← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 38

Sashe 15

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Oh ina mishi murna zamowar shi doctor, Allah yasa nima wata rana naganni hakan kamarshi "Amin autan ummi.

"Yawwa Aunty H. Kinsan abinda yakawoni gidan nan kuwa? "A'a sai kin fad'a.
Qasa tayi da murya tace "makiran matarcan ta sato takardun qaddarorin Alhaji ta saka miki a cikin sip, anjima zaizo nema in bai ganiba sai tayi jagora zuwa part d'inki ayi bincike, don haka yanzu zan d'auka in miqashi zuwa part d'inta, ai intasan wata bata san wata ba.

Cike da tarin mamaki Hindu tace "autan ummi samuwarki alkhairi ce a rayuwarmu, godiya nakeyi miki mara adadi.
"Kada ki damu aunty H. Allah yana tare da mai gaskiya.

Gaba gad'i Addawiyya ta shiga parlorn hajiya Karima, bakowa ciki don haka direct ta wuce bedroom d'inta ta bud'e bedside drawer ta saka ta fito da sauri tabace kamar walqiya.

"Autan ummi mi hakan ke nufi? "So take uncle tsoho ya sakeki ki barmata gidan tacigaba da mulkinta don tace tunda kika zo komi ya lalace mata ta rasa gane kan mijinta.
"Ikon Allah sai kallo, to ta Allah ba nata ba,, zama daram a gidannan, "zancenki haqqun aunty.

Da yammacin ranar suna kitchen suna gabatar da girkin dare.
hayaniyar hajiya karima tayi musu sallama fad'i take "wallahi yau dubun barauniya yacika, dama don arzikinshi kika aureshi 'yar matsiyata, to kisani mu kam bazamu lamunci sata ba a irin wannan gidan mai cike da nagarta.

"Kimin shiru nace karima ko in saba miki, miye kikeyi haka? Alh. Muktar yace haka cikin qunar rai.

Tsaye su Addawiyya sukayi kirko2 suna kallon ta, zuwa can Alhaji yace "Hindu wasu takardu nake nema bangani ba shine nace ko kin gansu?
A'a Alhaji bangansu ba sam "qarya takeyi ita ta sace don haka dole abincika ko ina na cikin d'akinta.

Wani kallo Addawiyya ta doka mata tana girgiza kai tare da cije labba.

"Ke uwarki kikewa wannan kallon? Tace da Addawiyya.
"A'a inamawa marka ce matar basharu.

A fusace tayo kan Addawiyya Alhaji ya tareta "ke!! Banson sokarci anan wurin, inace tambayarta kikayi ta kuma baki amsa?

Cikin kuka hajiya karima tace "su malam fa ta kira sunarsu, sunacan kwance cikin qabarinsu ta tashesu.

Kallo mamaki Alhaji ya saukewa Addawiyya, zaiyi magna tariga shi "a'a Abba nikam bansan sunar iyayenta nakiraba, sunar zuwamin yayi kawai abaki amma ni banma san wasu masu suna hakan ba.

Jinjina kai Alhaji yayi yace "to kindaiji badasu takeyi ba don haka sai ki kama mana baki haka nan, kina bareshi kamar anyaga faranti.

Ga dariya amma ba halin yinshi.

Tana hararan Addawiyya tace "To naji, amma sai anyi binciken nan angano barawo yau, "karima fice kibani wuri tun ban saba miki ba.

Hindu tayi saurin cewa "Azo ayi binciken Alhaji ko za agano mai halin beran.

"Dear baza'ayiba nace, kaya dai nawane to bakomi kowa ya d'auka nauyi yaragemin.

Afusace hajiya karima ta fad'a bedroom d'in Hindu tana masifa, "ai wallahi sai naduba haka kawai acucemu inaji ina gani taf bazai sabuba kam.

Alhaji zai bita Hindu ta riqeshi tana girgiza mishi kai, akan dole yaja ya tsaya amma ranshi inyayi dubu ya baci.

Tsawon 15 minutes karima tana bincike amma bataga komai ba hankalinta yayi mugun tashi. ayyanawa take cikin ranta 'anya kuwa khairi ta kawo file d'akin nan kuwa?

"Malama kifito mata a d'aki hakan nan tun kafin ranki ya baci, jiki ba lakka ta fito, her face was dripping with weat, sai sharcewa takeyi da hanunta, tawani maqure gefe tana zare idanu narashin gaskiya.

Kallo 1 Alhji yayi mata ya kauda kai yace "Allah ya shiryaki karima, Allah yasa kibar qage arayuwarki.

Da qarfi Addawiyya ta amsa "Aminn Abba.

Taja jiki asanyaye zatabar parlor Addawiyya tace"Abba aje abincika part dinta itama mugani ko yana can "ohk je ki duba Rabi'a, kuma kibincika dakyau "angama Abba.

Hajiya karima tasoma masifa ita tafi qarfin sata don haka ba wanda zai yamutsa mata d'aki.

"Ai kam baki isaba madam, yarda kika bincika na wata to kema sai anduba naki, kuma ni da kaina zan jagoranta don haka ke yarinya zo muje.
Abdul Hameed ne yake cewa haka donmin tun farkon dramar yana tsaye abakin qofa yana kallo.

"Alhaji karabani da d'anka tun kafin in d'au mataki akanshi, tace cikin hargagi.

Bai kula taba yace "Abdul kuje kuduba, ke kuma karima dawo ki zauna har su dawo, zatayi magana ya daka mata wani tsawa bashiri ta dawo ta zube bisa kujera tana faman hararan Hindu.

Acikin 5 minutes suka dawo d'auke da file suka miqawa Alhaji.

Tuni hajiya karima tasoma rantsuwa tana hawaye, wai baki suka had'a suka qulla mata sharri.

Kad'a kansa kawai Alhaji muktar yayi tare da ficewa zuwa part d'insa batare da yace komi ba, Abdul hameed yamara mishi baya.

Addawiyya ta dubi hajiya Karima ta sheqe da dariya tace "inzaka gina ramin mungunta to ginashi kad'an don gudun wata rana zai iya zurmawa da kai ciki, ta qara kwashewa da dariya.

"Dani kikeyin zancen yarinya, zakiga yarda zan maidake "uhmm hajjaju ma abociyan sabon Allah, to ki rubuta ki ajiye ni Addawiyya badai mutum ba sai dai Allah, kuma kisani ni da kaina na kai miki file d'in d'akinki kamar yarda kika turo fingilallaliyar 'yarki ta kawo nan, don haka ina baki shawara kada kibari kicigaba shege kafasa.

Cike da fusata Hajiya Karima ta kawo mata wani mari taji anriqe mata hannu gam koda ta juyo tayi arba da Haydar yayi mugun had'e rai, cikin kakkauran voice yace "fice da arzi ko in baki mamaki.
Kafin kace me tafice har tana tumtube, sabida sosai take shakkan Haydar fiye da kowa agidan hatta Alhajin kuwa.

"Aunty please kidaina biyewa sokuwan matan nan kuna fad'a kinji? "Insha Allahu zan kiyaye Haydar "madallah, ya juya yafice baiko duba inda Addawiyya take ba.

Gaban ta yariqa bugawa fat!! fat!!, asannu ta zame jikinta tashige room tana maijin wani yanayi wanda tarasa gano ko miye shi.

Da dare suna cin abinci, Addawiyya tace da Hindu "aunty H. Matar can fa tayi mugun tsorata da ni, bazata qara marmarin qulla miki sharri ba "uhmm autan ummi wallahi lamarin matar nan yasoma isata, amma yanzu nayanke shawara nabar sakeyi mata shiru balle ta zaci tsoronta nakeji.

"yawwa aunty, gara kiriqa zare musu ita da 'yarta "kedai bari ai komi yazo qarshe, zasu sha mamaki na.

Wshe gari tana part d'in hajja suna hiransu cikin nushad'i ita da hajja, khairi ta shigo bako sallama, ta dage ta dallawa Addawiyya mari, ko kafin ta sauke hannunta Addawiyya ta maida mata da martani kuma bata tsaya a 1 ba a'a cigaba tayi da dalla mata zafafan maruka, Abdul Hameed yana tsaye yana irgawa har sai da tayi mata hawa 12 kwarara sanan ta dakata.

Tuni khairi da zube tana tsala ihu, face d'inta kuwa har ya kumbura.

A. Hameed yasoma dariya har da riqe ciki, yace "very good beauty, take my phone as a gift, ya tako ya ya fidda sim da m.card d'insa ya d'ora mata phone d'in ajikinta, tabi wayar da kallo taga Apple ce ash calour, ta d'ago tana kallonshi ya sakar mata murmushi yana yi mata jinjina da hannu, ya d'ora da cewa"najima ina son ganin wanda zai cimin uwar shegiyan yarinyan nan sai yau Allah ya kawoki don haka tashi ma yanzu muje shopping domin jindad'in abinda kikayi jiya da yau dole in karramaki ainun.

"Gidanku nace Hameedu, hajja tace dashi tare da yi masa daquwa, ta kuma cewa "amma kai kam anyi wofi mara raba fad'a sai zigawa.

Dariya ya saki tare da janyo hannun Addawiyya yace "oyo come on beauty mubarwa wannan old woman d'in matsuguninta taci tsiyarta ita 1.
"Qaniyar kace zataci tsiyarta ba ni ba, yana dariya suka barmara d'akin.

Kamar doluwa Addawiyya tabiyo bayanshi, suna shiga part d'in Hindu sukayi kicibis da Haydar.

Wani fad'uwan gaba ya kawowa Addawiyya ziyaran bazata, tayi sauri dafe qirjinta tana kwama numfashi, "wash ta furta ahankali.

"Kai dai bakajin magana ko? "To minayi kuma uban yan sa ido? "Hameed wallahi zancima qaniya fa, inbanda iskanci kasan kana da aiki a hospital amma tazo gida ka rashe sannan kuma ka kashe wayarka don tsaban rainin wayau.

Sai da yashafi sumar kansa yana dariya ya amsa "to second Abbana ayimin affuwa bazan sake ba oga Ali gadanga qusar yaqi.

Dukan wasa ya kaiwa kad'an Hameed tare da ja mishi kunni, sannan ya wuce yana murmushi.

Da sauri ya juya zai bishi tayi hanzarin tura mishi phone d'insa a aljihun wandonsa ta baya ta ruga ciki da gudu.
Dariya ya saki kad'an ya furta "zanzo miki da sabuwa dal anjima beauty.

"Aunty yana da kyau sosai harma yafi Hameed kyau amma dai suna mugun kama da juna kamar 'yan biyu.
"Eh sosai suke kama da juna kuma Aliyu haydar shi ne babba da Abdul Hameed.

"Taf ai kam Hameed yafishi jikin girma sosai "ko, autan ummi? "Eh, Allah yafishi har tsawo, shi dai haskene kad'an zai nuna mishi "to kodai kina ciki ne? Oya fad'amin wane ne gwanin naki cikinsu?

Dafe kanta tayi kamar zatayi kuka tace "Wayyo aunty H. Amma Kingama dani wallahi.
Dariya Hindu tasaka mata tana shirin yin magana suka tsinkayi hayaniyar hajiya karima, "tofa ni Hindu nashiga uku!!!! "Kai aunty H. Kina bada mata wallahi.

"Ina kike? gayyar tsiya mai siffan aljannu Wallahi yau ko ni ko ku, zanga uban da ya d'aure muku gindi a gidannan da har zaki kusa sumarmin da 'ya don kawai tazo shashin kakanta.

Kalllon tuhuma Hindu ta saukewa Addawiyya, tayi saurin sauke kanta qasa tana motsa yatsun hannunta tana kuma dariya qasa2.

*mrs j moon*
[1/11, 4:47 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*27*

Kunninta ta kama ta matse da kyau "oya fad'amin mi kikayiwa 'yar muta ne?
Kukan shagwaba Addawiyya ta saki har da hawaye, da sauri hindu ta sakar mata kunni, tana cewa "ayya sorry qanwata da zafi ko? "Eh aunty "to affuwan kinji? "Uhm! Uhm!! Ni bakimkin komiba "ina sonki autan ummi "nima ina sonki sosai aunty H. Uwar ta gari.

"Ja'iran banza to waye ba ta gari ba? ceqar hajiya karima wacce ta kaicinsu tuni yagama cikata ji take kamar ta bisu da duka.
Chapter 15 · 0% Book details