← Book details Anjane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 44

Sashe 7

Anjane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A ƙaddarar dai ya rufa miki asiri in ba haka ba mutum ya fita titi mana ya kwanta, se shegen baƙin faɗin rai yawa ƴar ƙaruna, naga kuɗin hayar ma har yanzu ina bin ku ciko amma har kika samu bakin kankanba ".

Salame dake zauren banda zarar ido ba abinda take yi jin sabuwar duniyar da ta shigo yau da rana tsaka, a gidan hayar ma wato dai ba hutawa mutum ze yi ba, ya baro masifar dangi ya shiga masifar wasu mutanen daban kuma.

"Bismilla, ina me sallama ta shigo in ga kowace da kuma me ya kawo ta tunda Allah ya rufa asiri yasa nidai ba'a sanni da cin bashi ba".

"A'a Hajiya wannan magana taki kuma me kike nufi, ina ce faÉ—an ku tsakanin ke da saratu ne to me kuma ya shigo da ni ciki?".

Matar É—aya É—akin ta yi but ta fito tana faÉ—in haka acewar ta Hajiya ita take neman faÉ—awa magana da tace ba'a san ta da cin bashi ba.

"Ai ba zan yi mamaki dan kin yi uwa kin yi makarɓiya a zance na ba Huwaila, in ma Baki yi magana ba ai se a canja miki suna, to ni dai na faɗa ba'a sanni da cin bashi ba sedai in ke aka biyo dan kece gandun bashi mara haƙuri da kaɗan a gidan nan".

Turo É—ankwali gaba Huwaila tayi da alama zata karta rashin mutunci ne se kuma ga Salame ta shigo dan ta gaji da tsayuwa ta kuma fahimci da É—aiÉ—aya da É—aiÉ—aya wannan maganar se ta fiddo duk matan gidan ita kuma ba zata iya jumurin su gama ba, so take ta sami wajen sauke yaran nan ta huta.

Kallan kallo aka shiga yi tsakanin ta da magidanta biyu wato Hajiya da kuma saratu se kuma matashiya É—aya wato Huwaila,

"Dama nace a kai ni gidan haya zan kama É—aki shine aka kawo ni nan".

"Aiho Allah sarki, ashe abin arziƙi ne ya same ni saratu da Huwaila ke neman yi min tawaiwai, shigo baiwar Allah ai nice me gidan ɗaki kuma Allah ya soki akwai ɗaya da masu shi suka tashi".

Ajiyar zuciya Salame ta saki tana É—aukar jakar ta ratse Huwaila da saratu ta shige É—akin Hajiya da tace ta shiga.

Ruwa me sanyi ta bata ta sha kafin tayi mata bayanin kuɗin ɗakin da ya ragu be kai sauran ba dan duk shine ƙarami dan haka zata bada dubu biyu wata shida dubu huɗu kuma shekara se ta zaɓa in sunje ta ga yayi mata.

BuÉ—e É—akin tayi suka shiga a tare sedai gani kaya a É—akin yasa Salame juyowa ta kalle ta

"Wanda suka saki É—akin basu sami kwashe kayan su bane?".

"To ni dai abin ne da mamaki, ganin gida suka tafi basu dawo ba dama sun ce min ba lallai su dawo ba dan haka suka kwashe kayan sawar su, wannan kuma suka ce in suka rufa wata uku basu dawo ba to sun bar min, yanzu kuma ana batun watan su na shida kenan basu dawo ba, ina ta son É—aukar kayan ina kuma tsoro amma tun da gaki ga yara kuma naga baki taho da komai ba se ki yi amfani da kayan sedai zan É—au Æ´an abubuwan amfani da nake so acikin kwanikan".

Saroro tayi tana bin Hajiya da kallo kamar wadda bata gane abinda tace ba, se da Hajiyar ta taɓa ta sannan ta sunkuyar da kai

"Amma Hajiya daga gani na yau har se ki bar min duk wannan kayan arziƙin bayan ke aka bawa?".

"Kin shiga É—akina fa kin gani mene bani dashi da zan ce zan É—auka?, wanda nace É—in ma sha'awa ce kawai irin ta É—an Adam amma gwargwado ai Allah yayi min suttura, kinga ki kwantar da hankalin ki ni ba haka nake ba dan haka ki shiga É—aki in har yayi miki gobe zaki bani kuÉ—i na".

Tana faɗa tayi gaba abinta Salame ta bi bayan ta da kallo tana murmushi, da alama matar zata yi daɗin zama ɗan alamu sun nuna bata da ƙyashi da hassada haka kuma bata da san kai.

Jakar su ta shigar sannan ta shiga ta tsaya tana sake bin ɗakin da kallo, labulaye masu kyau kuma sababbi, fenti me kyau ga katifa ma me taushi da tudu, flower vase ƙarama a gefe, dustbin, tiles, carpet ƙarami tabarma nannaɗe a tsaye ga kuma wardrobe madaidaiciya itama a gefe.

Hamadala ta shiga yi tana hawaye kafin ta kwance yaranta ta shimfiɗe kowacce kan zanin ta ta shiga gyara ɗakin..........................✍🏻.

©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️Ote, Comment and share please.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 06 [ 11/27/2022 9:29 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★

_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.

                      FREE PAGE 06

_______________________📖 Seda ta Gama gyara ko ina dan dama ƙura ce kawai a ɗakin sannan ta lura da ƙaramin toilet tsayuwar mutum ɗaya, wanke shi shima tayi da ruwan da Hajiya ta bata jarka biyu ta roƙe ta gawayi ta ɗora musu ruwan wanka.

Ƴan biyu ta fara yi wa wanka sannan itama ta samu tayi, bata iya ta nemi abinci ba ta kwanta bacci saboda gajiya.

★★★★

"Haba bawan Allah, ya kamata a ce ka saurara wa kanka wannan ɗimbin damuwar, fisabilillah shikenan kai in aka ga fara'a a fuskar ka sedai fake, ka sake kayi rayuwar kamar kowa ka ƙi, in ance dalilin da yasa rayuwa take zamar maka baibai kuma kaƙi yarda".

A hankali mutumin da aka kira da bawan Allah ya shiga É—ago kan sa daga sunkuye da yake har ya É—ago baki É—aya.

Tsurawa wanda ya gama magana ido yayi na wasu sakanni kafin ya miƙe tsaye yana duban agogon hannun sa, bece masa komai ba ya shiga tarkata takardun sa ya zuba cikin briefcase sannan ya fita.

Baki buÉ—e É—ayan mutumin ya bishi da kallo kafin kuma ya gyaÉ—a kan sa ganin yau iskancin bawan Allah har a kan sa, halin sa ne dama Amma ze iya rantsewa ya manta rabon da ya karta masa in ba yau ba.

Fita yayi yana sanar da masinjan sa ya kulle office É—in shima ya fita, kamar yadda yayi tsammani be ga ko shatin tayar motar sa a parking space ba, tasa ya shiga ya bar building É—in shima.

★★★★★

'Ban san wane irin aiki na tafka ba, ban san wace irin ƙwaƙwalwa gare ni ba da kullum bata bani mafita miƙaƙƙiya, duk da Riyya ta faɗa min nayi gaggawa in jira tukunna amma ni gani nake in na zauna to zan ta jira ne har na gaban abada, in bana son haka ya faru me zanyi kenan, me zan yi?!'

Wannan shine tunanin da matashiyar ke tayi tana kai kawo a madaidaicin falon da yaji kayan alatu da alama dai tana cikin state of confusion ne dan se cije yatsun hannunta take cikin son samun mafita.

Shigowar wata dattijuwa É—akin yasa ta nemi kujera ta faÉ—a kamar wadda bata da laka, kallon ta dattijuwar tayi tana kaiwa zaune itama kan wata kujerar kafin ta shiga mata kallon tambaya

"Yanzu shikenan Anna mu haka zamu zuba ido muna kallon komai na faruwa a gidan nan, ki duba fa watan yaya nawa yanzu da rasuwa amma ba wanda ke bin takan mu ke kuma naga ma abin ko ɗaɗa ki da ƙasa be yi ba".

"Ni kin sa ba wani gane magana cikin magana nake ba gwara ki fito fili ki sanar dani me ke faruwa a gidan bamu sani ba".

"Amma Anna kin san in mukai sake mun kusa barin daular nan mu koma kwana ƙarƙashin gada ko?".

"Tuf tuf, Allah ya tsare ni.....". Anna ta faÉ—a tana tofar da miyau a gefe

".....banda neman masifa da bala'i irin naki me yakawo batun komawa ƙarƙashin gada kuma da ko a mafarki na gani in na tashi se na yi sadaka".

"Nima ba so nake yi ba sedai in dai bamu motsa ba abinda ke daf da faruwa kenan".

"Dan Allah yi min dalla dalla dan kin san bana san jan rai a magana".

"Kamata yayi ace nice Abdu ze aura amma muna nan mun zuba ido yanzu haka naji jita jitar ze aure Æ´ar uwar Hajiya Babba".

"Kam babban bu**uba, ni za'a kawo wa iskanci har gida, lallai Hajiya Babba ta É—ebo ruwan dafa kanta, ki kwantar da hankalin ki Audu bashi da wata mataa gidan duniya suke, da alama zan gwada musu barikanci na da basu sani ba".

Cikin jin daÉ—i matashiyar ta gyara zama tana kai fuska gefe

"Atoh abinda ya kamata dai muyi kenan dan yana auro wata kin san dole zamu bar gidan nan tun da yaya da ta haÉ—a mu ta raba Ni kuma shine bana fata".

"Ki sa a ranki hakan ma baze taɓa faruwa ba, mu da gidan nan kuma mutu ka raba, mun shigo shi kenan fita kuma ba rana".

★★★★★

"Amma dai kin san ni ke san auran yarinyar nan shine kike wani batun wancan lusarin, yanzu da nayi magana kuma kice komai dan mu kike yi, ko ina basira a wannan tunanin naki oho, na daɗe ina faɗa miki tsufa yasa duk wata basira taki gujewa amma kin ƙi yarda, to wannan karon kam sedai kiyi haƙuri dan wallahi ba zan iya bin tsarin ki ba".
Chapter 7 · 0% Book details