← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 38

Sashe 1

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[12/29/2017, 2:59 PM] Asma'u Seema1: 🙊
*RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
*SAFIYYA (mrs j moon)*

*1 ~2*

Gudu take zubawa irin na ceton rai bata ko duba inda take jefa qafafunta ita dai burinta tasami wurin tsira daga sharrin azzalumai, arba tayi da wani sark'aqiya na bishiyar tsamiya aiko take ta kutsa kai ciki sark'aqiyar batare da tunanin komi ba, duk sukan da k'ayoyi da suke mata bataji ita dai burinta tasami wurin buya yarda baza su ganta ba ballan tana su yagamata martabarta, da kyar ta sami ta shige. Abin mamaki sai ta sami wurin da fili sosai gashi kamar anshare domin tas tas yake, sai dai uban sanyi wurin kamar k'anqara. Zama tayi tana maida numfashi tare da tunanin maganganun da umminta tafada mata fashewa tayi da kuka tana cewa "ummi kiyafemin kinfini sanin abinda zai amfaneni amma nasa k'afa nayi fatali da maganarki nayi wutowata batare da saninki ba gashinan za akuma maimaita abinda yafaru da adda Salma,, wayyo ni Addawiyya nakawo kaina ga halaka.... nishin da taji ne kamar na mutum yasa ta d'auke kukanta tasoma zare idanu tana waige waige bataga komi ba saita gyara zamanta tajingina jikin wani abu mai taushi tare da d'an uban sanyi. Wani zabura tayi tana bin abinda ta jingina dashi da kallo. Arbatayi da wata murd'ed'iyar micijiya ta nad'e jikinta kamar tayan babban mota ta zuro kanta tsakanin circle d'in datayima jikinta ta kafe Addawiyya da idanunta masu tsananin haske kamar tough light.
Addawiyya wacce tuni tasaki fitsari a wando tasoma ja da baya mucijiyan tayi wani girgiza iska mai tsananin k'arfi yatashi wanda saida yad'aga Addawiyya sama ya dawo da ita k'asa ya watsar,, tamik'e agigice tana neman hanyar fita daga sark'aqiya tsamiyar mucijiyar ta saki wani uban qara ta nufota bakinta bud'e zata had'iyeta........ razanannniyar ihu ta saka wanda yasa ummi tare da salma suka shigo d'akin datake.
Gumi take had'awa sai kace wacce ta fito wanka sabida zufa takeyi kamar ta watsa ruwa.

"Lafiya kike Rabi'atu? Shiru ba amsa sai zare idanu takeyi tana gwama numfashi.
Tsaki Salma taja tare da fad'in "ummi iskancinta ne ya motsa kawai. Harara ummi ta sakarwa Salma ta maida hankakinta wurin Addawiyya ta matsa tare da dafa kafad'unta tace "autan ummi mike faruwa? Quri tayima ummin da idanu tana son tuno mufarkin da tayi amma takasa tuno komi illah hasken idanun macijiyan da har yanzu yake mata hizo afuska.

"Ko mufarki kikayi mara kyau? Ahankakili ta gyad'a kanta alamar eh.
"To shine bazaki farka da du'a,iba sai da ihu? Cikin rawar murya tace "nakasa ne ummi.
"Kingani ba, taya zaki tuna addu'a alhakin kin kwanta barci a irin wannan lokacin mai tattare da hatsari. Nasha tunasar dake barci yaban sallar ka'asar abu ne mara kyau, domin ko marasa lafiya wanda basa iya tashi tadasu akeji a jinginar dasu har akira magrib sabida masana sirrin barci sunce yana haifar da mutuwar fuji'a haka kuma junnu suna iya shiga jikin bil'adam a irin lokacin sannan manzon Allah S.A.W. yayi hani da barci bayan sallar la'asar domin yana gadar da bak'in ciki haka na bayan subahi kafin fitowar alfijir tare dana tsakiyar rana su kuma barcin asarane don haka sai ki kiyaye barci alokutan.
Kai ta gyad'a tana jan hanci wanda majina yake barazanar zubowa sabida sanyin da ta shak'a amufarkin da alama ya saukar mata da mura. Kuma abin mamaki jikinta ajiqe alamun fitsari tayi, tana wanka tana mamakin wannan kalan lamari mai figitarwa.

Bayan sallar magarib Addawiyya ce zaune tatasa touch light sabon zubi a gabanta tana yanke farcenta tare da k'anqaresu, Zuciyanta cumkushe yake da tunanin mufarkin da tayi wanda har lokacin takasa tunano ya yake amma idanun macijiyan nan yaqi bace mata.

Afusace ta iso wurin ta d'auke touch light d'in tayi gaba zuwa wurin garken shanu. Da gudu Addawiyya tabi bayanta tana fad'in "Allah baki isaba, insama kayana batur shine zakizo ki d'auke alhalin kina ganin aiki nake da shi.
Aiko tana cinmata suka soma dambe tuni Salma ta danne Addawiyya ta matse mata baki don kada tayi ihu Abbi ya jiyosu. Abinda basu sani ba duk Abinda sukeyi Abbi yana tsaye agefe yana kallonsu, ganin abinnasu bana k'are bane yasa ya iso ya d'aga salma ya dalla mata mari ta tsala ihu ta arce da gudu yayin da Addawiyya tasoma bashi hakuri itama mik'ar da ita yayi ya falla mata mari tare da jan hannunta zuwa rumfar da suke cin abinci. Fad'a yayi musu sosai sunata bashi hakuri.

"Adda Salma yau muje rafin cigogo muyi kallon wasan iyo man, "bazanje ko inaba ni, "ummm kai Adda keko muje mugana na bankwana man, kinga ashekara su 1 akeyi kuma ina son sake ganin rafin sabida na dade ban gantaba gashi nan da kwana uku zan koma school ke kuma ki koma kwantagora.
"Ke Allah zan makeki yanzu inbaki bacemin da gani ba, wato so kike inje suyi ta kallona suna cemin fanko ko? "A'a adda banufina kenan ba, amma tunda kince haka to abar zancen.

****** Rafin cigogo ruwane mai fad'i da tsawo gashi da burgewa tare da d'aukan hankali. masinta sunayin su awurin lokaci zuwa lokaci amma fa rafin tana da had'ari musanman ayayin gabatar da wasan iyo na shekara shekara domin duk lokacin da akazo aiwatar da wasan to tana cin mutane a qalla mutum biyu zuwa uku amma duk da wannan had'arin baisa mutanen qauyen Jangab'a sun daina wasan ba, sabida sun d'aukeshi a wani al'ada mai mahinmanci.

Yau ake wasan iyon wasan ruwan na zagayowar shekara,, bakin ruwan cike yake da mutane jinsin fulani kad'o, kanbari tare da dikkawa mazauna yankin da kuma masu zuwa kallo amma junsin fulani sunfi yawa sabida ayankinsu rafin take kuma sune suke gabatar da wasan tare da wasu 'yan k'alilan na sauran qabilun. Inda duk wanda yazo na 1 zai zabi budurwan dayakeso a cikin jinsunsu ya nufi daji da ita wai zai cire mata kashin mundirik'i, kuma bawanda ya isa ya hanashi hatta da iyayensu domin wurin yana samun halartan sarakunan yankunan tare da iyayen da matasa harm da yara qanana.
Shiyasa yara mata basa zuwa wurin indai da sanin iyayensu.

Wasa yayi wasa bakajin komi sai ihu da sowar mutane. and'auki kimanin awanni biyu ana gabatar da wasan tseren ruwan amma bawanda yazamo zakara sabida zakarun ana samun mutane sama da goma wand'anda suke kai bakin gaba atare. acikinsu aka fidda mutane bakwai domin su fafata suma atare suke kai bakin ruwan ganin haka sai aka soma yin mutane 2~2 wanda yariga kaiwa sai yakoma gefe ahaka aka sami mutane hud'u suka fafata ananma aka sami mutun 2 sukayi bracket sai suka koma domin asamu zakara komawarsu ke da wuya aka hango wata qatuwar kada tayi kasan ruwa dasu sai sowa ya koma kuka aka tura masana ruwa su dubosu suma acikin mutane biyar mutun 1 ya tsira ya fito yana cewa "ba aljannun da muka sani bane aruwan bana wasune kuma mugayene don haka kowa yayi ta kanshi domin yasu ambaliyan ruwa yanzu, aiko yana gama rufe bakinshi ruwa yasoma toro yana malala zuwa cikin mutane, tsere aka soma ana fad'uwa cikin masu fad'uwan kuwa har da Addawiyya da Salma wad'anda suke labe awata bishiya suna kallon wasan.

Sunacin tuwan dare suna hira k'asa k'asa gudun kada iyayensu suji "amma wallahi ke kam Addiy 'yar buhu ce, "to minayi kuma adda? "A'a kin manta wuk'a ce ba Adda ba, kinsan Allah nakumajin kin kirani da Adda sai na fashe miki baki na zubda miki da haqora. Ja da baya Addawiyya tayi tace "nima kidaina cemin Addiy in kuma kink'i sai na jefaki arafin cigogo wannan kadar ta cinyeki tare da baqin mucijin nan na rijiyan kugu kuma nace Adda adda adda lolo.
Afusace Salma tayi kanta ta kwasa da gudu tana dariya tayi cikin garken shanu bata ko tsoron dare ga duhun damina.

Ganin haka Salma ta dawo tacigaba da cin tuwonta. Ita kam Addawiyya zama tayi agefen wata bishiyar tumfafiya ta kankwashe k'afafunta kamar mai d'aukan darasi, sai gyad'a kai takeyi tana murmushi. Motsin mutum taji kusa da ita tatashi da sauri ta shige cikin shanu ta sulale tafice zuwa d'akinsu.
Tana kwanciya Abbi ya shigo yayi shiru yana kallonta sai kuma ya fice bayan ya tofesu sa Addi'o,i

*mrs j moon*
[12/29/2017, 2:59 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA

*This page is for you Sadia lawal bala, Allah yakaimu ranar bikinki muzo kt mu kwashi rawar d'aga buje😅 inaji dake sosai a ruhina 'yan matan kwarni.*😘

*3~4*

Misalin k'arfe 8:30am.
Zaune suke a wani bukka wanda yazamo wurin cin abincinsu ako da yaushe. Yanzuma karyawa sukeyi cike da jin dad'i.
Ko rafin shan tea d'in Addawiyya batayiba ta mik'e tafice bata jima ba ta dawo hannunta riqe da kwaryan madarar shanu tazo ta zauna tasoma sha har ta shanye tas sannan ta dubi Salma wacce take da tura bread tare da k'osai sannan tabi da ruwan tea. Dariya ta saki tana nuna Salma da yatsa, "amma Adda kina harkan 'yan k'auye fa, diba yarda kike ta tura abinci kamar kwancen hauka, kai Allah kinada matsala ta rashin iya cin abinci cikin natsuwa.

Wani mari Salma ta kawo mata ummi ta riqe hannuta tana hararanta tace "amma wai Salma bana hanaki biyewa Rabi'a ba? "To ummi kinajifa tana cemin mara natsuwa don kawai ina bawa tymmyna hakkinshi, ko tana tunanin kowama irinta ne wanda bai kula da cikinsa.

"Uhmm inajinta, nadaice ki kyaleta ki daure kina rik'e girmanki, waishin injin ko kin manta shekaru biyar da wata biyu kika bata ne? "Ban manta ba ummi "to daga yau duk abinda tayi miki ki fad'amin zakiga yarda zanyi da ita "tam ummi, Allah yasa ki iya hutamin ita tan.

Dariya Abbi yasa sanda yaji k'arshen zancen Salma yace "aikam gara da kikace hakan domin zuwaira da 'yar autanta kam sai Allah.
Chapter 1 · 0% Book details