← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 38

Sashe 4

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****** Addawiyya jitayi anayin qasa da ita wani uban hucin zafi yana dokanmata jiki, sai kuma taji an gizgeta anyi sama da ita, atake tasomajin iska yayi mata yawo domin jin shigarsa takeyi cikin bargo da jijiyoyin jikinta, bata kuma sanin abinda yake faruwa ba illa dai taganta tsaye agefen wani qaton fili rasharre tas dashi.
Waige2 tasomayi can ta hango wani lambu mai kyau ta taka ahankali ta isa wurin, k'aton lambun ne mai d'auke da kayan marmari kala kala, cike da gajiya ta zaune qasar wata bishiyar d'orawa ta dafe kanta tana hawaye "oh ni Addawiyya rayuwata tana cikin garari, nan kuma ina nakawo kaina? Wani qishin ruwane ya tasomata kamar mak'oshinta zai kama da wuta don azabar bushewa tamiqe cike da ganin jiri tasoma bin wurin da kallo, kamar asama taga tulo agabanta tako d'agashi sama ta kafa baki, jikinta narawa tasoma shan ruwan ciki, saida taji cikinta ya k'ulle sannan ta direshi k'asa ta koma ta jingina da itaciyar d'orawan tana lumshe idanunta,, batako jimaba barci ya d'auketa awurin ta zame ta kwanta.

****** rukunin mutanen dasuka nufo bakin kogin cigogo suna isowa suka tarada da gawarwakin Amrya haule, A'ilo tare da hanne abakin kogin, atake suka tsamosu waje. Suna shirin barin wurin suka ci karo dasu hisk'ilu, juma tare da ilya tsirara babu kyan gani jikinsu duk jini halittansu duk ya sanja kamar basuba.
Cikin gigita suka ja baya suna k'aremasu kallo da kyat wani ya iya ganosu juma ne suka koma haka.
Suka d'auke zuwa bakin wuron hard'o jama'a suna ta zuwa ganinsu yayin da danginsu sukayi ta kukan rashinsu. Hard'o yayi umurni da ayi musu sutura yanzu amik'asu zuwa makwancinsu.

******** Tawagan su Abbi kuwa sunyi dube duben daza suyi har sun gaji basuga ko alamar mai kama da Addawiyya ba, ganin dare yasoma kuma bawanda yayi sallah sai suka yanke shawaran komowa gari gobe in Allah yakaimu sai su dawo lokacin ido naganin ido.

Abbi bayako gani gabansa yabiyo bayansu, tuntube yaci da wani abu koda yaduba sai yaga takalman Addawiyya ne ya duk'a ya d'auka yana nunawa abokan tafiyanshi duk suka tsaya suka soma duba wurin nanma wurin wata bishiya suka sami gyalenta ganin haka sai suka k'ara qaimi amma basu kuma ganin komi nata ba, hakanan suka haqura suka baro dajin cikin jimami tare da burin komawa gobe.

*****wani farin haske ne yabayyana gaban Addawiyya zuwa can ya rikid'a yakoma mutum atake kuma k'amshi ya cika wurin kamar anyi barin turare.

Takowa yayi asannu cikin mulki zuwa gabanta ya tsaya yana murmushi ya bud'e hannayenshi sama ya runtse manyan idanunshi yace "welcome to my place mai babban suna. Ya soma takawa yana bin wurin da kallo zuwa can ya cinkayi wata guguwa ta nufo wurinshi cikin hanzari yadawo yatare inda Addawiyya take kwance tana shakan barcinta kamar tasami gadon umminta.

Iskan tasoma lafawa tana gama lafawa wata budurwa fara tas mai tsananin kyau ta bayyana ta nufo wurinshi gadan gadan tsawa ya daka mata taja ta tsaya tana kallonshi zuwa can tace "ba wurinka nazoba malam kayata nazo d'auka "tana ina kayan naki? Gatanan ka kareta "oh wai mai babban suna kike nufi itace kayan taki ko wa? "Eh itace kayata, kuma yau zan aika da ita k'iyoma sabida kuskuren datayi na shigamin fada har tayimin barna "fadarki ko fadar wasu domin kwacensa kikayi sabida tsaban zakunchinki, to kisani daga yau baki qara aikata zalinchi har abada, ni masoyin Allah da manzon Allah Habibullah ina mai umurtanki daki bar yankinnan tun fushina bai sauka akanki ba.

Cike da tsoron kalamanshi ta matsa baya ta rikid'a takoma rabi mutum rabi micijiya ta nufoshi da wata irin iska ya d'aga hannunshi ya nunata atake sarqa ya zubo tayi maza takoma mutum sarqan ya cukui kuyeta ya nunata da yatsa yace "k'arshe zaluncinki yazo yanzu zan aikaki zuwa ga mahaifinki dama yana nemanki ruwa ajallo don haka ki kuka da kanki sabida kinfi kowa sanin waye malam, hukuncin dazai miki sai kin gwammace bakizo duniyaba.

Cikin kuka take roqonshi da yasaketa bazata k'ara zalinchiba zata koma ga Allah tacigaba da bautansa yanda yakamata.

"Inkin koma yankinku sai ki tuban da kyau amma nan kam kinbarshi kenan har abada, dama wannan ranar nake jira kuma gashi tazo.
Da yatsa ya nunata iska tayi samada ita cikin sarqan tabace bat kamar walkiya.

Jan numfashi yayi yadawo gaban Addawiyya ya duqa yace "na ceceki ahannun yaran sarkin yankin rijiyan kugu kuma yanzu Allah ya kuma bani ikon tsirad dake daga muguntar micijiya zailumat sannan kuma bada jimawaba zan maidaki zuwa ga iyayenki,kisani mai babban suna inatare dake ne tun kina cikin mahaifiyarki 'yar wata hud'u kuma zanci gaba da kasancewa dake har izuwa k'arshen rayuwarki. Ya bud'e baki ya hura mata iska wani haske ya fito ya sauka zuwa jikinta atake suka bace bat shi da ita kuma alokaci d'aya wurin yakoma babu dukkanin wani shukan kayan marmarin yadawo fili wanda baya da yawan bishiyoyi.

******Daren ranar kam dukkanin d'aukakin al'umman garin yankin jangaba k'alilan ne sukayi barcin dad'i cikin marasa barcin dadinkuwa har da su Ummin Addawiyya domin kwana kuka ummi tayi yayi da Abbi ya kwana sallah shima in yagaji sai yatsaya yayi ta shere hawaye sai kuma ya tashi ya d'ora, yana addu'ar Allah yabayyana mishi d'iyarsu cikin gaggawa.
Ahaka suka kwana basu rintsaba ko kad'an.

*Kai haba kubar jin tsoro man*🙊

*mrs j moon*
[12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*Shafin nakine K'awalliyata Zainab VC.ina jidake sosai my sis, Allah yabarmu tare*😘

*9 ~ 10*

Asannu tasoma motsa idanunta har ta bud'esu duka tayi mik'a tare da salati ta d'ora da addu'ar tashi daga barci, ta dafe kanta tana son tuno wani abu.

Azabure ta duro daga bisa gadon tasoma bin d'akin da kallo, jikinta yasoma rawa sai kuma tafashe da kuka ta durgushe k'asa tana yarfe hannunta "wayyo Allahna ni Addaiyya naga takaina, nan kuma ina nakawo kai? Ya ubangijin sammai da k'assai ka kawomin d'auki bisa wand'an nan abubuwa dasuke faruwa dani, ka kanemomin hanyar dazankoma zuwa ga mahaifana. "Amin taji amsa mata tamiqe tana kalle2, Alamar tafiya taji yasa tayi tsam tana saurare can ta kumajin
Kamar ana magana kusa da ita ta sai ta bud'e kunniwanta sosai tana saurare amma sai taji shiru,, ta miqe a tsorace tana k'arewa d'akin kallo k'aton d'akine wanda yake d'auke da kayan alatu masu mugun kyau da had'uwa, tunda Addawiyya take bata taba ganin wuri mai kyawun hakaba duk kyau da tsarin d'akin mama Ramlat batajin yakai ko kwatan wan nan a had'uwa.
"Oh ni ko inane nan? "Baza'acutar dakeba mai babbab suna, kidai hanzarta rama sallolin da'ake binki.

Agigice ta mik'e tana duba ta ina maganar yake fitowa, jitayi anja hannunsa har zuwa bakin toilet ance "kiyi wanka ki d'auro arolla sai kizo ga abinci can yana jiranki. Muryan mace taji mai dad'i tace da ita haka.

Murya ta bud'e ta kwalla ihu "wayyo ummi nafad'a gidan aljannu, nashiga uku, rashinjin magana baiyiba wallahi musanman na iyaye, gashinan nazo inayin nadama.

Wani ubanTsaki taji anja mai qarfi tare da turata bayin, jikinta ya d'auki bari. "Inbaki hanzarta sauke bashin sallar da ake binkiba Allah zan maidaki biri yanzunnan ki koma daji dazama.
Tanajin haka jiki na bari tasoma cire kayanta ta hau wanka tana gamawa ta d'auro arollah ta fito kaya tagani agefen gadon tabishi da kallo saiji tayi ance "oya d'auki kisaka bamusu ta sanya ta duba geden damarta taga sallaya shinfid'e tare d hijab tamatsa ta hau kai tasoma ranka sallolin da ake binta ta d'ora da sallar azuhur ta ranar sabida lokacim k'arfe 1:45pm.

Tana idarwa ta takure wuri 1 ta zuba uban tagumi,,, kice take da kewar su Abbinta tasan yanzu duk inda suke sunanan cikin tashin hankalin rashinta musanma ma umminta domin tasanta da rud'ewa.
Uhmm ko ya adda Salma zakaji intami labarin bacewata oho, Allah gani gareka. Duk cikin zuciyarta take wannan zancen sai tafashe da kuka,, sanda tayi tunanin qilama gidan yankan kai ne ta fad'o, Kukan nata sai yaqaru tayi2 bamai rarrashinta.

"Uhmm nidai kam yaya yahad'ani kula da sangartattan bil'adama oooo.

Wani tsalle tayi ta koma gefe tana raba idanu, tanason ganin wake mata magana amma bataga kowa ba sai sautin tsaki dataji ankuma ja tare da buga k'ofar fita daga room d'in da qarfi ta ja baya tana gwama numfashi.

K'amshin abinci taji yasa ta kai dubanta inda qamshin ke fitowa arba tayi da girke2 masu rai da lafiya ai cikin sarsarfa ta qarasa wurin tasoma bama cikinta hakkinsa bata kojin tsoro domin jitayi kamar tana d'akin umminta ne.

Tana gama ci taji wani barci yazo mata tazame awurin ta kwanta, rufe idanunta ke da wuya barci yayi gaba da ita.

****** washe gari Abbi da mutanen gari suka koma dajin neman Addawiyya, sunsha yawo har sun gaji basu gantaba don haka sai suka haqura suka dawo gida, ard'o yayi ta jajantawa Abbi tare da iyayen yaran dasuka rasa 'ya'yansu kuma yace ya soke dukkan wani yawon gudu Amarya ayankinshi sannan hatta wasan iyon ruwa ta kogin cigogo ya soke kuma dole kowa yasa yaronshi makarantar addini,, zaije gari yasamo malamai.
Ahaka aka watse taron kowa yana fad'an albarkacin bakinshi.

Salma kam sumarta biyu kafin su iso jangaba. Sosai ta d'imauce dajin labarin, koda suka iso kuka tafashe dashi mai cinrai barinma da taga kayan shopping d'inta tare da a kwatin kayan makarantar ta sai ka sake sumewa da kyat aka sami ta dawo hayyacinta Abbi yasa agaba yayi tayi mata nasiha nata dauki qaddara tazamo mai juriya tareda tawakkali.

Mushaffa'u shine yaqara yi mata nasiha harta soma haquri ta rage kukan.

Kwanar su uku mama Ramkat tare da aunty hindu da mushaffa'u suka yi sallama dasu suka koma garin kwantagora yayin da Salma tak'i binsu fafur tace ita sai 'yar uwanta tadawo zata dawo, ba'ason ran mushaffa'u ba yabi su mama amma ya qudurta kwana biyu zaiyi yadawo su wuce.
Chapter 4 · 0% Book details