← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 38

Sashe 18

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amin Amin my Addawiy, wallahi kinsan kuwa abin yana bani haushi sosai, ya zauna ya kalla agida amma yaqi innafiye qorafi yace kallo tare da friends yafi dad'i wai anayi na ihu hakan yana shashi nushad'i.

"Uhmm Allah dai ya kyauta.
"Amin.

***Kwanci tashi ba wuya gashi Addawiyya ta kammala secondary har tasoma zuwa computer training center kafin result ya fito.

Yau tadawo gida agajiye ta zube a parlor ta dafe kanta datakejin kamar zaiyi mata ciwo.

"Mai babban suna mazumunciyarki ta haihu yanzu ta sami 'yan biyu dukansu maza, yi sauri ki isa tun kafin makiran matar can ta kashe mata su da guba.

Wani zabura tayi tafice waje da gudu tana kwallawa driver kira ya iso a rud'e, tace "gidan aunty Hindu, da sauri yayi reverse suka fice.
Ummi tafito daga cikin tayo compound da sauri sakamakon jin ihun kiran da Addawiyya keyiwa driver, don ita ba tasan ta dawo ba, jin hayaniyarta tayi kawai.

Ko kafin ta iso sun fice, asanyaye ta qarawa wurin get man tace "baba mike faruwa? Cikin girmamawa ya amsa " Hajiya naji tana kiran gidan Hajiya Hindu zasuje "to ko lafiya? "Wallahi bansani "ok to Allah yasa muji Alkhairi "Amin Hajiya.

Jiki ba k'wari ummi takoma ciki, tana isa wayar na qara alamar kira, ganin sumar mijin Hindu yasa jikinta d'aukan rawa.

Hamdalah tayi ta jerawa sanda taji cewa Hindu ta sauka lafiya kuma a gida.
Sai sannan tagano sanadin fitar Addawiyya agigice.

"Auta manya halinta sai ita, mai makon ta tsaya ta sanar dani sai kawai tafice kamar yaqi.

Ko gama gyara perking bai yiba ta balle door d'in tafice da gudu bako gyale jikinta.

Shigarta parlorn yayi Dai dai d'aga feeder da Hajiya karima tayi mai cike da madara zata bawa hussain.

Wani tsalle ta doka kamar 'yar chana ta buge feedern ya fad'i qasa murfin ya bud'e yasoma zubewa tayi sauri d'awa gudun kada yazube duka tarasa tujja.

Jikin Hajiya karima ba'inda baya rawa don tsaban firgici.

"Nashiga uku! Anya yarinyar nan mutunce kuwa? Tafurta hakan cikin rawar baki.

Wani kallo Addawiyya ta sauke mata sannan ta d'auki yaron daga jikinta tace "ki tanaji bayanan da zakiyiwa polices, ta shige bedroom din Hindu tabarta nan zaune kamar gari.

*mrs j moon*
[1/14, 12:25 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATU ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*Shafin na masoya ne dake dukkanin lungu da saqo, ku sani sosai nakejin dad'in yabawarku tare da addu'o,in ku agareni, domin haka shi yake qaramin qarfin guiwa, godiya nake agareku sosai fans. Allah yabar kauna, luv u always* 😍😘

*30*

Turus Hindu tayi sanda ta fito daga toilet ta cimma Addawiyya zaune hawaye jage jage a fuskanta.
Cikin rawar jiki ta isa inda take zaune ta dafa kad'anta tace "autan ummi mi aka miki?
Mai makon ta amsa mata sai ta fashe da kuka mai sauti.

Gaban Hindu ya yanke ya fad'i rass!!! Ta zauna gefenta jiki ba k'wari ta kamo hannunta ta rintse qam tace "fad'amin damuwarki Addawiyya, ko bakiso nasami qaruwan twins bane?

Da sauri ta girgiza kai tana jan hanci tace "tunani nake da ace hussain ya rasu ko ya zakiji aranki.

Cikin daburcewa Hindu tace "autan ummi wani abu ya farune? "Eh, ta amsa mata tare da bata labarin tundaga sanka taji uncle Habibullah yayi mata magana zuwa sanda ta ceci jaririn ahannun hajiya karima ta d'ora da cewa "amma ina mai roqonki dan Allah tare da manzonsa kada kisanar da kowa zancen, ita da kanta zata fad'a da bakinta intaji azaba.

"Autan ummi kinaganin rashin d'aukan matakin ba zai kuma bata dama wata rana tadowo ta cutar dasu ba?

Jim tayi tana nazari "bana tunanin zata kuma samun kuzarin sake cutar dasu, sabida yanzu haka tana cikin rud'anin kamata danayi tare da fargaba kada Alhaji yaji kuma tana mugun tsoron 'yan sanda, tana can ana fetsa yawo. Tagarasa maganar cike da dariyan mugunta, hawayen daya maqale yazubo a fuskanta ta sa hannu ta share tana cigaba da dariya.

Kama kunninta Hindu tayi tace Allah shiryamin ke Addawiy "Amin.

" Allah yacigaba dabamu kariya gabaki d'aya.
"Amin.aunty shine addu'ar da yadace muyi tayi kawai domin ita kaddaran Allah wanzarciya ce inta tashi zuwa babu tsimi babu daraba sai ta ilahu.

Atare Salma da Ummi suka iso, sai murna sukeyi suna hamdalah ga Allah.

Addawiyya tun shigowarsu dasun had'a idanu da Salma sai ta sa dariya.
Ummi ta dubeta tayi mata daquwa "kinci gidanku auta, yazakisa mutane agaba kiyi tayi musu dariya kamar wata mai tanbotsai.
Dariya takuma kwashewa dashi har da riqe ciki, ummi ta zabura tayo kanta ta kwasa da gudu tabar room d'in.

"Ummi kibarni da ita, nasa abinda take ma dariya kuma zanci mutuncinta inbata kiyayeni.
"Oh to kunfi kusa ai, nawa idanu.

Hindu ta sauke kallonta bisa tumbin Salma ta kauda kanta gefe tana dariya qasa2 tace "eh dole autan ummi tayi ta dariyan murna ashe mun kusa samun wani qaruwan ne.

Cike dajin kunya Salma ta miqe ta fad'a toilet, suka bita da dariya.

"Allah yaraba lafiya, "Allahumma Amin umminmu.

Mugun karo sukayi da juna ta kwalla qara ta zube aqasa, domin tayi mugun tsorata da ganinsa abazata, cikin hanzari ya d'agata yana kiran "sorry sorry, ta zame jikinta hannunta dafe da qirjinta, tafiya soma yi da baya da baya eyes d'inta yana kanshi har ta shige cikin kitchen.

Ya dafe kansa tare da cije labbanshi, ya saki murmushi mai sauti "i really luv u pretty, yafurta ahankali sai kuma ya yamutsa fuska "uhmm Allah kin wuce pretty akomai my heart, beauty zaifi dacewa dake my kwaila sai yasaki dariya ya dungule hannu ya naushi iska yana mai furta"amma fa Hameed d'an air ne, yanzu wannan zankad'ed'iyar budurwan yake kiranta da kwaila?

"Eh, Nakiratan mi za'ayi? Kai kwanso ma sunarta daga yanzu. Muryan Hameed ne ya doke kunninsa, ya juyo yana jifanshi da harara.

"Mantawa kayi fara ce.
"Eh, hakan ma yafi dad'i, naushi ya kai mishi ya kauce da sauri yana dariya. "Zan gyarama zama Allah "uhmm mr love ina saurare.

Bai kuma kula shiba ya shige bedroom d'in Hindu d'auke da sallama, Hameed yabi bayanshi yana tsokanar shi.

Addawiyya tana shiga cikin kitchen ta jingina da bango idanunta lumshe sai murmishi take dokawa tamotsa labbanta kad'an tace "he is very charming guy, uhmm ina son.... Sai kuma tayi saurin bud'e eyes d'inta ta tafe bakinta tana girgiza kai, jin motsin za'a shigo yasa tayi saurin bud'e qofa tafice ta baya ta nufi part d'in Hajja.

Khairi ta cimma zauna tana kallo bata dubi inda takeba ta wuce kitchen inda takejin motsin ana aiki da alama hajja ce.

Dogon tsaki khairi taja tace "shishshigi ba kwarjini, banza 'yar maula ka wai.

Bataga dawowar ta sai jin saukan mari tayi a face d'inta tassss!!!! Ta dafe wurin tana laliben hanya sabida ganinta ne ya d'auke na wucin gadi, tana ko samun hanya ta d'iba karce har tanajin tuntube yatsarta ta fashe amma ko dubawa batayi ba, burinta ta kawai taga ta tsira daga shan maru kan Addawiyya domin har yanxu bata manta da artabun suba na kwanaki ba.

Dariya ta saka har da dafe ciki tana nuna hanyar da khairi tabi da gudu.

Hajja ce ta fito d'auke da babban kula, ganin Addawiyya na dariya yasa ta koma kitchen da hamzari jikinta yana kyarma sabida ji tayi sautin dariyar wani iri kamar ba na muta ne ba.

Shigowa kitchen d'in tayi anatse hajja taja baya.
"Uhmm hajja dariyan nawane yabaki tsoro ko mi? To bara kiji abinda yasani dariya.

Tana gama bawa Hajja labari itama tasoma dariya tace "amma Rabi'a kinyi mugun tsorata min qawar hirata.
Cikin dariya ta amsa "gyara mata zama nakeyi, kuma yanzu muka soma buga game d'in har sai ta dawo cikin natsuwarta zan sarara mata.

"Lallai hakan yayi kyau d'iyar albarka, Allah yabaki sa'ar saita mana tunanita ta bar yiwa mutane fitsara.
"Amin hajjajunmu.

*****Ranar suna yara suka amsa sunarsu hassan da hussain.

Anyi barin naira, mutanen arziki sukayi ta zuwa suna kwasan gara.

Hajiya karima kam kamar zata had'iye zuciyarta don tsaban baqin ciki da yayi mata yawa gashi Addawiyya takasa ta tsare ta hanata halaka su kotaji dama dama, sabida dazaran ta doso part d'in Hindu sai wani hucin zafi ya dameta akan dole zata koma tana tsinewa Addawiyya, taje wurin malamanta sun kasa gono dalili afkuwar hakan, hakanan tanaji tana gani aka gama taron suna cike da masara.

Alh. Muktar ya biyawa Abbie, ummi, Addawiyya, mushaffa'u, Abba, mama, tare da Salma kujerun makka, yayin da zarar Hindu ta gama wanka yace zasu wuce umrah kuma baza su dawoba har sai sunyi aikin hajji wanda yanzu saura kimanin watani shida asoma tafiya.

Labarin yayi mugun jefa hajiya karima cikin rud'ani wanda atake jininta yayi mugun hawa ta yanke jiki ta fad'i aka kwashe sai asibiti, dakyat doctors sukayi nasaran ceto ranta amma fa taji jiki sosai, khairi sai kuka takeyi gunin ban tausayi.

Kakan su Hindu mahaifiyar maman su itace take kula da ita tare da yaranta.
Hajjama ba'abarta abayaba, ga ummi tana yimata soqo akai akai nakayan gyara da samun ruwa nono sabida Alh. Muktar yace baza'abama yaranshi madara ba nonon uwa yafi komi inganci ajikin jarirai.

Ita kam Addawiyya kuwa ta tarewa tayi agidan, islamiyya da computer school duk tana take zuwa ta dawo, ummi tayi mitan har tagaji na tadawo gidan yayi mata girma ita d'aya amma taqi.

Sunyi mugun shaquwa na ban mamaki da Hameed yayin da duk sanda suka had'u da Haydar ko taji muryanshi sai gabata yafad'i ga kuma wani tausayinshi datakeji acikin ranta.
zuwa lokacin tagama ganewa ta afka kogin son shi abinda take ta boyewa kada kowa yasani domin aganinta baqaramin zubda aji bane mace ta fidda soyayyarta fili ga namiji.

Shi kam Haydar yaqi sanar da ita ne sabida ganin yayi kamar tanajin tsoronsa yafiso su saba da juna sosai kamar yarda ta sake da Hameed.

Yau tana zaune cikin garden laptop ne agabanta tanayin assignment, gefenta had'ad'd'iyar phone d'inne take ta sauraren cool music, sai gyada kai takeyi abinta cike da nishad'i.

Yana zaune a balcony yana aikin kallonta yana doka murmushi, zuciyarshi sai azalzalanshi take da ya isa wurinta amma miskilanci ya hanashi motsawa. Ya kulle eyes d'inshi yana tasbihi cikin ranshi.
Chapter 18 · 0% Book details