← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 38

Sashe 2

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hararan wasa ummi ta dokawa Abbi tana k'iftamishi idanu. Dariya Addawiyya tasa tana cewa "haramunne k'ifce da yafice da kuma zund'e haka mai k'awa'idi yafad'a ko Abbi? Gyad'a mata kai yayi yana dariya. Daquwa ummi tayi mata "kagamin ja'ira dai wato karatun naki akaina zai sauka ko auta? Ta kama baki tare daja baya tace "nop ummi kawai ina dai tunasar dake ne da kibari kada... make bakinta Salma tayi tahanata fad'an abinda tayi niyya aiko wani tsalle ta daka ta cukumeta ummi ta mik'e da hanzari tasoma jan Addawiyya amma ta maqale jikin Salma kamar mayen qarfe Abbi ya kishin gid'a yana kallansu yana murmushi da kyat ummi tayi nasaran janye Addawiyya yayin da Salma take hawaye tana liliya qirjinta sabida a nononta Addawiyya ta manna mata cizo.

"Zonan Rabi'atu, cewar Abbi. Ta isa gabansa ta durk'usa ta sunkuyar da kanta k'asa.

Kunninta yaja da kyarfi ta kwalla qara yace "daga yau nakuma ganin kina dambe da yayarki sai na cire miki kunni, kinaji na ko? "Eh Abbi, bazan qaraba insha Allahu. Sakin kunnin nata yayi yace "kutafi ku d'auko littafanmu kuzo ku biyamin k'arin danayi muku jiya in kun iya sai mu d'ora.

Atare suka amsa da "to Abbi.

Suna fita ummi ta dubi mijinta tace "amma malam baka ganin lamarin auta abin abincika ne? "Kamar ya? "Gani nayi tafiye jan fad'a ga k'arfi kamar shari'a. Dariya Abbi yasa "amma kindai san duk qarfinta Salma maketa takeyi ko? "Eh hkane kuma "to kibar wani tunani can naki mara tushe, kawai kicigaba dayi musu addu'a shi yafi. "Tam malam Allah ya shirya manasu tare dabasu kariya cikin amincin ubangiji "Amin.

Acan d'akinsu kuwa fad'ane ya kaure a tsakaninsu sakamakon dariyan da Addawiyya tayi ta sheqawa Salma tana liliya qirjinta irin yarda Salma takeyi aiko cikin fushi Salma ta cukkumeta ta d'aga ta buga a bisa katifarsu tabita ta danne ta zauna bisa ruwan cikinta tana cewa wallahi sai na rama a wad'annan naniqak'k'un nonuwan naki, duk qoqarin Addawiyya naganin ta hana Salma rama cizonta ta kasa sabida k'arfin ba d'aya ba.

Abbi kam ganin sun dad'e basu fito ba yasa ya miqe yace da ummi in sunzo su biya wurinki inna dawo daga ta'aziyyan wad'anda rafin cigogo ta cinye jiya wurin wasan banznsu sai na k'ara musu "tam Allah yadawo da kai lafiya su kuma Allah yaji k'ansu "Amin.

Da kuka ta shigo kanta bako d'an kwali, ta zube jikin ummi ta cire riganta ta d'ago tana nunawa ummi qirjinta wanda yasoma cika da dukiyan fulani.

Idanu waje ummi take duban inda shaidan haqora suka fito a samar fatan, waya cije ki? "Adda ce. "To maida riganki ta maida tana share hawaye alokacin Salma ta shigo d'auke a littansu na karatun addini.

"Salma wani irin wasan banza ne wannan zaki bud'e baki kamar karya ki cijemin auta a inda ruhinta yake? "Ummi ita tasoma ai, kallafa kigani ta d'aga riganta bako kunya tana nunawa ummi kan nononta inda Addawiyya ta cijeta d'azun, wanda suka gama nuna sun kuma cika qirjin dam.

da sauri ummi ta rubemata rigan tana hararanta "amma dai kekam anyi babban banza yanzu don ta cijeki sai ki rama don tsaban rashin wayau kuma sai kizo kina nuna nunamin wanda tayo miki? "Ummi to bagashinan itama ta nuna miki nataba.
"Naboni ni zuwaira ashe dai har yanzu bakiyi hankaliba Salamatu? Shin ke da auta shekarunku 1 ne? To Allah kifita idanuna tun banyi rawar banjo akanki ba tam.

Dariya Addawiyya take tayi mata k'asa2 tare da kwalo ita dai sai cika takeyi tana batsewa, tana hararan Addawiyya.

zuwa can ummi ta umurcesu dasu matso suyi karatunsu.bayan sun kammala ta yi musu nasiha dasu bar fad'a da juna balle har yakaisu ga cizo.

Bayan sallar azuhur suka zauna cin abincin rana dambun zogale ne wanda yaji gyada da soyayen man kad'e gami da man shanu yayi laushi sosai, sai damammiyar fura agefensu wacce taji nonon shanu mai kyau da gard'i.

K'asa k'asa Addawiyya take magana "Adda jiya naga abin mamaki atushen itaciyar tumfafiyan can "uhmm mi kika gani awurin? sarkin iya labari. Qasa ta k'arayi da muryanta tace "karatun Al-qur'anin karim naji anayi wanda yasa na zauna ina saurare cike da nishad'i, kuma abin mamaki wurin yacika da k'amshin turare mai dad'in shak'a, kai ai jiya kwanar mamaki nayi donma Abbi yabiyo wurin yakatsemin jin dad'ina.

Quri Salma tayi mata da idanu tana saurarenta ganin haka Addawiyya tacigaba "kuma karatun cikin suratul isla'i akeyi, bakiji yarda ake fidda tajwid ba, kai naso naji qarshen karatun nan kam.

Da gudu Salma tatashi ta nufi bukkan dasu Abbi suke ta labe abayan ummi tana maida numfashi. Atare suka ce "lafiya kuwa? "Babu lafiya kam Abbi, ummi Addawiy tayi gamo.

Gamo!!! Kuma? Sai kuma suka fice da sauri, turus sukayi suna kallon wacce akace tayi gamo tana zaune tana cin dambunta tana korawa da fura cikin kwanciyar hankali.

Tsaki suka ja suka koma cikin bukkansu Salma zata biyosu ummi ta daka mata tsawa ta dawo da baya tana kallon Addawiyya wacce tayi kamar bata gantaba. Cikin sanyin jiki tazo ta zauna ta cigaba da cin dambunta.

"Uhmm Adda Salma kenan gabaki d'ayanki sai ahankaki domin ina zargin lissafinki yagoce shi yasa baki iya tabuka komi amakaranatar da Aunty hindu ta saki, inaganima cireki zatayi ayi miki aure tunda dama shi kike buqata acikin ranki.

Banza Salma tayi mata. Addawiyya ta sheqe da dariya ta taskama cinyar Salma duka tanagani zata rama tamiqe suka soma tsere har saida suka gaji duk suka zube aqasa suna maida numfashi.

Adda kitashi kije kisanja kaya kada yaya mushaffahu ya iso yaganki cikin wad'anan fingilallun kayan.
"Banson iskanci Addawiy yaushe kikaji labarin zaizo?

"To kada kibi shawarata yarinya zauna tambayata, inyazo kyaji kunyarki ke 1 nikam kinga tafiyata tafice zuwa bayan bukkokinsu tana waqen alami abbiyad wa ahadar.

Shiru Salma tayi tana tunanin anya Addawiyya ita kad'aice kuwa?

Sallamar mushaffahu ya katse mata tunani da gudu ta yi baya inda Addawiyya take batre da ta sami damar amsa mish sallamar da yayi ba.

"Addawiy yazo wallahi yazo zomuje kiganshi ta fizgo mata hannu, yana cikin bukkan su Abbi suka shigo suka zube agabanshi atare suka gaisheshi ya masa cike da walwala.

" 'yar qauye tashi kikawomin ruwa qishi nakeji, dariya Addawiyya tasa nata kallon Salma tace cikin harshen fulatanci "tashi kisamowa saurayinki abinda zai jiqa maqoshinshi ya kwaso rana, harara ta dalla mata tare da miqewa ta fice.

"dad'ina dake Rabi'a gulma wallahi, yanzu sabida kinsan banaji abinda kike cewa shine zaki maidani bare ko? Tana dariya tace "a'a kad'o bawanmu fulani. Dariya su Abbi suka sa mata.

Washe gari mushaffahu ya wuce tare da Salma wai zata raka mama kano bikin qanninta, suka bar Addawiyya cikin kewa mara misaltuwa.

Wanki ta yini yi tayi guga domin itama gobe zata koma makaranta.
Sai dai duk abinsa takeyi cikin sanyi jiki takeyi aiwatar dashi wanda har ummi saida ta lura da rashin karsashinta kuma tayi mata tambayar duniya nan taqi cewa komi sai dai tabi ummin da idanu ko kuma tace mi kikagani ne ummi? Ganin taqi fadamata damuwarta sai tafita harkata tacigaba kintsa mata abubuwan dazata wuce makaranta da su.

Dayammaci ummi tayi mata sallam zata leqa gidan biki a kusa dasu.

Bayan tagama kwashe tuwon da ummi ta tuqa musu ta adana tare da miyar sai taje tayo wanka ta dawo ta zauna qasan bishiyar mango tana bitan wani English novel sabida arayuwarta tana makuqar son labarai musanman na hikayan zamanin mutanen da.

K'awayentane suka shigo kowacce taci d'amara kamar 'yan kokuwa da kallo tabisu tana tabe baki tana kallonsu sama da qasa.

"Dalla malama miye kike kallanmu kamar kinga kashi, kodon kina boko mu kuma bamayi, shine zaki samu agaba da wannan kallon rainin wayau d'in irin na 'yan hanyar jahannama?

Banza Addawiyya tayiwa yariyar mai suna haule.

"Ke kam haule kinboni kam, ace ana yawan gudun bikinki amma baki bar masifaba, kai Allah yayi wadaran naka ya lalace.

"Surare kifita harkata wallahi ko yanzu muware qashi mu kwashi 'yan kallo.

Wani dariya Addawiyya ta kwashe dashi tana nuna haule wacce taci kyalliya kamar birin wasa wai itanan Amarya.

"Auh wai bikinki dama ummi tace zata leqa wai? Tayi wani marmar da idanu kamar kura ta amsa "ya wuce wai, amma wanke wanken kayanna zata gani, biki kam sainan da jibi kuma yanzu munzo ne kitashi mutafi yawon gudu tunda jiya umminki ta hanaki binmu kasuwa sayayya.

"Yawon gudu kuma? Ni Addawiyya inbiku? Taf ba inda zani kam, ko kunmanta agarin wannan yawonne Adda Salma tarasa budurcinta? Shiru sukayi zuwa can haule tace "ayya Addawiy ai bazamuyi nisaba iyakarmu tungan jauro kuma ai yanzu anhana mazajen danne 'yanmatan Amare sannan kuma wa'yanda sukayi k'aurin suna akan aikata iskanci kwanaki sunyi sata abirni ankamasu yanzu haka suna gidan kaso, don haka ba dan niba don Allah kitaso muje kiqara ganin inda kika manata.

Kamar baza tajeba sai kuma ta miqe ta maida littafanta d'aki ta kulle qofofin bukkokinsu ta zira wani flat shoes tare da qaramin gyale tace "tam kumuje amma wallahi kowa sai ta kwance wannan d'amaran da tasha a k'uqunta kamar wasu bibrai.

Dariya suka saka mata suna cewa "sai 'yar birni kuma 'yar boko. Ita dai murmushi take musu agefe d'aya kuma gabanta yatsananta fad'uwa sannan ga tsoron yarda zasu kwashe da ummi intadawo bata gantaba.

Haka suka miqa suna ta wak'e2nsu irinta al'adarsu insun fita irin wannan wayon dasuke mishi laqabi da yawon gudun amarci.

Shidai wannan yawo anayinsa ne kafin d'aurin aure da kwana biyu kuma mazane abokan ango zasubi bayan 'yanmata sukuma da sungansu sai suyi ta gudu suna ihu har mazan suyi nasaran kamo Amaryan acikinsu wanda kafin sukawota gida sai sun gama latse mata nonuwa wasuma har fad'e suna mata amma anfi samun hakan in amaryan bata son mijin to in sun kamota sai suba mijin yayi abinda yaso da ita wai nufinsu dole zaisa ta zauna dashi kuma ta soshi tunda yayaga mata munta.
To kuma wanj zubin har 'yanmatan wasu suke bi su danne a irin hakane Salma yayar Addawiyya tafita yawon gudun qawarta akayi mata aika aika to tundaga lokacim ummi da Abbi suka soke wannan baqar yawon akan 'ya'yansu wanda bakomi cikinshi sai tanbad'a.
Wai acewarsu al'adace.

*Nace kodai jahilci*
Chapter 2 · 0% Book details