← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 38

Sashe 8

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirub Addawiyya tayi kamar ba ita ake tambaya ba.

"Autan Ummi kefa nake sauraro.

"Aunty jiyane nayi mufarki zaizo yau kuma nasan tabbas zaizo sabida wata rana mufrkina yana zama gaskiya.

K'uri hindu tayi mata d idanu zuwa can taja nufashi tace "nafahinceki amma hak'iqanin gaskiya autan Ummi lamarinki yasoma bani tsoro.

"Kidainaji tsoro komi aunty baiwace kowa da irin nashi

"haka ne kam.

"Autan ummi amma fa inaji ajikina inyazo da matsala.

"Eh wallahi aunty ba mutunci zaizo kuma yasan kina da cikinsa d'an wata d'aya koda kuka rabu, yanzu kuma yana tunanin ya kai watani biyar kenan.

"Ya ilahil alamina!! Ni hindu yazanyi? "Aunty ki tubure mishi ke bakida komi tunda ko su mama basu san kin zubda cikin ba.

Idanu waje Hindu take duban Addawiyya, cikin rawar baki tace "autan Ummi wai wayake fad'a miki sirri mutane ne?

Abarcina naganki tun sanda kika aikata abin domin ma har kwanciya kikayi a asibiti na kwanaki biyu, to nad'auka shirmen mufarki ne, sai yanzu nagano da gaskene don naga adnan din yana ta kuri sai kindawo gareshi kodon abinda zaki haifa amma fa bata lalama zaibi ba ta tsiya da tijara wai ganinshi kece kika cuceshi da kika gudu da aurenshi kika kumayi biris da lamarin shi.

Ahankali Hindu tace "autan Ummi baki da wayon dazan fad'a miki abinda yasa na guji zama da Adnan amma inamai tabbatar miki shine ya zalunceni yayimin qarya alhalin shid'in mara asaline wanda bawanda yasan inda iyayenshi suke kuma rayuwarshi gaba d'aya sabon Allah ne.

"Aunty rabuwarku shine mafita kuma gara da kika zubda cikin domin had'a zuri'a da irinshi hatsari ne, kuma yanxu koda yazo ki rufe idannu kici masa qaniya ta haka zaiji shakkan sake tunqaranki kuma atake zai baki takardanki ki huta da shegen aurenshi.

Cike da mamakin basiran yarinyar Hindu tace "autan ummi wai shekarunki nawa yanzu?

"Goma sha hud'u da watanni.
"Ok, amma fa kina da azancin iya magana gashi wayonki ya girmi shekarunki.

Kwantar da kanta tayi a cinyar Hindu tace "haka mutane ke fad'i, hatta Abbi yafiso yayi shawara dani fiye da Adda Salma.

"Aikam Salma sokuwa ne ba wayau sai uban iya fushi, abu ba abu ba tayi ta hawa kamar garin kwaki.

Dariya Addawiyya tasa tana cewa "kuma kinsan fa abincin Adda ne kwaki, sosai take son shanshi dayin qosanshi.
"Nima na shaida hakan, tunda gashinan mushaffa'u yakoyi cin qosan, kamar wasu dikkawa.

Dariya sosai sukayi sannan suka cigaba da hiransu amma lokaci2 Addawiyya sai duba gefen damarta ta gyad'a dai, ita kam hindu batama san tanayi ba.

Washe gari suna shirin tafiya motar Adnan ta iso bakin bukkan su Addawiyya, baiko gyara parking ba ya kashe motar ya fito yasoma tsula rashin mutuncimshi.

Duk tsayawa sukayi cirko2 suna kallonshi cike da ta'ajibin dalilin faruwan hakan alhalin sune suke jiranshi dayazo yayi musu bayanin abinda kefaruwa tunda ita Hindu taqi cewa komi duk tsawon lakacin da ta kwashe zaune agida.

Zuwa can mushaffa'u ya shammaceshi ya d'agashi sama ya soka da k'asa yayi ta bugu.

Mutanen qauyen suka sami abin kallo, saida yahad'a mishi jini da majina sannan Abbi yayi nasaran rabasu.

Atake Adnan ya rubuta takardan saki ya cillawa Hindu ta d'auka ta shige ciki tana kuka.

Abbi ya matsa domin yabashi haquri ya tureshi kad'an yarage bai fad'i ba.

Mushaffa'u ya zabura zai kuma dukanshi mama ta riqeshi tace
"wandama kayi mishi ya isa, barshi ya wuce duniya ce.

Afusace yaja motarshi ya wuce, bakinsa tare da hancinshi zai zuban jini yakeyi sannan aqasan zuciyarshi kuma tunanin abinda zaiyiwa mushaffa'u yakeyi.

Aciki kuwa Hindu kuka take tayi kamar ranta zai fita.

Addawiyya dake zaune gefenta ta soma share mata hawaye tana cewa "kyaleshi aunty kansa yayi mawa kuma yanzu haka yana tace da masifa tunda garin yawon banzanshi yaje ya kwaso k'anjamau.

"Nashiga uku, yasamin kenan yanzu? "A'a aunty ke bakya tare da cutar komi domin sanda ya aureki lafiyarshi lau, bayan kin barshine ya kwaso abinsa.

Shiru hindu tayi tana mai cike da mamakin lamarin Addawiyya, yarinya kamar goyon aljannu.

Dariya Addawiyya tasaki tace "nikam wallahi goyon bin'dama ne.

Idanu waje Hindu tace "nashiga uku, ko dai maganar Salma zai tabbane da tace ked'in rabinki mutum ne rabinki junnu.

"Au wai sai yau kika fahimci Addwiy tana da matsala aunty?

Cikin tsiwa ta tari gaba Salma tace "waya kasa dake?

"Yanzu zan zubarmiki da haqora wallahi, kindai sanni sarai bana d'aukan rainin wayonki.

"Eh na sanki kam, amma a fannin kare martabanki baki iya tsinana komi sai tura baki kina wani cewa "banso2 kamar wata sakarya.

Afusace tayo kanta tayi saurin maqalewa a bayan Hindu tana yimata kwalo.

Ficewa Salma tayi tana cewa "mai rabani da yarinya yau sai wanda yabusan numfashi.

"Kedai tafi wurin mijinki, kud'ora daga inda kuka tsaya jiya.

Afusace Salma ta dawo ta fizgota abayan Hindu tayi d'akinsu da ita, hindu tabiyo bayansu Salma ta kulle qofan.

Daga ciki Addawiyya tace "yi tafiyanki aunty na isheta riga da wando domin ba'abin da zata iyayimin duk tarin burgane.

Hindu dai dariya tayi tabar qofan ta nufi inda su Abbi suke zaune. Inda sukayi ta bata baki tare dayimata tuni akan yarda da k'addara.

Sai bayan la'asar suka sami tafiya wanda har da Addawiyya suka wuto sabida takafe ita sai ta koma makaranta aranar, sabida an wuceta sosai akaratu.

Ita suka fara saukewa a school tana ta kuka dakyat suka shawo kanta tayi shiru sanna suka k'arasa cikin gari.

Washe garim ranar Salma da Mushaffa'u ne zaune cikin garden suna hiransu ta masoya.

Ya rungumeta a jikinshi yana lalibenta, kamar yarda yasaba.
Cikin fushi ta kwace jikinta tasoma magana "wallahi yaya bana sin abinda kakemin ko don kasanni d'in ba virgin bace shiyasa kakemin haka?
"Honey mi yakawo wannan maganar kuma? Nifa ke nakeao da k'auna ba jikinki ba.

"To indai kayarda da haka kabar tabani har sai shedu sun shaida na zama mallakinka, in kuma kacigaba damin haka zan fasa auren muhaqura da junaid.
"Nabari honey wallahi, inkuma kinga naqara kimin duk hukuncin da kikaso.

Murmushi tayi tana mai jinninawa qanwarta Addawiyya databa wannan shawaran.

Haka ko yafaru domin tsawon kwanakin da suka biyo baya ya kame gabbanshi daga lata mata jikinki saima yasoma azumi donmin samun kariya daga afkawa cikin sha'awar datake yawan taso mishi wanda bai samun sauqi har sai ya kai hannunsa jikinta,sannan ya qagara su Abbi su iso ko atsaida lokacin bikinsu ya Hutu.

Ita kam Salma hakan yayi Mata mugun dad'i tunda gashi har yamaida hankali da bautan ubangijinsa ta hanyar yin azumin nafila. Sai takuma qara jinjiwa Addawiyya da kuma godemata sabida ita ce sanadin tsamosu ga fad'ama sabon Allah SWA.

**** Bayan sati biyu su Abbi sukayo parking din kayansu sukayi ban kwana da mutanen garin jangaba suka nufo kwantagora amma kafi su isa sai suntsaya a makarantar su Addawiyya sun d'auketa domin ason ran Abbi kwana 1 zasuyi agarin su d'uki hanyar birnin kano don tuni ansama musu gidan dazasu zauna.

*TUNA BAYA* (Nasabarsu)

*mrs j moon*
[12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*Ina kuke 'yan mata Adon gari, ga page d'inku nabaku shi kyauta.*
*Maryam Rano*
*Maryam Kaumi*
*Ummiey Ahmad*
*Fatima kaka malam*
*Khady kd (my inlaw)*
*Aisha gombe*
*Pretty (meena)*
*Exclusive (zainab)*
Allah ya kaimu lokacin bikinku musha bidiri bired'e Ameen👏🏻😊

*17~18*

Malam Yusuf shine cikakken sunar Abbi? Haifaffen garin jangaba ne, mahaifiyanshi tare da k'anninshi uku biyu maza d'aya mace wutane ta yi ajalinsu lokacin shi yana can cikin garken shanu yana gad'insu, wutan ta tashi kokafin akawo agaji wutar ta lashesu sanadin haka mahaifinshi yakamu da ciwon zuciya shima bai jimaba yace ga garinku nan sakamakon haka sai yataso maraya.
ga dukiya ubanshi yabari sosai amma 'yan uwanshi sukace nasune yake yi musu kiwo kuma bawanda ya musanta hakan a garin sabida haka suka k'wace komi su bar mishi wata tsohuwar saniya wai ladan kiwon da yariqa yi yayi kuka har yagode Allah kawunshi yayan mahaifiyarshi daya rage mishi shine yayi tabashi baki ya nuna mishi wuta sukaci kuma da yardan Allah bazai amfanesu ba.

Haka nan yacigaba da rayuwanshi a gidan kawunshi ya kuma jefa karsanan shi cikin garken kawun duk da suma basu da yawa domin basufi bakwai ba.

Bayan shera saiga sanuwa ta haifi 'yan maruk'qa biyu suna isa yaye suka saida uwar suka bar 'ya'yan sabida ta tsufa.
suka sayo wasu mata biyu suma shekara na kewayowa suka haihu 'yan bibiyu.

abufa yayi albarka sai gashi a cikin shekaru uku shanun yusufa suntasarma kusan ashirin banda tumaki da raguna ga kaji tare da zabbi.

Ganin haka sai yacewa kawunshi zai shiga duniya neman ilimi sabida ilimi Addin yayi qaranci sosai ayankinsu, bai hanashi ba saima addu'a daya bishi dashi.

Ya soma isa garin kwantagora a inda yahad'u da wani matashi mai suna Abubakar ya taimakeshi ganin yana tare da k'auyenci, ya kaishi gidansu ya kwana washe gari ya kaishi tasha ya sashi amotar garin Zaria birnin ilimi sabida yasanar mishi cewa ilimin addini yafito nema shine yaga ba inda zai samu mai nagarta irin birnin zazzau.

Ya iso garin zaria daf da la'asariyya, ranar ya nemi gidan shehin malamin dazai soma karatu, wani mutum yayi mishi jagora zuwa gidan lamamin mai suna Alhaji malam Haruna mai riguna. yanemi iso atake kuma akayi maraba dashi domin gidane na karamci da nagarta, kowa nasune domin irin adalcin mai gidan, yasa ake karrama bak'o kodaga ina yazo sabida yakance shima ai zuwa yayi gashi har yazama wani abin wanda har ake zuwa wurinshi.

Anan yusufa yasamu karatun AL-QUR'ANI dawasu littafai na addina sai yakoma gida amma akwantagora ya sauka.
Abokin shi Abubakar yayi ta mamakin ilimin da yasamo.
Washe gari yayi misu bankwana ya nufo qauyensu kafin ya shiga mota yaji wani yana bawa abokinshi labarin ya kosa yakoma kano yacigaba da sa'arshi.
Sai yayi tsam da ranshi atake kuma yaji bazai koma garinsu baida komi ahannumshi ba sai kawai yanufi wurin saurayin nan yayi masa sallama ya fad'a mishi intafiya zaiyi to zai bishi, atake saurayin mai suna gambo ya amince suka shiga motan kano.

Ya shigo garin kano da qafar dama sabida a shera 1 yasami alkhairi mai tarin yawa, fad'i yake lallai tacika tumbin giwa.

Sai ya shirya yayiwa abokinshi Gambo bankwana ya nufo gida.
Chapter 8 · 0% Book details