← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 38

Sashe 35

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya biyo bayanta ya kama hannunta yace "bakice a gaida my heat riyya ba, da sauri ta amsa mishi "a'a zanba zance agaisar ba riyya ba, ta fizge hannunta tayi gaba bud'e murya yayi da qarfi yace "gudan jininta dai tana hannunki don haka akul kika soma kishi da ita tun zuciyar mijinta bai gama tantance zancen ba.

Wani juyowa tayi afusace, ya kwasa da gudu ya fad'a motarshi yafice a 100 yana ta kyal kyalan dariya domin sosai yau rigimarta yajefashi cikin mishad'i.

Ita kam zubewa tayi awurin tana maimaita kalmar kishi cikin ranta, "kardai ace ya Alee shima yayi mishi maganar da yataba yimin a hospital ne? To inko yayi masa ita lallai ina cikin matsala,, Saita dafe kanta cike da rud'ani takuma cewa "To ma wai duka duka yaushe ne ya Alee yarasun da har Hameed yasami kuzarin da zai soma min zancen banzan nan? Ganin bata san amsarba sai tamiqe jiki ba kwari ta shige ciki tana aiyana abinda zatayiwa Hameed duk randa yakuma zuwa inda take.

Kamarko yasani sai ya d'auke qafarshi tsam daga gidan baima ko kiran wayarta balle yaji irin tanajin da tayi masa.

Baby ummul kuwa sunyi mugun shaquwa da Addawiyya,, batayi mata rigimar komi,, sosai takejin dad'in zama da yarinyar, sai su qulle cikin d'aki suyi ta ifece ifacen su, hakan kuwa yana faran tawa ummie da Abbie rai sosai sakama kon zuwan yarinyan sun fahimci ya tafi mata da damuwarta sama da kaso 80 cikin d'ari, shi yasa kullum suke godewa Hameed da samishi albarka.

Cikin sauri tagama shiryawa ta d'auki ummul itama ta shiryata cikin kayan sanyi masu laushi ta ratayo bag d'inta maroon ta sauko downstairs, ummie ta taradda zaune bisa dinning tana yin break fast, qarawa tayi ta zaumar da ummul bisa cinyar ummie tace "ga rainonan nakawo miki kema kisami ladan.

"Tam auta na amsa, tad'ora da cewa "sai ina kuma yau haka da sassafe?

Sai da tayi gaba sannan ta amsa "skul zani.

Cikin mamaki ummie ta mai maita skul kuma? "Eh, ummie nayanke shawaran komawa ne domin nafahimci kuna son haka, "tam hakan yayi kyau auta, Allah ya tai maka, "Amin ta amsa tare da d'agawa ummul hannu itama hannun ta d'aga mata tana tsalle jikin ummie.

Driving takeyi ranta fal da tunanin mafarkin datayi da Haydar daren jiya, lokaci zuwa lokaci sai tasaki murmushi cike dajin dad'i.

Ta mirror ta lura da wata mota tana binta abaya, hakan tacigaba da tafiyarta tana tunanin ko waye wannan dake bin nata?

Daf dazata shiga get d'in skul motar tazo ta wuceta da gudu tuni bace bat kamar walqiya.

Tabe baki tayi tare da shigewa ciki tana mai furta "can ta matse ma koma waye a matse matsin matsalar shi.

*mrs j moon*
[2/4, 10:37 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*47*

parking tayi a qasar wata bishiya tayi jim kamar baza ta fitoba zuwa can kuma sai ta bud'e qofar ta zuro santala santalan qafafunta waje tana qarewa students d'in dake kai kawo a harabar wurin kallo, caraf idanunta suka had'u dana wani malaminsu yako kafeta da idanu quri, da saurin ta koma ciki ta kulle door din ta kwanta sosai ta d'aga kanta sama ranta abace.

Qaran shiqowar message taji cikin phone d'inta ta d'ago ta fiddota cikin bag ta duba.
Baquwar number tagani qin bud'ewa tayi tare da yin cilli da wayar cikin jikka, ta koma ta kuma kwanciya tana tuno yarda taga Haydar cikin mufarkinta.
Qiba, haske, jin dad'i duk sun bayyana ajikinsa ga wani qamshi da yake fitarwa mai dad'in shaqa, hatta wurin da yake zaune abin kallo ne, ni'ima mai dad'i yake ta fitarwa sai ta qamqame jikinta cikin jin dad'i tana mai furta kalmar "Alhamdulillah a fili sai kuma ta d'ago ta kife kanta samar sitiyari tayi shiru kamar mai barci tsawon lokaci ta d'auka ahaka sannan ta lalibo phone d'inta ta duba saqon daya shigo d'azun.

*kwailata lallai kinyiwa kanki qiyamun laili tunda kin koma skul amma da yau na yanke zanje nasameki insa ki koma ko tatsiya ne sai gashi kin hutashshe dani, don haka inayi miki fatan samun nasarori masu yawa ki kulamin da kanki sosai Allah yadawo dake lafiya, Abu ummul bait ne mijinki bada jimawa ba da yardan mai duka*

Wani dogon tsaki taja tare da furta "iska na wahalar da mai kayan kara, kuma asannu zan gyarama zama indai har baka bar kirana da kwaila ba, ai wannan ma sunan rainin wayau, fuska a had'e ta fito waje ta kulle motar batare da ta kuma kallon inda taga mayen kallon ba sunar da tabawa malamin kenan ta doshi wurin dasuke zama dasu maryam tun can da, sabida tasan kotace zata shiga class yanzu lokaci ya qure sun kusa fitowa.

Zama tayi tare da juyawa mutane baya ahaka maryam ta qaraso wurin sakamakon hangota datayi tun sanda ta fito daga mota.

Cikin mamaki ta zauna gefenta tare da dafata tace "qawalliya dagaske ke nake gani a cikin skul yau?

Bata ta juyoba ta amsa mata da "eh, nice ya kike dasu mamie?
Sai da ta miqe ta dawo gabanta ta duqa sannan ta amsa "muna lafiya lau.
"Masha Allah.

Shiru sukayi Addawiyya taqi d'ago kanta ta dubi maryam ita kuma taqi tashi daga tsugunon datayi a gabanta, zuwa can ta sa hannun ta tureta aikan abazata ta ganta qasa zaune, dariya tasaka mata irin ta mugunta, maryam bata ce komi ta koma ta zauna agefenta ta ta aikin kallonta, ganin haka tuni ta gintse fuska sai abin yabawa maryam dariya kuma.

Qawayensu ne sukayi ta zuwa suna yi mata ta'aziyya tana amsawa ita da maryam ganin sunqi qarewa masu zuwan yasa ta miqe tana mai cewa maryam "besty bara na koma mota kafin lokacin shiga ta lecture yayi domin naga mutanen nan so suke su sani kuka kuma alhalin nayiwa ya Alee alkawarin nadai yi masa kuka sai addu'a.

Biyo bayanta maryam d'in tayi tana cewa "hakan shi yakamaceki dashi dama, Allah dai yaji qansa da rahama "Amin.

Atare suka isa wurin motar suka shiga.

Maryam ta dubeta tace "amma besty ya akayi kika sanja ra'ayinki kika dawo skul?

Tana murmushi ta amsa "wallahi tunda na falka misalin 3 daren jiya naji jin son komawa skul ya d'arsu azuciyata kuma inajin duk don ganin ya Aleen danayi ne a ciki mufarkina cikin shiga mai kyau da jin dad'i da alama yasa mi kyakykyawan makoama sannan maganar da mukayi dashi ita ce ta karatu na, to inaga shine yahassa samin son komowata.

"Uhmm yayi kyau hakan amma inajin junnu uncle d'in kine dai yafito miki a siffarshi shine kike ganin kamar ya haydar ne.

"To nidai koma waye nasan mufarkin ya jefani cikin nishad'i haka nan yakasa wucemin arai.

"To Allah yacigaba da sadamu da mufarkan Alkhairi "Amin.

Koda zata koma gida wannan motar data biyota ita ce tayi mata rakiya har bakin get sannan ta juya.

Cike da saqe saqe tayi parking ta mufi ciki.
yaran Salma tare dana Hindu tayi arba a falon suna ta iface ifacen su da ummul.

Cogewa tayi a qofa tana ta kallonsu cike da jin dad'i.
Dama ace Allah ya k'addara cewa ya Alee yabar gudan jininsa a jikina fa, uhmm lallai da nafi kowa jin dad'i da kuma wata rana da shi ko ita za'ayi wasar nan.
Cikin zuciyarta take wannan tunanin, atake kuma sai hawaye suka soma zubo mata tayi sauri sharesu tana mai furta "affuwan ya Alee, bayin kaina bane zuciyata ce takasa manta ka.

Muryan ummie taji kusa da ita yasa tayi saurin fad'awa jikinta tana ta sauke ajiyar zuciya.

Shafa kanta ummien tayi2 har ta dawo natsuwarta sannan tayi qasa da murya tace "nasan damuwarki haydar ne to don Allah ba dan niba ina son duk sanda kikaji ya fad'o miki arai kiyi mishi addu'a ne ba kuka ba, kinji?

Gyad'a kai tayi tare da janye jikinta ta qarasa wurin yaran suna ganinta suka soma ihun murnan ganinta ta durqusa tayi ta manna musu kisses cike da murna.

Washe gari da sassafe tafita don ko ummul bata tashi barci ba.
Misalin 10am ta fito daga lecture.

Tafiya suke ita da maryam suka tsinkayi muryan khairi tana kwalla musu kira atare suka juyo ta qaraso tana dariya harara addawiyya ta cilla mata ta kuma saka dariya tana cewa "ke madam ashe dai kin dawo skul ne bako sanarwa.
"Yo ai yanzu idanunki yaga ne miki, dalla kina tawani kwallawa mutane kira kamar wata yarinya, girma yariga hankali zuwa dama ai.

Dukan wasa ta kawo mata tayi sauri gofcewa duk suka sa dariya.

Cikin motar maryam suka shiga sunata yi mata murna tare da addu'ar Allah ya tsare ya ka tsone idannun maqiya sai amsawa take da Amin Amin, da yammacin jiya Abbanta ya danqa mata key d'in motar.

Sosai Addawiyya ta mai da hankali akaratunta sabida komi yazo daf da qarshe, a tsawon lokaci data d'auka nata zuwa uncle d'inta shi yayi ta fitowa a mutum yana zana mata duk kannin wani tests da exams da akayi da bata nan shi yasa komi yazo mata cikin sauqi.

Mai binta abaya dai ya bari kuma har lokacin bata san ko waye ba haka taqi tambayar habibullah sabida bata son ya tado mata da zancen aure sam.

Su Abbie kam yarda ta dawo real Addawiyyanta sosai hakan yake faranta musu rai, shi yasa tunda suka fahimci bata son zancen aure sai suma sukay biris da ita amma hakiqa akwai abinda suke shiryawa agame da aurenta.

Tafiya take cikin jin dad'i ta kunna begen Annabin Allah mai taken murna muke da zuwan shugaba d'aha...... Akan hanyar ta na zuwa saloon sai gyad'a kai takeyi tayi tare da bin begen,sai da tayi nisa da gida sannan motarta ta bata matsala gangarawa tayi gefen hanya ta gyara parking tayi shiru tarasa yarda zatayi gashi tayi nisa da gida.

Har ya wuce sai kuma ya dawo da baya ya iso dai dai inda take yayi parking tare da fitowa.
Nocking yayi mata ta d'ago tare da sauke glass ta zuba mishi idanu, murmushi ya sakar mata tayi saurin kauda fuska tayi tana maijin wani tashin tsiyar jiki yarrrr, yace "matsala kika samu ne?
Chapter 35 · 0% Book details