓi kayan ta wajen Maigadi ta ma sallama tukunna ta wuce, mota ta tara zuwa tasha inda batare da tunanin komai ba ta biya motar garin GAMJI dan a can ne makarantar da take son yi take.

Motar na cika aka fara tafiya inda ita kuma ta fara nata tunanin kan irin rayuwar da zata yi a can ita da yaran ta dama yadda rayuwar karatun ta zata kasance, shafa Form É—in da Maah Hadiza ta bata ta sake yi tare da lumshe ido tana ayyana batutuwa da yawa a ranta.

Zata cike Form ɗin tayi submitting a can makarantar a karan kanta batare da jiran Maah Hadiza ba dan bata jin nan kusa zata kuma komawa koda hanyar ƙauyen BA MUNI ne, da kanta zata tsaya wa kanta tayi komai sedai ta yaya tunda ba kuɗin hakan ne da ita ba, gashi yanzun nan in bata manta lissafin da Maah take mata na kuɗin da za'a kashe kusan dubu sha biyar ne, registration goma da ɗari biyar ragowar kunji kunji kuma su cinye sauran.

A ina zata samo wannan kuÉ—in ita da ba ta da kowa bata da kuma komai?

Wannan shine tunanin Salame yayinda mota ke ta tsuga gudu a titi, ragowar passengers kowa da abinda yake yi, wasu hira, wasu kallo, wasu karatu wasu kuwa bacci.

Itama dai cikin tunanin ta da yake kakare mata sanadin rashin abokan rayuwa wato kuÉ—i nata baccin ya saÉ—aÉ—a saÉ—af saÉ—af yayi wuf! Yayi gaba da ita.

Hayaniyar da ta cika wa kowa kunne ce ta sanar da masu barci an iso in da zasu wanda Salame na cikin su, miƙa tayi a hankali ta kalli Hassana dake ɗaure a gabanta tana baccin ta hankali kwance, tun da aka fara tafiyar bata yi wani rigima ba se Ussaina da ta ɗan yi kuka ta kunto ta ta bata tasha ta kuma maida ta bayan ta ɗan bata ruwan leda da ta saya guda biyu tun a can tasha kafin su tashi.

A hankali ta sauka daga motar hannun ta riƙe da jakar kayan su ɗayan kuma jakar makarantar ta da ta saka Form da ragowar takardun ta a ciki.

Tun da ta sakko taji ana shelar kowa ya kula da jakar kuɗi ko kayan sa saboda ɓarayi ta kuma damƙe jakar makarantar a ƙirjin ta ɗayar kuwa ta mata riƙon da tasan ba me iya fincike ta a hannun ta ta sauƙi.

Tunanin inda zata nufa ta shiga yi se kuma ta tuno yadda suka yi da Maah Hadiza da ta tambaye ta ko ina zata zauna in ta zo karatun tace mata ai duk me napep É—in da tace ya kai ta gidan haya ze kaita dan ba ya wahala a garin GAMJI.

Bakin tashar ta fita taƙi kula duk me napep ɗin dake cikin tashar dan bata yarda dasu ba, suma zasu iya zama ɓarayi ne, a nan titi ta sami wani tace ya kai ta gidan haya.

Seda suka fara tafiya ya tambaye ta gidan mutane da yawa ko kaÉ—an

"Kamar dai biyar ko bakwai".

Amsar da ta bashi kenan shima be kuma magana ba ya shiga tuƙa abar sa cike da ƙwarewa, wata unguwa ya shiga mara wadatacciyar tsafta ga nan gidaje a wajen ba fasali se uban yara da suka cika layin jikin su ba kyan gani.

Gaban wani gidan bulo yayi fakin tare da nuna mata gidan

"Ko a layin in kika lura gidan na cikin gidaje masu kyau haka ma É—akunan su suka da yawa megidan ma a nan take rayuwa a É—aki É—aya, yanzu dai bani kuÉ—i na in tafi".

"Tsaya dan Allah, nawa ake biya na hayar?".

"Wata shida dubu uku shekara kuma dubu shida".

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauka tare da fidda kayan ta ta bashi Naira hamsin É—in shi ya tafi.

Cikin É—ari É—ari gaban ta na faÉ—uwa ta shigar da kayan zauren gidan ta shiga doka sallama kamar sabuwar warkewar makanta

"Kai haba wannan wane irin bala'i ne tun ɗazu ake ta waalaikumussalam amma dan baƙin rashin mutunci an ƙi shigowa, to dan Allah mutum ya ɗige a wajen ƙarƙari in na gaji in ɗau taɓarya in jirge mutum dan na gaji da iskancin ƴan unguwar nan, me ake da gidan haya ni saratu ban da dai ƙaddara".
Chapter 6 · 0% Book details