← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 38

Sashe 16

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

juyowa Addawiyya tayi ta sakarwa hajiya karima harara, ahasale tayo kanta da bugu, hindu ta tareta da hanzari "hajiya ya isheki abinda kikemin agidan nan, ki kama ragowar girmanki dayarage, tun kafin ya qarasa zubewa a idanuna tam.

"Bazan kamaba kinji ko? kiyi duk abinda kike da niyya, gaiyar tsiya kawai, jinin hatsabibai, masu mugun abu, to wallahi dani kuke zancen, kusani ni karima naci dubu sai ceto ballantana ku qananan k'wari, na d'auki aniyar bazan bar kowa ya shaqata ba a cikin ku saina baku mamaki matuqa.

Tsaki Hindu taja "Allah shine gatanmu hajiya ke baki isa kiyi mana komi ba sai da izininsa kuma maji roqon bayine shi don haka mugun nufinki sai dai ya qare mikk can amma mu kam muriqe babban takobin yaqi wato addu'a.
"Zaki gani yarinya "naga Alkhairi.

Ta kalli Addawiyya cikin had'e gira tace "Autan ummi mi kikama 'yarta?

"Mari na tayi ni kam nayi mata hawa 12, kuma ko yanzu ta kuma zuwa part d'in nan sai nayi mata hawa 24 wanda sai ta suma, in kuma kina ganin wasa nakeyi ki turota ki sha kallo, ta qarasa tana yiwa hajiya karima kallon tabbatarwa.

Baki sake hajiya karima take kallon 'yar qaramar yarinya tana fad'a mata magana amma takasa cewa komi, domin zuwa yanzu lamarin yarinyar yasoma bata tsoro sosai.

"Ficemin a parlor ko in baki mamaki, wawiya kawai.
"Ni ce wawiyar Hindatu? "Eh, har wofima kece, mara tunani.

"Qara mata da shasha sha, doluwa wanda girmanta bai mata komi ba sai mai data mashirmanciya da yayi. Alh. Muktar ne yake fad'an haka sanda yafito daga room d'inshi, ko su hindu basu san yana ciki ba sabida tabaya ya shiga.

"Alhaji, ni kake watsawa qasa a idanu haka gaban wad'an nan banzayen?

Tasss!!! Sautin marin da Alh. Yayi wa hajiya karima kenan yakuma nuna mata qofa yace "get out ko in miki abinda yafi haka.

Afusace tayi waje tana cewa "had'uwarmu da ku bazai muku kyau ba.

Dariyan Addawiyya ta ki da qarfi duk don hajiyan tajiyota kuma taji d'in.

"Dear bana ce dake kada ki kuma kulata ba? "Affuwan Abban Hameed kaga wacce ta tabota nan, ta nuna Addawiyya.

"Uhm Rabi'a mi ya had'aki da ita?
Duk abinda yafaru ta fad'a mishi.
Yaja numfashi yace "kinmin dai2 don khairi bata da kunya sam, ta rainamin uwa sosai amma zan d'auki mataki sosai akai, shi kuma Hameed zanci qaniyarshi mai makon ya raba sai ya kuma zigawa, kai halin Hameed sai shi, sannan ni da kaina nabaki umurni duk sanda takuma gigin tabaki kiyi mata duka wanda bazata taba mancewa da keba, kinji? "Tam Abba.

A'a Abban Hameed ba'a haka kada ka zuga autan ummi tayi aika aika, abinda yafi dai ka tarasu kayi musu nasiha tunda dukkansu yarinta yana damunsu.
"To zan duba yiwuwar hakan maman 2.

Kauda kanta tayi gyefe tana murmushi.
Nan ya zauna yakuma yi musu hasiha sosai.

"Beauty!! Beauty!!! Yashigo yana kwallawa Addawiyya kira, ita kam tana zaune a parlor tana buga game a laptop d'in hindu.
Zama yayi gefenta tare da rufe laptop d'in "yakinaji ina kiranki kikaqi amsawa?
Sai da ta juya mishi manyan idanuta san nan ta amsa kamar mai ciwon hak'ori "banzaci nice keda suna hakan ba.

Kallonta yakeyi bako qirtawa, ta miqe ta shige bedroom tabar mishi wurin.

Tsaki yaja mai sauti ya ture laptop d'in gefe ya miqe ya fice bayan ya ajiye mata kwalin sabuwar wayarta da yasayo mata zai bata amma tawani tsaya yi mishi yanga, acewarshi.

Ni ne yarinyar nan zata yima yanga? lallai kuwa zan fita harkanta don kada taga kamar ina sonta ne, wani tsakin ya kuma ja, afili ya furta "ko cika budurwa bata gama yiba amma ta san kan iskaranci haka.

Haydar ya dubeshi ya tabe baki ya miqe ya shige bedroom d'inshi, da harara Hameed yabi bayanshi yanajin kamar yabishi ya rufeshi da duka na halin ko'inkula da yake nunawa mutum in dai balamarinsa bane to baruwanshi ko mi zakayi bazai tambayeka ba sai indai kaine ka bara kasanar dashi to zai saurareka shima bawani abin arzikin da zai tabuka sai dai kalmar yi sorry, kalmar datake mugun batawa Hameed rai kenan duk sanda ya fad'a mishi ita.

Ranar sunday da yammaci Addawiyya tashirya zata koma gida, Hindu ta rakota har bakin mota tana jadda mata zatayi kewarta sosai.

"Aunty kada kidamu ina tare da ke ai, komi ya shige miki duhu ki kirani awayar ummi zan warware miki
"tam, Allah bar kauna "Amin.

Sai da ta gyara zama a cikin motar sannan ta miqowa Hindu ledar da Hameed ya ajiye mata jiya wacce yake d'auke da sabuwar waya ta kece raini.

"kibashi kayarshi, kice masa Abbiena zai sayamin in lokaci yayi kuma ina bata mishi rai yayi haquri.

Amsa Hindu tayi batare da tace qalaba ta.

Suna d'agawa juna hannu har tafice get.

"Aunty mike damun sistern ki? "Babu komi "to minayi mata data kasa amsan kyau tata? Ko dai tayi mata qarama ce sai na sanja mata wanda ta fita komai?

"A'a babu ko 1 Hameed, inaga dai sabida Abbie yace sai ta soma university zata soma riqe phone shine yasa taqi amsar gift d'inka.

"Uhmm tam zanko ajiye mata har sai ta soma jami'ar.

Dariya Hindu ta saki tace "azubo maka abincin ne? Ta kauda zancen
"No am ok, yanzu naci snacks a wurin Ya Haydar "ohk to kaci anjima ai "eh, zanci insha Allah.

Gyara zama yayi ya koma serious yace "aunty ina son inyi aure, wacce yarinya kikaga ya dace ta zamo abokiyar rayuwata?

"To pah!! Hameed ni kam bansan zabin da ranka ke soba "aunty bana da zabi sai wanda kika zabamin domin mai yanayin rayuwarki nake so wacce bata da hayaniya ga iya tattali da natsuwa, ko da kuwa cikin qanninki ne ina muradi.

shiru Hindu tayi tana nazari zuwa can tace "bana da qanni sai Addawiyya, ita kuma a kwai d'an aboki Abbie dayake sonta.

Ya mutsa fuska Hameed yayi kamar mace yace "a'a nima bana rajinta, kidai nemomin wata koda cikin students d'inki ne amma mai aji da kyau kuma mature enough nake so ba yarinya qara irin qanwarki ba Addawiy take ko wa? Dariya tayi sosai.
"To Hameed zan duba nagani, amma hakiqa ka had'ani da aiki.

Dariya yasaka tare da miqewa yace "kawo saqon da zan kaiwa su Abbie don yau zanje nagansu duk da basu sanniba "aiko suna ganika zasu gane daga inda kazo, sabida kamannin Abbanka dazasu gani atare da kai.
Aunty hoo, Ya haydar shine ziryan Abba amma ni hajja nabiyo, "haka dai kace amma sosai kuke kama da juna ku duka hud'un.

Ya shafi sajansa ya amsa "To nayarda Aunty, saura ki haifo mana brothers nd sisters masu kama da ke, kinga an surka kenan.
"Uhmmm tace, tare da miqe tanufi room d'inta saida ta kusa shiga tajuyo tace "agaishemin dasu Abbie sosai, acewa ummie tayimin dambun zogale ka zomin dashi, ta zubamin man shanu ne ba man gyad'a ba.
"Ohk don't worry I'll tell her.
"Thanks, se kadawo, ka sayomin yalo farare tas nake so.
"Angama our special mummy.
Nuna shi tayi da yatsa tana murmushi ta shige ciki.

"That's why i luv u too much aunty, kina da kirki ga hankali da natsuwa, Abba yayi dacen mata yanzu, Allah yaji qan ummanmu da rahama yabata aljanna mad'aukakiya.

"Amin bros. Haydar ya amsa mishi.
Juyowa yayi ya rungume d'an uwan nashi sai kuma ya saki kuka mara sauti.

Bubbuga bayanshi Haydar yakeyi asannu kuma yanayi mishi magana qasa qasa da alama haquri yake bashi.

*mrs j moon*
[1/12, 11:27 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*28*

Parking sukayi a daf da bakin get, Hameed ya fito yayi nocking, get man ya lek'o yana tamabayar waye?

"Baba barka da hantsi, yace dashi "barka kadai samari, wakake nema? "Mai gidan, dafatan yana nan? "Eh, yana ciki, bari nayi mishi magana, "ohk nagode baba, "bakomi yaro, amma ace wane ke nemanshi? "Kace jikanshi ne "to jirani a nan.

Tare suka iso wurin Abbaie, yana ganinsu yaga ne ko daga ina suke, cikin fara'a ya miqa misu hannu tare da sallama duk suka noqe kansu qasa suka ce atare "munsameka lafiya? "Lafiya lau, ku shigo ciki man, kwa tsaya awaje kamar baqi.

Bayanshi suka biyo suna qus qus, "yana da kirki kamar aunty Hindu, "to suda sarkin zance kasoma ba "ya haydar zan zarema halina fa yanzu kada kaga wai munzo baqunta tam.
Banza Haydar yayi mishi, ya qara sauri ya cimma Abbie suka jera, harara Hameed yabi kyeyarshi da shi sannan ya qara da d'an gudu ya cimmasu.

Tana kwance bisa doguwa kujera face d'inta yana kallon ceiling idanunta lumshe kamar mai barci.

Sallamar su Abbie yayi daidai ya saukan wani dum!! Sataji a qirjinta ta dafe wuri tare da furta "washh Allah, awahale ta amsawa su Abbie sallamar, ganin su Hameed atare dashi yasa ta miqe zaune da sauri tana neman inda hularta ta fad'a.

Kamar mara gaskiya ta zame ta gaishesu tana wani matse jikinta wuri d'aya.

Hameed ne ya amsa mata yayin da Haydar yazuba mata idanu yanajin bugun zuciyarsa ta canja a cikin second.

Saukawar ummi daga upstairs yabawa Addawiyya damar tashi da sauri ta haye sama ta bace kamar walkiya, jinkina tayi da door tana kwama numfashi har lokacin hannayenta suna dafe da qirjinta "washh ni Rabi'atu mike faruwa dani? Karo na 3 kenan dana kejin haka da zaran na ganshi, oh Allah ka warwaremin abinda ke boye.

"Auta kina ina? "Gani ummi "to fito ki had'awa su Hameed abinci ki miqa musu "to ummi.

Sai da ta shaqe wani babban tire da abinci kala2, ta iso parlor n ta jera musu kan wani table mai d'an fad'i.

Tana gamawa ta d'ago ta dubi gefen da Hameed yake tace "Bissimillanku "tam mungode, ya amsa.

Ta gefen idanu ta kai dubanta inda Haydar yake, caraf suka had'a idanu, gabanta ya buga tayi sauri kauda kanta tana kiran sunar Allah a cikin ranta.

"Ke!! Tafi kisanja dress. Idanu ta zuba mishi quri, ya watsa mata harara "ko bakiji mi nace bane? Sauke kanta qasa tayi tare da juyawa tabar wurin batare datace dashi qalaba.

"Miye haka bros? Ko kamanta ita d'in ba khairi bace abin ikonta
ka?
Chapter 16 · 0% Book details