Sashe 19
Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hotel ta fara ganin baba acan kasar Dubai yaje harkokin sa na kasuwanci ita kuma ta raka wani Alhajin ta, tunda ta sauke ido akan baba shikenan ta Nace masa tun bare da taji wanene shi da irin dukiyar da ya mallaka.
Ba irin bibiyar da bata yiwa baba ba kan ya amince mata suyi rayuwa irin wadda take yi sedai firr yaki, kasancewar yana son ta yasa ya bullo da maganar suyi aure, ganin fa zata iya rasa shi in ta cigaba da dagewa yasa kawai ga hakura akayi auren.
Gawurtacciyar mara kunya ce number ɗaya dan ko a cikin karuwan ma ita ɗin ta daban ce, ba ƙaramin wahalar ta Hajiya Babba ta sha ba kafin kuma tayi yunkuri, yunƙurin da har yau ban da ita ba wanda yasa yadda akayi sedai kawai gani akayi baba ya koma kamar wani kani ko yaron ta dan se abinda tace yake aikatawa.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sa hannu ya shafe hawayen da suke kuncin sa ya mike ya nufi hanyar fita daga É—akin saboda jin kiran Sallah da yayi, wai har asuba tayi ba tare da ya lura ba , ko da yake a yadda yayi nisa cikin tunani dole baze gane sauri ko nawar agogo ba.
Kamar ya wuce se kuma ya ga rashin dacewar hakan dan haka ya ƙarasa bakin kofar dakin su ya shiga knocking.
Bata da nauyin bacci shiyasa a bugu na biyu ta tashi, hannu ta miƙa ta kunna fitilar dakin tare da dan yi gyaran murya ta tambayi waye, shiru bata ji ance komai ba dan haka ta bude kofar dakin a hankali ta leka, wayam taga ni ba kowa dan haka da sauri kuma a tsorace ta maida ƙofar ta rufe.
Cike da mamakin wa ya buga mata ƙofa ta daga kai ta kalli agogon ɗakin, ganin time ɗin subhi yayi yasa take ranta ya bata shine ya buga wato ya tashe ta sallah kenan.
Toilet ta shiga tayi alwala ta fito ta yi raka'a tanul fajr sannan tayi asubar, a takaice tayi azkhar da addu'o'in da ta saba sannan ta miƙe ta fita zuwa kitchen.
Breakfast ta fara haÉ—a musu tana yi tana duba wall clock din dake kitchen din, karfe shida da rabi ta kammala komai ta dauka ta kai kan table sedai ganin abincin da ta aje masa akan table ba'a taba komai ba se jikin ta yayi sanyi.
Ajiye na hannun ta tayi ta É—au warmer din ta Kai kitchen, tunani ta shiga yi na yadda zata yi da abincin dan da ta san be ci ba da shi zata musu warning suci da safen sedai ta riga ta gama komai.
Wani dan bowl ta É—auka me É—an girma ta juye abinci a ciki tayi warning É—in shi sannan ta ajiye da niyyar in zasu fita ta dauka ta ba gare man ya bawa almajiri in ya gani dan ba ta san zubar da abinci alhalin ba lalacewa yayi ba, hakan ya zama almubazaranci.
Yanzu ma a daki suka karya ita da yan biyu yayinda ta ajiye masa nasa a dining, suna gamawa ta musu wanka tare da shirya su cikin uniform din su dake matuƙar daukar kyakkyawar fatar su wadda ta kasance fara ce sosai dan sun fi salma haske duk da itama ba baka bace.
Da suari ta yi wanka ta shiga shiryawa itama ganin lokaci har ya tafi dan It's seven ten am, yau brown abaya ta É—ora kan kayan ta sannan ta sa farin hijab din ta da da kadan ya sauka daga kafaÉ—ar ta.
A falo ta tadda shi kwance kan doguwar kujera sanye da milk ɗin jallabiya da tayi masa matukar kyau, cikin ɗan mamaki ta kalle shi sannan ta kau da kai, to ko dai yau baze je officer bane, amma kuma yadda yasan shi workaholic indai ba dole ba baya taɓa fashin office.
Da gudu Ifty ta fincike hannun ta daga na salma tayi wajen sa tare da faÉ—awa kan sa, a hankali ya buÉ—e idon sa ya sauke akan ta lokacin da take kai masa kiss goshin sa tare da gaishe shi
"Good morning Daddy".
"Morning pretty".
Ya faɗa yana miƙewa zaune ɗauke da ita a jikin shi, itama Ibty janye hannun ta tayi ta tafi wajen sa tare da zama kan side din cinyar ta Ifty na zaune a dayan.
"Good morning Dad".
"Morning beauty".
"School zamu je Daddy, momma tace yau zata kunna mana tiger in muka yi karatu da yawa ko Ibty?".
Ifty ta faÉ—a tana kallon Ibty, gyada mata kai tayi kasancewar ita ba me yawan magana bace
"Kun kusa makara fa babies, maza ake school ayi karatu kunji, ai kuna san kallon tiger din ko?".
Da sauri suka gyada masa kan su Ifty na sakin murmushi
"Yauwa to maza aje, Allah ya kiyaye hanya".
Peck suka yi masa daya bayan daya a goshi kafin suka sauka a jikin sa suka koma wajen salma da take kallon su kamar ta sace saboda yadda suka burge ta, ba wanda ze kalle su a haka yace ba yayan sa bane, ba wai dan kama ba, a'a yanayin mu'amalar su.
Sosai taji daÉ—in hakan da yayi ganin yadda suke walwala da fari ciki suka bayyana kan fuskar su.
Sunkuyar da kanta tayi kafin ta shiga takowa zuwa hanyar fita, seda ta kai tsakiyar ɗakin daidai saitin kujerar da yake zaune jingine da bayan kujera idon sa a lumshe sannan ta durƙusa
"Ina kwana".
"Lafiya". Ya faɗa bayan yaja lokaci kamar baze amsa ba, miƙewa tayi tana satar kallon sa ganin yadda kibiyoyi kansa suka tattashi, a hankali ta juya ta fita dan twins tuni suka fice.
Da sauri ta ƙarasa fita dan tunanin kar wani yayi wa ƴaƴan sa wani abu, ajiyar zuciya ta sauke da ta gan su bakin part din, karasa fita suka yi ta bawa gateman bowl din hannun ta.
Suna tsaye aka buÉ—e gate wata mota ja me kyau ta fito, kau da kanta tayi dan bata san ko haÉ—a ido da yan gidan balle akai ga magana, gaban ta motar ta tsaya hakan yasa ta ja hannun babies din ta zasu wuce.
"Megida ne yace akai ku inda zakuje Hajiya".
Dakatawa tayi ta juyo ta kalle shi, maigida, wani maigidan kenan?!.
"Yallabai Abu Aulad nake nufi".
Jin haka yasa ta buÉ—e gidan gaba ta sa twins ita Kuma ta shiga baya.
Cikin ranta kuwa sosai taji daÉ—i dan a yadda suka tsaya gaisawa dashi in napep zasu jira dole se sun makara, amma yanzu kalli yadda nan da nan har sun kusa isa makarantar.
A parking lot yayi parking ta fita tare da kama hannun su ta rakasu har class sannan ta koma suka fita zuwa Company.
A bakin gate tace ya sauke ta base ya shiga ba, ganin zata wuce yasa yayi saurin tsayar da ita
"Ƙarfe nawa zan dawo Hajiya?".
ÆŠan jim tayi cikin jin abin wani bako, ita ake tambaya karfe nawa za'a dawo daukar ta lallai rayuwa.
"Ƙarfe huɗu".
Amsa mata yayi yaja motar ita kuma ta juya zuwa ciki.
Karkaɗe seat ɗin tayi duk da an gyara gurin sannan ta zauna, cikin kwanciyar hankali ta shiga gabatar da ayyukan gaban ta, har ƙarfe sha biyu babu boss ba alamun sa gashi kuma suna da meeting da wasu clients in less than 30 minutes.
Tuni ta gama haɗa duk abinda zasu buƙata wajen meeting din ta zauna baza ido, Haisam da ta hango yasa ta ɗan sauke numfashi.
"Baze samu shigowa ba salma, tashi maza mu hada abinda ya kamata dan saura ten mins lokaci yayi".
Daukar takardun tayi Haisam ya taya ta da wasu suka nufi office din sa, tsara komai suka shiga yi wanda cikin ikon Allah nan da nan suka gama.
Ko a cikin hall ɗin meeting din haƙuri Haisam ya bayar kan rashin zuwan Abu Aulad ɗin, bakin basu wani ja ba saboda sun san shi jajirtacce ne dan haka suna san ba ƙaramin abu bane ya hana su zuwa so se suka amsa uzurin da aka basu.
Cikin walwala da farin ciki suka sallami bakin dan an samu nasara a zaman, kwangila ce suka basu na gina estate me ɗauke da gida dari uku wanda ba ƙaramin samu za'a yi ba a aikin, basu bar wajen ba seda akayi signing akan komai suka kuma transfer rabin kuɗin aikin.
Office din Haisam suka wuce riƙe da tulin papers din da akayi presenting da kuma na negotiation din, kan table ɗin sa ta ajiye masa
"Bari in koma office sir".
"Zauna salma". Haisam ya bukata yana cigaba da gyara takardun da suka shigo dasu wajen ware kowane zuwa inda ya kamata.
ÆŠan jim tayi kamar ba zata zauna É—in ba sedai tunanin ko akan contract din yake son su tattauna ko wani aikin ze Bata yasa ta ja kujera ta zauna.
Be katse aikin da yake yi ba har sead ya gama komai sannan ya zauna bayan ya ciro ruwa a fridge.
Seda ya Sha ya ishe shi sannan ya ajiye a gaban sa ya ciro wani ya aje mata a gaban ta.
"Thank you". Tace masa ba tare data ɗauka tasha ba dan ita buƙatar ta ɗaya ce yasan da ita dalilin zaman da ya bukaci tayi.
ÆŠagowa yayi ya kalle ta kafin cikin sanyin murya ya furta yayi magana
"Bashi da lafiya". Itama É—agowa tayi tana yi masa kallon rashin fahimta, bashi da lafiya?, Waye bashi da lafiyar?.
"Abdallah bashi da lafiya salma, yana kwance a gida dan seda na Kai doctor ya duba shi".
Wannan karon kam ta fahimci bayanin sa dan haka ta sunkuyar da kai cikin ranta tana tunani yaushe yake rashin lafiyar, dan ita dai har ta fito yana zaune a falo kuma bata ga wani alamun dake nuni da rashin lafiya ba a tattare dashi, to ita da ma kallo biyu kawai tayi masa duk yau, ta ina zata sani.
"Kansa ke tsananin ciwo ga kuma ciwon kirji Wanda ulcer ce ta haddasa masa shi, likita yace yana zama da yunwa shiyasa ulcer ta kama shi sosai".
"Allah ya bashi lafiya". Abinda ta iya furtawa kenan tana wasa da yatsun hannun ta