← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 38

Sashe 17

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sa ya jingina sosai a kujeran dayake zaune ya lumshe idanunsa yana wani sakin murmushi.

Tsaki Hameed yaja ya kuma cewa "to tun wuri kacire idanunka akan yarinyar mutane, kuma nibanga aibun shigarta ba "in anqi fa? ya amsa mishi cikin isa.
"Duka zaka sha wurin samarinta.
Wani zabura Haydar yayi yace "kai! banson tanbad'a fa, 'yar wannan yarinyar ce take da samari?
"Uhmm naka wasa ne bros.

Komawa yayi ya gyara zamansa, Hameed yabishi da kallo cike da zargi.

Sai da ya bud'e kwankwanin Amstel ya zuba awani qaramin glas cup ya kai bakinsa ya sha kamar rabi sannan ya dubi Haydar "mike damun ka? Kai tsaye ya amsa mishi "so da k'aunarta yayimin shigan bazata haka nan atake nakejin matsanancin kishinta tunda idanuna ya hangomin shigar dake jikinta daga shigowarmu.

Kut!!! Sautin had'iyan yamun da Hameed yayi kenan sai kuma yasoma tari zuwa can ya lafa mishi, Haydar ya miqa mishi ruwa ya sha yana ta jera mishk sorry, shikam sai gyada mishi kai yakeyi.

Ya lalibo handkerchief ya miqa mishi, ganin yarda yaketa zufa kamar ya had'iya kunama.

Idanun Haydar ya tsareshi da su yace "Mike faruwa Hameed? Ko kaima zuciyarka ta kamu da son tane? Cikin hanzari ya amsa "A'a bros, ni batayiminba sam kuma bazata taba yimin ba "topah, minyakawo wad'annan zancen haka? "Uhmm ya Haydar mubar zancen nan sai in mun isa gida tukunna "ohk, amma ina son kada ka boyemin komi dake ranka, in har kana sonta ka sanar dani tun wuri "ni kam koda zan so mace bazanso kamar Addawiy ba sabida Allah tayimin qarama da aure "kai banson iskanci ita d'ince tayi qaramar? Yana dariya ya amsa "sosai ma, kofa secondary school bata gama ba "to sai me? "Sai bakomi mr. luv a cikin kallo d'aya, murmushi mai sauti ya saki "zanci gidanku ne yaro "uhm 2nd Abba sannu.

Direct gaban mirror ta isa ta zame after dress d'in data sanya kafinta fito warta tana qarewa kayan jikinta kallo, T-shirt ce mai dogon hannu amma ta kamata sosai sai sket wanda bai gama kai gwaiwarta ba, tsaki taja tace "shegen kallon qurillansa har yagano kayan nan ajikina, ta kuma jan tsaki ta koma bakin bed ta zauna ta dafe kanta.
"Uncle kazo inji labarin wannan mutumin da zuciyata take fad'awa halin firgici duk sanda tayi arba dashi.

Qamshin turarensa tajiyo daf da ita, ta juya cikin zumud'i sai kuma taga wayam ta tura baki cikin shagwaba tace "haba uncle minayi maka karage zuwamin yanzu, alhalin kasan ina buqatan bayanai masu yawa atare da kai, to Allah nikam mun kwance amintan daga yau.

"Mai babban suna tashi kije umminki tana jiranki a madafi. "Banzuwa ni sai ka sanar dani labarin wad'ancan mazajen musamman Ali. "To zan sanar dake ko mai amma bayan zuba, ciki shagwaba tace "uhmm don Allah dai uncle kafad'amin yanzu.

"Auta ina kike ne? "Gani ummi "oya zo ki yima Hindu dambu su Haydar zasu tafi mata da shi donka ki hamzarta ki gama akan lokaci komi na had'insa yana kitchen zogalen ne yanzu Audu zai d'ebo na gyara miki "to ummi gani nan zuwa.

Koda ta fito parlor n ko kallon inda suke zaune bata yiba amma tanaji ajikinta kallonta sukeyi.

"Bros gafa ta can ta fito, yimaza kabita kasoma kafa gabnatinka tun yanzu "kai fa d'an air ne Hammed, kai haka kayi sanda ka soma son Najiba, ina ce aji kayi taja har yanzu kaqi bada kai bori ya hau.

"Kam bala'i!! Ya haydar nine nake son wannan 'yar buhun yarinyan? mai shegen yawon bin club kamar wanda iyalan sarkin aljannun ibilisai su kayiwa fitsari akai.

Murmushi mai sauti Haydar ya saki domin shi bai fiye dariya ba.

"Hameed Allah ya shirya ka kai kam, "Amin tare da kai.
"Yanzu Najiban ce take bin club don tsaban sharrin ka? "Ba sharri sai gaskiya domin ni naganta da idanuna ta shiga club "to kasani wani abu taje amsa "a cikin club d'in? "Eh
"in jikina duka kunne ne bazan taba yarda da zancen ba, don haka Allah kada ka kuma had'ani da mashir maciya yarinyan can "to nabari qanina, dama tsokanarka nakeyi "kaiko bros, Hameed yanunashi da pinger. Duk suka saka dariya.

Cikin 1hr Addawiyya tagama gambun, sai gamshi yake tashi ta juye akula babba ta zuba soyayyiyar man shanun awani roba qarami ta jefa cikin kulan ta saka cikin leda ta d'auka zuwa parlor.

Suna ta hira da ummi tare da Abbie kamar sun saba da juna amma Hameed shine jigon maganar domin Haydar iya kanshi murmushi sai eh ko a'a in ansakoshi ciki.

Ajiyewa tayi zata bar wurin da sauri, Hameed yakira sunarta ta dawo da baya tana kallonshi.

Ya sakar mata murshi ya dubi ummi yace "ummi autanki bata da kirki, kijiba tun zuwarmu gidan nan taqi zama damu ayi hira sai gudunmu takeyi kamar taga dodonni sannan mu kuma bama yi mata haka duk in tazo gidanmu.

"Auta baki kyauta ba kam, ai baqonka Annabinka sabida haka yimaza ki basu hak'uri.

Kamar zata fasa ihu tace "kuyi sorry to, tana fad'an haka ta hau upstairs da sauri har tana hard'ewa da sket d'in atamfan Kayan da ta sanja.

Haydar yabi bayanta da kallo yana murmushi, Hameed ya take mishi qafafu da k'arfi, ya saki ajiyar zuciya da qarfi wanda sai da su Abbie suka kalleshi, ya sauke kanshi qasa cike da kunya sai kuma ya miqe yayiwa su Abbie sallama shima Hameed sallmar yayi musu Abbie ya rakosu har bakin motarsu, saida yaga bacewar motarsu sannan yashigo gida cike da yabon halinsu na kirki.

*mrs j moon*
[1/13, 1:27 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*29*

Tana isa room d'inta ta zube bisa gado tasoma juye2 kamar mai ciwon ciki zuwa can kuma ta miqe da sauri ta sauko qasa, direct kujeran dasuka tashi ta isa ta kwanta ta qamqame jikinta kamar maijin sanyi.

Qasa qasa takejin dariyan uncle takulle idanunta tana tura baki, ahankali take furta "mun bata da kai, baruwa da kai, don haka kayi tafiyar ehe.

Iska taji yatashi fiyy, ta bude idanu tana hararan inda taji motsin tashin iskan.

Tanajin motsin isawar ummi tayi saurin sake kulle eyes d'inta.

"Auta baki da lafiya ne? Da kika kwanta haka kamar maijin sanyi.

Idanunta yana kulle ta amsa"Lafiyata lau ummi, ina dai jin kasala ce "ayya inaga shawara take damunki, bari na tafa miki maganin da Abbienki yazo dashi rannan.

Shiru tayi kar wacce barci ya d'auka, ganin haka ummi ta shafi face d'inta cike da kulawa tace "atashi lafiya autana.

***** Hameed ya dubi Haydar yaja tsuka mara sauti ya maida hankalinshi bisa titi zuwa can yakuma duban Haydar ya tabe baki.

Haydar ya bud'e idanushi dasu lumshe ya zubawa Hameed na 'yan dqiqu sannan yace "inkasake kallona sai na cirema eye 1.

"Uhmm sai kasoma cire naka sannan kadawo nawa, banza yayi mishi tare da komawa ya lafe cikin seat.

"Uhmm ya Haydar kenan wallahi mamakinka ya isheni yau sosai "kamar na mi? Ya tambaye cikin rashin kula.
"Na haukacewar da zuciyanka tayi akan Addawiy, ka koma mara aji, kamar bakaine mata 'yank'walisa da class suke fad'a akan kaba amma kaqi kulasu amma yanzu akaron banza ka mace akan kwaila wacce bata gama cika budurwa ba.

"Hameed! Yakira sunarshi cikin kaushin murya.
"Uhmm my name.

Har yabud'e baki zaiyi magana sai kuma ya koma ya kwanta tare da tura yatsunsa cikin sumar kanshi.

"Uhmm kaga Waziri ba kafi mai abu iko.

"Kallon Hameed yayi cike da son qarin bayani game da maganar shi.

Driving yacigaba dayi yaqi kallo inda Haydar yake balle ya fahinci manufarshi.

Shi kuma miskilanci yahanashi ya tambayeshi, haka yayi ta mai maita kalmar aranshi har suka iso gida.

Hameed direct parlorn Hindu ya wuce yayin da Haydar ya nufi part d'insu.

Yana wanka zuciyarshi tana gargad'inshi akan kada ya afkawa abinda zai tona mishi asirin dake binne wanda dagashi sai mahaliccinsa suka sanda shi, wani kuma shashin ya amsa da ka sota har yakaiku ga aure juna tanan ne zaka tabbatar da zarginka.
Ajiyar zuciya yaja mai qarfi ya furta "lallai ina sonki sosai Rabi'atul Addawiyya, Allah yasa ki soni da gaskiya ki kuma iya riqemin sirrina, Amin.

A parlor ya cimma Hameed ya barrarraje sai kwasan dambu yakeyi, da sauri ya iso ya d'auke plate d'in ya ruga da gudu suka soma zagaje parlorn Hameed yana cewa "ya Ali kabani abincina, shi kuma yana fad'in "anqi badawan, kai da kace mata kwaila sai kaje yanzu wurin balugun wa balagun ta dafama.

Hameed yanaji yana gani Haydar ya cinye dambu ya hana shi, cike dajin haushi yace "zan baka mamaki, don sai na kawo maka wacce za kayi zuban yamu don kyau, cika, diri, sura tare da girma irin ta isassun mata.

"Eh, naji dai, kuma wuce nan, namajo kawai, jeka garin neman qiba ka samo rama.
"Ina ruwanka, koma mizan samo "kai kaga tafiyata in duba tsohuwata hajja, yafice d'auke da empty plate d'in dambun.

Afusace Hameed ya fito zuwa part d'in Hindu domin samo wani dambun sabida sosai yayi mishi dad'i.

*** Cikin barci taji ana jan mata baki ta bud'e idanunta ta saukesu bisa Annur wanda yake ta bangala mata dariya, d'aukanshi tayi cike da murna tace "my handsome ina miminka? "Yala ummi daki.
Dariya tasaka mishi ta ja kumatunshi "kai Abbiena wai sai yaushe zaka iya magana ne? gashi har kaciki 2yrs.

Cikin shirmen yarinta ya amsa "yau aunty adda, dariya ta kuma sawa tamiqe sabe dashi tanufi upstairs.

"Adda Salma naga kin qara haskene kamar tasa... "Qaniyarki Addawiy, baki da kunya ko? Cikin dariya ta amsa "ni kam ke da kunya tunda ko kallon maza ban iya d'aga eyes d'ina inyishi sai dai su suyi ta kallo na kamar sun sami tv.

"Oh my Addawiy soyayya kika soma kenan, oya gist me , tana karkad'e kunninta.

Cike dajin kunyar maganar Addawiyya ta juya mata baya tace "nikam Allah ya tsarene fad'awa wahala.

Kyal kyalewa da dariya Salma tayi tana cew "very soon wahala zatayi miki kamun kazar kuku yarinya.

"Bakinki ya sari legs d'in mijinki ya daina zuwa kallon ball.
Chapter 17 · 0% Book details