← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 38

Sashe 26

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To pa!! Sunarta kenan? "Eh "to wai uncle ita d'in tafi qarfinka ne dabaza karabani da ita ba?
"A'a bata isheni komai ba sai dai kisani komi na duniya yana da iyaka inkin cire ikon Allah shikad'ai ne wanzajje bawanda yasan qarshensa sai shi kad'ai. "Hak ne kam "to don haka iyakar ce bai zoba amma Allah yabani iko nayi miki katanga da ita tayarda koda tazo domin cutar dake baza ta iya yi miki komi ba "tam nagode uncle sosai.
"Bakomi mai babban suna.

"Sai kuma ina so ki kula da Ali sosai ki maidashi tamkar yaron da yake buqatar kulawa, kiyi haquri da halin dazaki riskeshi ciki, shine jarabawar rayuwar dana taba fad'a miki zai riskeku amma in kinyi haquri zai wuce kamar ba'ayiba.

"Tam uncle Allah yabamu ikon cinye jarabawar.
Ya amsa "Amin.
Zata kuma yin magana ta tsinkayi muryan khairi agefenta inda ta kai mata duka tana cewa "kefa wata kalan mutumce ayi ta nemanki arasa sai kace wacce taci eggs d'in makwarwa.

Kallon uncle tayi, ya sakar murmushi yace "itama ta kusa aure ita da d'an uwarta hameed za'asha bikinsu bada jimawa ba.

Dariya ta saki tana kallon khairi, sai kuma tamiqe tayi gaba ta juyo tace "bye, gyada mata kai yayi tare da bacewa.

Khairi ta waiga taga bataga kowa ba tace "kefa aljana ce inaga, ke da qaye kike bye.
"dake nakeyi koba ki fahimci narigaki barin wurin ba ne? "eh haka ne "yawwa yarinyata, duka ta kawo mata ta gofce tana cewa "hattara dai yarinya domin Amarya dai tsautsayi gareta, ki lallabani ko yanzu in sume miki.

"Duka takuma kawo mata tace "oya mace man man, kuma Allah haka nan zamu kaiwa ya Haydar ya more sadakinshi.

'Yar buhu kawai, banza wanda batsa yayiwa zubar 'ya'yan kanya a baki kawai.

Dariya khairi tasa sosai ta amsa "naji dai, kuma zuwa jibi kamar yanzu wata yarinya tagama zama ragowa.

Afusace takaima bakin khairi duka takauce tare da fallawa da gudu tana dariya.

Murmushi tayi ta furta "uhmm drama kenan ni Addawiyya a bed d'in aure, sai tasoma kyalkyala dariya, ahaka Hindu ta sameta ta janyo hannunta ta suka fito zuwa d'akin Abbie.
Daf dazasu shiga tace da ita "hala uncle d'inki ne yazo miki sallama yasakaki wannan dariyan kikayi tayi kamar sabuwar kamun almatsutsai?

Qince mata komi tayi har suka shige parlor n d'auke da sallama, gaban Abbansu ta kaita ta zaunar ita kuma ta dawo gefen ummie ta zauna.

Nahisa sosai Abba yayi mata sannan Abbie ya d'ora da tasa, mama tayi irin nata, ummie tayi kai hatta da Salma saida ta tsoma baki kuma sosai tayi magana mai cike da natsuwa da shiga jiki.

Addawiyya sai kuka takeyi, tanajin wani irin kewa yana shigarta.

Ana idar da sallar magrib motocin d'aukan Amarya suka soma layi wanda dukka daga abokan Ango ne suke.

Tana kuka kamar ranta zaifita mama ta sakata a cikin motar Hameed tare da babban qawarta Maryam wacce itama kukan take tayi kamar itace Amaryan.

Part d'in Hajiya karima aka fara kaita.
Tana jinsu taqi fitowa har suka gaji Hindu tace "sufito su tafi ai anfita hakkinta.

Suna fita khairi ta fad'a bedroom d'in nata cikin kuka take fad'i take "ni kika wulaqanta momy ba kowaba, masifa ta rufeta dashi wanda yasa dole tafice bashiri domin taga inta tsaya zata bata na gidan bread.

A part d'in Hajja sun sami tarba mai kyau inda tanemi da Abar mata ita da kanta zata sadata da d'akin mijinta, atakeko suka barta suka koma akabarta tare da qawayenta.

Misalin tara saura Hajja ta umurceta data shiga wanka, ruwan zalla turare irin tasu na kanuri tazuba mata acikin ruwan wankar, bayan ta fito ta zuba mata wani na tsugun.
Cike da kunya ta tsuguna, wani d'an ubansun swiss lace ta fito mata dashi bayan ta sata ta mulke jikinta da had'in su humra da kulacca.

Koda tafito wurin su maryam duk miqewa sukayi suna yaba kyawunta Hajja tayi ta fad'in Tubarkallah masha Allah.

Suna shirin kaita part d'inta Hameed ya shigo afujanjan.
"Kai lafiya kuwa? Hajja ta tambayeshi cike da rud'ani.

Dariya yasoma batare da ya amsata ba ya nufi inda Addawiyya take ya kai hannu zai kamata ta noqe, Hajja ta qaraso wurin ta dima mishi duka abaya ya ja baya yana fad'in "Kai hajja mugunta dai bai da kyau, kuma zuwa nayi na d'auki Amaryanmu lokacin zuwa dinner zai qure.
Cikin fad'a Hajja ta amsa "Uban dinner za'a nace, ficemin dagani ko yanzu ranka yabaci.

"Hajja don girman Allah kada kiyi mana haka, kibani ita kada ayi ta jiranmu.
"Hameed kaficemin anan ko ranka ya baci, dinner banza da wofi, to bata zuwa ko qofa ta kashi kaji dai na fad'a maka.

Cike dajin haushi ya fice, ta dubi 'yanmatan tace "irin wannan bidi'ar yake kwashe karamar aure don haka sai ku kiyaye habbaka shi.

Suka amsa da "to cike da yabawa hangen nesa irin na tsohuwar.

A ta qaice dai a part d'in Hajja suka kwana duk don kada ta kaita atafi dinner aboye.

Da yamacin ranar akayi bud'an kai inda Alhaji muktar ya mallaka mata wani gidan hayarsa mai d'auke da parts shiga.

Wayyo zo kuga yarda hankalin h. Karima yatashi, khairice tayi ta lallabata kada taraba abin fad'a qarshema sai tajata kawai suka bar wurin, tana mai cike da qunar rai agame da d'abi'ar mahaifiyarta.

Taro yawatse lafiya qawayenta duk sun tafi sai maryam tare da khairi kawai suka rage.
Qara gyara gidan sukayi, ya d'auki qamshi.
Salma tashigo ta shiryata cikin wata koriyan atamfa mai tsad'a da kyau, ta kuma amsheta sosai d'inkin yayi mata cif2 ajiki, ta yafa gyale kalar atamfar, tafesheta da perfumes masu taushin qamshi.

A gefen gado ta zaunar da ita tace "jirani inzo yanzu my Addawiy, gyad'a mata akai tayi.

Maganganun isowar abokan Ango ya ankarad da ita wayau Salma tayi mata, gudu su kayi suka barta, atake idanunta suka kawo ruwa alokaci d'aya kuma taji gabanta ya bada sound dam!!!

Murd'a handle d'in yayi tare da sallama, can qasar maqoshi ta amsa, tsaye yayi yana qare mata kallo zuwa can ya tako a sannu ya yaye gyalen data rufe fuskanta dashi ya d'ago kanta, tayi saurin kulle eyes hawayen dasuka maqale suka zubo ya sunya sosai ya zaro harshenshi ya lashesu.
Cikin hanzari ta bud'e idanun ya sakar mata murmushi tare da furta "shine cikar so da qauna.
Kayda fuskanta tayi gefe, ya juyo dashi tare da miqar da ita ya gyara mata zaman gyalen sosai ya rufe mata jiki sannan yaja hannuta suka fito parlor inda abokananshi suke jiransu.

nasiha tare da addu'o,i sukayi musu sannan syka ajiye mata kayan siyan baki kamar dai yarda al'adar mafi aka sarin hausa fulani yake.

Sunagama fita ya kulle qofar parlon ya dawo ya cimmata inda yabarta.
Zama yayi a gabanta samar carpet ya zuba tagumi yana aikin kallonta.
Tura baki tayi tare da sakar mishi hararan love tace "miye kuma? "Uhmm uhmm qaunar kice ce zata maidani kurma.
Bata san sanda dariya ta kufce mata ba ganin yarda ya kwaikwayi voice d'in mata.
"Masha Allah ya furta da qarfi tare da d'agata cak kamar baby, bai sauketa ko ina ba sai cikin bathroom, yace "oya muyi arolla sai muyi sallah domin nuna godiyarmu ga Allah.

Bayan sun idar da sallah ya d'au ledar da suka shigo dashi yace "bismillah, girgiza kai tayi alamar ta qoshi. Ture ledar gefe yayi ya miqe yashiga wanka bai jimaba yafito yazo ya zauna gabanta yace "ehem fara aikin ladarki tun yanzu,kallon qari batani tabishi da shi, ya miqa mara cream "shamamin zakiyi, kauda fuska tayi gefe, ahankali tace "niban iyayiwa gato shafa ba, "yau zaki koya zuwa gobe kisoma da koyon yarda ake wanke gato.

Ganin da gaske yakeyi yasa ta marairaice fuska takoma kalan tausayi tace "ya Ali nidai kazo kaci abinci tukunna "in har baza kiciba nima na haqura, shiru tayi tana kallonshi.

"Mai babban suna tun safe baici komi ba don haka ki lallabashi yaci.
Haran gefen da sautin yafito tayi, murmushi mai sauti yaka saki tare da cewa "affuwan Amarsu ta ango yanzu zan wuce dama sallan godiya ga Allah na tsaya binku jam'i amma ba burina naga sirrin kuba.

Da sauri tasoke kanta qasa cike dajin kunyar qarshen Ancen shi.
"Asuba tagari mai babban suna, motsa bakinta tayi alamar amsawa sai kuma ta juyo wurin Haydar taga har yagama shafanshi ya sanya night wear, turare yake fesawa.

Tashi tayi ta d'auko plate ta juye kazar ta zuba fresh milk a cup tazo gabanshi tasoma bashi abaki saida ya qoshi sanna yabata taci kad'an tace taqoshi.

Miqewa tayi tashiga toilet, yabita da kallon tausayi, gamace har mace amma lafiyar mijinta sai a slow, abinda yake ayyanwa a zuciyarshi kenan.

Kansa bisa qirjinta yake wasa yakeyi da sumarta, sai hira yake mata kad'an kad'an ita kam gabanta sai bugawa yakeyi sam bata fahimtar inda hiran nashi ta dosa.

Cire kanshi yayi a bisa qirjinta ya kwance zaren gaban riganta ya tura hannunshi ciki ta rutse idanu, yace "mi yasa gabanki yake beating haka? Tak'i cewa komi, sai da yakuma tambayarta ta amsa ahankali "bakomi barci nakeji kawai, shafa fuskanta yayi ya kai bakinsa daf da ear d'inta yasoma hura mata iska yana mai furta "yi barcinki my life, "uhmm uhmm to kabar huramin iska nan zata iya hanani barci "ohk na bari, ya rumgumeta tsam tsam yana ceqa muyi addu'ar shiga barci tukunna, suna shafawa ya kuma cewa "to asuba tagari kayan Haydar, murmushi tayi tare da kulle idanunta.

ASUBA TA GARI ADDHAY😍

*Mrs j moon*
[1/24, 9:09 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*39*

Qamk'ameshi tayi sosai, ita kuma sai qoqarin rabasu takeyi tsawon lokaci takasa yin nasara akansu sai ta ja baya ta koma kura bakinta yana fidda wuta ta nufosu ko kafin ta iso iska yazo yayi sama dasu tabisu ta gudu haka sukayi ta keta dazuka kamar walkiya tana biye dasu cikin siffarta na kura awani fili mai yawan itatuwa iskan ta saukesu, ita kuma kuran tuni hasken wurin yasa ta daina gani sai juye juye takeyi tana tsala ihu mai firgitarwa, zuwa can tabace bat.
Chapter 26 · 0% Book details