Sashe 11
Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar dana cika kwanaki hud'u daganin ta tana tsafi, awani yammaci mundawo d'ibo ruwa afamfo naganta dif agabana tana wani murmushi wanda na fassarashi dana mugunta, a'uziyya naja mata da sauri tare da soma addu'a a cikin raina,, wani mugun tsaki taja ta bangajeni ta wuce su Alawiyya suka bita da kallo cike da tsana domin bata da farin jini sam a school din.
ni kam gaba nayi ina tunanin mi hakan ke nufi.
Adaren ranar ta zomin cikin barcina, wannan karon so take ta kasheni domin tsafka take kawomin awuya ina gofcewa tare da tofa mata ayar Allah, mun jigata ni da ita har tagaji ta bace ni kuma na farka zufa yajiqamin jiki, nayita mamakin lamarin, to tundaga nan tahani sukuni abarcina sosai take son illatani Allah yana kareni.
A daren shekaranjiya mukayi dambe nayi ta d'agata ina bugawa da qasa nakuma gargad'eta da ta kuma zuwamin cikin barci sai na kasheta na juya domin tafiya shine ta zama min zaki tasa farce ta ya kusheni a gefen cikina ko kafin in kamata ta bace tanamin dariya to da na farka sai naga da gaske tajimin ciwo kuma yana min zafi sosai amma naqi nunawa kowa har kukazo tafiya dani.
sanda mommy Abida ta jani zuwa wurin bishiya nan shine nake fad'a musu abinda ke faruwa kuma haka sanda na farka amota afirgice ita ce nagani tanamin dariya wai nakusa zama gawa domin itace zata tsotse min jini, kuma sanda nake kiran sunarta kafin mu isa hospital ita nake gani tana son tara k'ok'o a jinin dake zuba ajikina amma ta kasa sabida da ta matso kusa dani sai ta koma da baya tana qara kamar taga wuta.
Shiru kowa yayi cike da tsoron lamarin sanda Addawiyya takawo qarshen labarin.
zuwa can mama tace "Allah yaqara tsare mana ke, suka Amsa da "Amin.
Salma tace "amma ya barcin ki najiya ya kasance? Shin ta kuma zuwa miki ko ya? "A'a banganta ba hasalima inaga banyi mufarkin komiba jiya sai na wata asararin smaniya yayi haske sosai har yana kashemin idanu.
Abba yace "Alhamdulilla, alamu yanuna kinfi qarfinta kenan amma duk da haka za'aneman miki maganin kariya daga miyaqu.
"Ai dukka gidan za'anemawa domin riga kafi yafi magani, cewar ummi.
Haka dai sukayi ta tattauna zancen tsawon wani lokaci kafin iyayen su tashi suka bar yaran suna cigaba da maida zancen.
Su Abbi basu bar kwantagora ba sai da sukacika sati 1 da zuwa sabida maganar auren Salma da Mushaffa'u Abbi ya tsaya ganin an tsaida rana kafin ya wuce.
Sun tsaida nan da lokacin dazata gama karatunta watanni biyu masu zuwa sai ayi biki.
Mushaffa'u tunda yaji haka bakinsa yaqi rufuwa sai tsokananshi Addawiyya ketayi shikam sai biye mata ya keyi cikin nushad'i.
Salma tasha kuka sanda su Addawiyya suka tafi barinma dataga har da Hindu aka tafi, da kyat mama tayi ta bata baki tare da tuna mata cewa in Allah yasa Mushaffa'u yasami aikin dayake nema a arewa bank itama zata koma kanon dazama kusa dasu umminta, sannan tayi shiru yayin da Mushaffa'u yake ta mata dariya yana mata waqa wai tazama mai kukan banza, dakyat mama ta samu ya bar tsokanta bayan tayi mishi jan ido.
******* Baqin kano sun isa lafiya, bayan sun huta gajiya a gidan aminin Abbi Alhaji gambo da la'asar suka d'unguma zuwa gidansu wanda iyalen Alh. Gambon suka kyarashi tsaf tunkafin su iso.
A unguwan Nasarawa gidan nasu yake, unguwan da masu kud'i suka cikashi, tun a hanya Abbi yace da Alh. Gambo "abokina "amma ba'anan unguwan gidan namu yakeba? Ya amsa "Anan ne aminina "tofa amma kasan unguwan ta masu hannu da shuni ne ko? "Eh, nasani kuma kaima ai mai hannu da shunin ne shi yasa na saya maka gida a wurinsu.
Abbi ya had'e fuska yace "to ka sai dashi kasamamin wani a kusa da kai zanfijin dad'i.
Murmushi Alh. Gambo yayi sannan yace to muqarasa gidan sai muyi maganar anatse.
Gida fa mai kyau da tsari gashi gato komi yaji irin na zamani, bayan sun gama dubawa Alh. Gambo ya dubi Abbi yace "gidan nan na mai gida nane yaji ina cigiyan gida ne zansaya shine yace inzo ya saidamin da nashi wai yayi mishi qarami zai koma wanda yafishi girma, atake mukaje nagani mukayi cikini na biya amma ya ragemin sosai akan yarda yace yayi mishi kud'i, shi azatonshi nine zan zauna sai daga baya yasan bani bane don haka in ka huta na kwana biyu sai inyima jagora kaje da kanka kaqara yi mishi godiya.
Numfashi Abbi yaja ya amsa "tam aminina sai kasamana ranar dazamuje kuma ina qara yima godiya sosai Allah saka da Alkhairi ya bar zumunci "Amin su ummi suka amsa.
Asatin dasuka iso Alh. Gambo ya samawa Addawiyya wata makaranta mai kyau tacigaba da karatunta kuma suka barta a ajin da take, sosai takejin dad'in karatun harma tayi qawa mai suna maryam Rano.
Aunty Hindu kuwa aiki ake neman mata kuma tana cigaba da idarta yayin da ummi take kula dasu sosai, basu rasa komiba na dangin kayan more rayuwa.
Abbi kuwa har ya bud'e shago na saida atamfofi akasuwan kwari, don haka baya samun zama dasu sai da dare.
Yau hutun qarshen mako kuma ranar suka shirya zuwa gaida uban gidan Alh. Gambo mai suna Alh. Muktar daloli.
Mrs j moon
[1/4, 8:42 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
Na
SAFIYYA.
*Masha ALLAH Your love, is sweet and true🤝 You are an ideal couple👫 Always stay together,🤳🏻 and the roads ahead shall shower only happiness 💃🏻Happy wedding anniversary to you my everlasting Bahijja (bebeelo)* 😍😘
This page is for you members of sophy nd vc novel luv u sosai uncountable, like yawan malalin gashin tunkiya😅.
*22*
Tafiya sukayi mai cike da nushad'i Abbi da Alh. Gambo cikin motar babban yaro Alhjin Suka shiga mai suna ayub ummi kuma na ubayyu suka shiga yaronshi na biyu kuma auta domin daga kanshi mamansu tasami matsa a mahaifarta bata sake haihuwa ba.
Sun sami ilimi sosai both side boko d na islama dukkansu suna aikin gobnati kuma suna da rufin asiri dai dai misali, Ayub yayi aure har da yaranshi biyu ubayyu ne yake bisa hanya.
Maman su hajiya Raliya mace ce mai kirki da dad'in zama yanzu haka tajawo ummi ajiki ta maidata tamkar 'yar uwarta ta jini inkagansu kace sun dad'e tare da juna ne.
Sun sami tarba ta karamci sosai a gidan Alh. Muktar daloli. Mahaifiyar hajiya sharifat wanda ake kira da hajja ita ce tayi ta hidima da su.
Hira suke ta sha abinsu cikin falon hajja bayan kammala cin lunc dinsu.
Azuciye ta shigo ba d'a'a ta zaune gefen Hajja tana ta cika da batsewa cikin daqunar rai Hajja ta danqashi kanta tana cewa "wai miyasa har yanzu baki da nutsuwa ne khairiyya? Tura baki yarinya da aka kira da khairiyya tayi tace "minayi kuma hajiyan complain? "Kinci gidanku nace, ke makauniya ce halan sanda kika shigo bakiga bak'i a tare dani ba ne ko ya? . "Oh sorryn ku mutane, tafad'i cikin salon iskanci. Hajja sauke kanta tayi qasa cike dajin kunyar abinda khairiyya tayi ma baqinta, su kam su ummi ko ajikinsu don ba'abinda ya damesu tunaninsuma wata qila tana da motsin rashin saiti ne dubi da yarda take ta gyad'a kai kamar mai sauraron music, nan kuwa da hankalinta ras tsaban rashin tarbiya ne ke damunta.
Ad'age take kallon Addawiyya wacce bama tasan tanayi ba don hankalinta nakan indian film da ake nunawa a Bollywood. Aunty Hindu ce take lura da abinda take yi kuma take taji tsanar yarinyar ya d'arsu a ranta, ta had'e rai ahankali ta matsa kunnin ummi tace "ummi kira Abbi mutafi hakanan wallahi natsani gidan yanzu, kallon mamaki ummi tabita da shi batare da tace komi ba tasoma dealing number n Abbie.
Sai bayan sa'asar sukayi haramar tafiya domin su Abbie sunfita da Alhjin wani wuri.
Abin arziki sosai Hajja tabasu, don ledar Hindu daban tabata abinda yayi mugun bawa hindun mamaki ainun.
Haka Alhjin yayi musu kyauta ta bajinta yayi ta musu godiyan ziyaran dasu kawo mishi. aha sukayi musu sallama sukabar Hajja cike da kewa. Ita kam 'yar fitsara khairiyya tana tsaye a balcony tana ta jifansu da harara kamar sunyi mata laifi, yayin da uwarta matar gidan hajiya Karima, basu kai isar dazata tafito su gaisa da ita ba, tana can kwance tana barcin asara, da alama wurinta khairi ta d'auko d'abi'un banza.
"Wallahi ummi tunda nake bantabajin tsanar gida irin na Alh. Muktar daloli ba duk da tarin karramawan da akayi mana "to Hindu duk akanmi kika damu kanki da zancen? Mu zumunci ya kaimu kuma munyi an wuce wurin don haka bana son sakejin maganar kinji ko? "Eh ummi insha Allahu ya wuce.
"Uhmm ummi wata qila zata zama 'yar gidanne domin nayi mufarkin wai Alhjin yazo neman aurenta tana ta kuka bata sonshi.
Da sauri hindu takawoma Addawiyya duka ta kauce tare ta miqewa ta gudu d'aki tana dariya.
Ajiyar zuciya ummi taja tace "Hindu lamarin auta yana jefani cikkn rud'ani fa. Kamar zatayi kuka ta amsa "nima haka ummi kuma wallahi yawanci mufarkinta gaskiya yake zama, amma ina addu'a Allah yasa wasa takemin batayi mufarkin komi ba "Amin dai.
Da hanzari ta sauko down stairs tana gyara zaman qaramin hijab d'in na school.
Ta sussuna gefen ummi tace "ina kwana ummi? "muntashi lafiya auta? Lafiya lau "madallah.
Tana qoqarin fita ta tsinkayi muryan Hindu "autan ummi dawo maza ki karya, a mairaice ta juyo "Aunty zan makara in na tsaya yin breakfast gashi yau monday "koma miye sai kinsha koda tea ne kafin ki tafi don haka oya zo ki amsa, kallon ummi take tana son tasa baki amma taqi cewa komi sai ma yi tayi kamar bata wurin ta maida hankalinta kan karatun dala'ilul khairat d'inta.
Baki ature tayi ta shan ruwan tea din bako bread har ta hanye tas ta fice da gudu tana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta.