← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 38

Sashe 14

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"hindu hakiqanin gaskiya inajin tsoron ayyikan auta kada fa muyi sakaci wata rana awayi gari ta hauka ce.
"A'a ummi ba'abinda zai faru insha Allah, adage dai dayi mata addu'a shi yafi "to Allah ya warware mana lamuranmu "Amin.

Bayan sungama cin supper, suna zaune a parlor, ummi tana damawa Abbie fura, hindu ta duqufa akan laptop d'inta tana wani aiki don yanzu lecture ce a fce wacce watan ta nabiyu kenan da soma aiki.

Addawiyya tare da Abbie kuwa kallon wani drama na larabawa sukeyi, duk abinda bata ganeba cikin maganarsu sai ta tambayi Abbie.

Ubaiyu yayi sallama saida aka amsa mishi sannan ya shigo ya zauna tare da zamewa ya gaida su ummi da Hindu, shi kuma Addawiyya ta gaishe shi.
Abbie ya tashi ya shiga room d'insa bai jimaba yafito da sak'o ya miqawa ubaiyu.
Yayi musu sallama ya fice, hindu ta dubi Addawiyya tace "malama tashi kiraka shi bakin motarshi, baki ature ta miqe tafita bako mayafi jikinta, ummi ta rakata da idanu fuskanta d'auke da murmushi, cikin ranta tana addu'ar Allah ya had'a kansu zumuncinsu dasu Alh. Gambo yakuma qarfi, haka abin take agefen Abbie, sosai yake murad'in su qulla zumunta tsakaninsu da zuri'ar Alh. Gambo.

Kamar yasan zata biyo shi a baya, da yafita sai ya tsaya a daf da parlorn yana ganin tafito yayi gaba cikin taqama taja ta tsaya tana kallon solon wani iskaro daykeyi mata, sai da ya shiga motarshi sannan ya ankara bata biyo shiba yafito da sauri yana waige waige can ya hangota tsaye bakin parlornsu ta kafeshi da mayun idanunta mai jefashi cikin rud'ani dazarar yayi arba dasu.

Sauke taqamarsa yayi yadawo inda take yayi kamar zai rungumeta ta ja baya yasa dariya yace "baki san kin girma bane halan, da kika fito babu mayafi? Harara ta watsa mishi, ya kuma matsowa kusa da ita tayi saurin juya mishi baya tace "zan saita maka maths d'inka da yasami matsala in har kace haka zaka riqa yimin, "minayi miki yanzu? Banza tayi mishi zuwancan kuma tace da shi "Sai da safe, kagaishemin da Aisha inkaje wurinta, kuma wayar da ka sayomin zaka bani, ina roqonka dan Allah kabawa Aisha ne domin ita tafini buqatar ta.

Ko kafin yayi magana ta shige parlor ta barshi nan tsaye cike da mamakin inda ta sami labarin sayar wayan da yayi mata.

Kamar kullum duk in sun fito break a school a qasan wata bishiyar mango suke zama suyi ta hiransu ita da maryam har zuwa sanda lokaci komawa class zaiyi.
Yauma zaune suke suna hira akan test d'in dasu kayi d'azun kafin fitowarsu. maryam tace "ke kam my Addawiy kinji dad'inki ba'abin da yake baki wuya jiba yarda kika riga kowa gama test alhalin da gwaraza masu tsananin kwazo a ajin amma tun sanda kikazo duk suka koma laqas kamar sun mace, ba salo da fi'ili.

Dariya Addawiyya tasaka sosai, "my Rano kina da abin dariya kam, yo nikam ai banga wani kwazo danake dashi ba tunda banyi ko quarter nkiba a komi d komai.
"Kefa 'yar wofi ce wata rana my Addawiy, wato abin naki har da tsokana ko? "Ba tsokana sai gaskiya 'yan matan rano. Dariya maryam tayi "my Addawiy da alama kina son garinmu, yakamata ki sa rana na kaiki kiga yatake, "aikam inasonta sosai, kuma insha Allah wannan hutun tare dake zamuyi acan.
Cike da murna maryam ta rungumeta ta manna mata light kiss a kumatu.

"Yawwa babe look at my new phone, maryam tace tare da fiddo da phone d'in tana nuna wa Addawiyya "uhmm tayi kyau sosai qawas amma dai wata qila zata zama hanyar lalacewarki ko kuma jiyo qamshin barzahu.

Wani kollo maryam da sauke mata tace "mi kike nufi? Ko dai kinamin baqin ciki ne nashigo gari da zazzafan waya ke kuma baki da ko gidan layi balle ki saran samun irinta.

Had'e rai Addawiyya tayi kamar bata taba dariya ba, maryam ta ja baya domin taji tsoron ganin mood d'inta sosai.

Allah ya tsareni tabewa na rashin aikinyi ace ni da kaina zan miki black stomach, tirr!! Wallahi, kuma kinsan nafi qarfin wannan banzan wayar taki ta sata, kisani in yanzu nace ina son waya wallahi kafin atashi school zaki ganni da apple bama tecno ba, don haka ina gargad'inki da kada ki kuma cemin inayi miki baqin ciki.
"To hajiya Ammi "bankai can ba amma ina so kina natsu in fad'amiki had'arin dake ga wayar nan "uhmm inajinki mai gani har hanji, "komi zaki ce na d'auka "to fad'an inji.

Sai Addawiyya ta kallace daga sama har qasa sannan tace "wayar takai kwana uku atare dake kina boyonta kada Ammi tagani sai jiya da dare kika fito da ita shima don d'an iskan da yabaki yayi miki qorafine da ki budeta zai kiraki.
to ki rubuta ki ajiye tabbas in kika koma da ita gida yau Ammi ta gani mai rabaki da ita sai Allah domin sai kin leqa barzahu na wucin gad'i sabida yanzu haka inda yayi satan wayar sungano shi yakuma ce ke yakawomawa anzo wurin su Abba, Ammi ta bincike d'akinki kaf bataga waya ba amma sunce ajira ki dawo abincikeki in da gaske ne sai abasu, don haka sai kisan mafita.

Ai tuni jikin maryam ya jiqe da zufa, tafad'a jikin Addawiyya ta rushe da kuka tana cewa "nashiga uku na lalace, ashe Ameer barawo ne bansani ba? "Ba barawo bane sonkine yaja mishi satan sabida da yarda kika matsa sai kinyi waya donmin kema a adama dake a social media alhalin kina sane Abbanki yace inkingama secondary zaki riqe waya ko wacce iri kike so amma son zuciya da hud'uban qawayenki su haule ya kaiki yabaro gashinan kinjawa yaro muta ne tabon tsiya yaci duka har ya gode Allah.

"Uhmm aminiyata bar wannan zancen kedai bani mafita "bansanya za'ayiba amma tashi muje wancan tap d'in ki wance face d'inki, insha Allahu zuwa kafin mutashi mafita zai zo mana.

Jiki asanyaye tabi bayan Addawiyya, bayan ta wanke face d'inta, suka taho Addawiyya tanayi mata nasiha data bar biyewa qawayen banza marasa kamun kai.
"ya ilahi!! Ranota kalli bishiya tana tafiya, maryam ta dubi wurin da Addawiyya take nuna mata tayi arba da wata qatuwar bishiyan kuka tana rangaji jijiyoyinta duk awaje ta nufo wurinsu zata kwalla ihu Addawiyya ta rufe mata baki tasa hannunta ta shafa mata idanu tace "dalla can matsoraciyan banza daga wasa har kin saki fitsari, jikinta ta duba taga qafafunta duk ruwa alamar fitsarin tasaki dai.
"Ban yafe ba Addawiy, ace don Allah ajannun da kike ta ammali dasu zaki sa subani tsoro har inyi fitsari ban sani ba? Dariya Addawiyya take tayi mata har suka iso class ta d'auki ruwan roba a lokansu ta wanke qafafunta.

Malamin physics ya shigo period d'insa yana daf da qarewa wayar maryam tasaki sauti mai qarfi, cikin fushi ya miqawa Addawiyya hannu ta saka mishi wayar, ya jefa a aljihu ya fice baiko gama darasin ba.

'Yan ajin sai cece kuce sukeyi wasu na Allah ya qara wasu kuma nayi mata jaje, ko kallo basu isheta saima ta soma yiwa maryam magana qasa2 "kinga munsamo mafita ko? "Eh wallahi qawata, "kinga sim din na cire in munfita sai mu karya dama kunnawa nayi yaji sautinta duk don ya kwace, inkin koma gida sai ki tubure ke bama kisanshi balle har yabaki waya "tam haka za'ayi 'yar gari "kuma kinsan shima sace wayar za'ayi bazaiyi mishi amfanin komi ba duk kuwa da rawan jikin da yakeyi yaje ya bud'e media, wawa wanda matsolanci ya hanashi siyan waya babba.

Wata uwar dariya maryam tasaka duk ajin suka maida hankalinsu kanta ta gintse fuska tana hararansu, Duk suka kauka fukokinsu domin sun san yanzu baqaramin aikinta bane ta feshesu da matsifarta.

******Rayuwa tacigaba da tafiya sannu sannu gashi yanzu har su Addawiyya ta kusa kammala secondary.

Tuni Salma ta haihu d'anta namiji yaci sunar Abbie ana kiranshi da Annur.

Hindu kuwa kimanin watanni biyar kenan da yin aurenta da Alh. Muktar har tasamu rabo.

Addawiyya ce tafito da sauri tace da ummi "natafi school daga can zan wuce wurin Aunty Hindu kuma sai ranar lahadi zan dawo tunda yau Friday "to kigaishe da ita sosai ga bushashen zogale ki kaimata kozatayi miya "ohk, ummi sena dawo "auta don Allah kada kiyi fad'a da mutanen gidan nan kinji? "To, amma fa in sun tabani bazan kyale kowa ba "a'a auta bance ki ramaba kinji ko? "Eh, zan kiyaye ummi "to madallah, Allah ya tsaremin ke "Amin ummina, ta janyo hanun ummin ta manna mata kiss tafice da gudu tana kiran drivernsu.

Akwwnakin baya Abbie yasaya motoci biyu tashi d'aya nasu d'aya, ya nemi driver mai hankali yana kaisu duk inda zasuje.

*****misalin 1:00pm suka tashi daga school, bayan sun sauke maryam driver ya wuce da ita gidan Hindu.

Driver yana gama parking ta fito ta dubeshi tace "malam khalid sai jibi da yamma kazo mu koma gida "to insha Allahu zanzo akan lokaci "aha sai kazo d'in.

Tashige parlor d'auke da sallama.
Bata tadda kowa cikin parlorn ba don haka sai ta cilla school bag d'inta samar kujera ta zare qaramin hijab d'inta tare da d'ankwalinta gashina ya bazu abayanta, ta fad'a bisa kujera tana kiran "washh wallahi nagaji.
Zuwa can ta yunqura ta zare sandal dinta tare da socks, "inje na watsa ruwa wata qila zanfijin daidai, ta furta hakan tare da miqewa ta nufi room d'in Hindu.

Daf dazata shiga room d'in ta juyo caraf idanunsu ya had'u ta kwasa da gudu ta shige cikin room d'in.

Shi kam murmushi yayi ya miqe ya fice yana tambayar kanshi wannan kuma wacece?

*mrs j moon*
[1/10, 8:29 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*26*

Motsin shigowarta ya tashi Hindu wacce take barci, ta yamutsa fuska tana hararan Addawiyya "autan ummi wai har sai yaushe zaki hankali ne?
Zaunawa tayi gefen bed d'in ta kamo hannun Hindu tace "affuwan maman 2, wani mutum nagani a parlornki yana da d'an kyau kuma naga yayi kama da habibinki mr tsoho.
Duka Hindu takawo mata ta matsa tana dariya.
"Yaron Alhji ne na biyu sunarsa Abdul Hameed, jiya yadawo daga Egypt wani course da yaje, cikakken doctor ne.
Chapter 14 · 0% Book details