← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 38

Sashe 32

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ta miqa don tabata ummul bait amma sai ta noqe ta wuceta abinda yayi mugun jefata cikin jin kunya ta sauke kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta.

Azuciye Hameed yazo ya fincike yarinyar ya iso inda Addawiyya take tsaye ya miqa mata ita tare da cewa "ni Hameed indai nine mahaifin ummul to daga yau nabaki ita kyauta na har abada, yanzu kece uwarta kuma banson kiyimin musu akai indai na isa nayi miki kyau ki amsa.

Tsit wurin ya d'auka kamar mutuwace ta gifta.

Muryan Hajja ya katse shirun "Hamidu lallai wannan kyauta ta faran tamin rai sosai kuma Rabi'atu ta amsa ta gode ainun Allah yata yata riqo.
"Amin mutanen wurin suka amsa, ta d'ora sai dai ina roqon abarta zuwa sanda za'a yayeta sai ta amshi kayanta.
"Hakan zance Hajja, cewar Haydar.
Hameed ya jinjina kai ya amsa "tam ai abin kamar gobe ne in muna da rai.

Cike da murna Addawiyya ta d'aga ummul sama tace "Allah ya albarkaci rayuwarki 'yata, ina sonki sosai, jama'a kushaida.

Sai addu'ar Allah tayata riqo ake tayi mata, yayin da zuhuriyya tuni tabar wuri zuciyarta cike da jin zafin mulkin mallakan da Hameed yayi mata batare da shawaranta ba.

Daren ranar Haydar yazo mata da wani baqon lamari wanda yagigi tata, domin daga romances sai ya zarce, tuntana d'auka lamarin wasane sai ga abu ya tabbata lafiya tasamu gareshi.

Taso ta d'aure amma ta kasa sai kawai ta saka mishi kuka tana bashi haquri amma ina Haydar yayi nisa bayajin kira, ya fad'a wata duniya da bai taba zaton da ita ba.

Koda yadawo natsuwarshi sai kawai ya fashe da kuka yana jera godiyarsa ga Allah subbahanahu wata ala da ya jarabbeshi da lalura kuma gashi ya yaye mishi alokacin dabaiyi zatoba.

Shi ya taimaka mata ta gyara jikinta sannan ya d'aukota ya shifed'e bayan ya fidda bedsheet d'in daya baci ya sanja wani, tsarkake jikinsa yayi shima ya zo ya rungumeta yasoma magana "Rabi'a Allah yasa kigama da iyayenki lafiya, Allah yayi albarka arayuwarki, Allah yacika miki dukkannin burukanki na alkhairi Allah yasa murayu da juna in da rabon haka, Allah yasa kece matata cikin aljanna, wallahi ina sonki Addawiyya, bana son inbarki, Allah yasa sanda zamu koma ga mahaliccinmu a tare da juna za'a zare ranmu.
Can qasar maqoshi ta amsa "Amin.

Bayan sun sallaci subahi Haydar yace mata kansa yana ciwo abu kamar wasa sai gashi yasoma fizge fizge duk tabi ta rud'e.

Number Hameed ta kira qara biyu yayi ya d'auka cikin kuka tace "Hameed kazo ya Ali zai tafi yabarni, ai bai gama jin metace ba yafito da gudu zuhuriyya tana tambayarshi bai ma san tanayi ba.

Tai makon gaggawa yasoma bashi har numfashinsa ya dawo normal sannan ya d'aukeshi suka nufi hospital dashi.

Addawiyya tun tana kuka da hawaye har ya komo hawayen ya qafe, ga jikinta da batajin dad'isa sam, abu dai duk yataru yayi mata yawa, takasa zaune ta kasa tsaye sai kai kawo takeyi.
Hailala tare da istiggifari take ta ambata afili, addu'ar Allah yabashi lafiya kuwa tayisa har tabawa uku lada, cikin 'yan awanni har tayi wani mugun rama.

*mrs j moon*
[1/31, 4:54 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*44*

Zaune take bisa kujeran roba a gaba gadon dayake kwance ta sarqe hannunta da nashi tare da kwantar da kanta samar qirjinsa idanunta lumshe, fatarsu duk ya kumbura da alama barci ne ya d'auketa ahakan.

Can daga d'an nesa take hangoshi cikin shigar sutura masu kyau tare da kyalkyali har suna kashe idanu don walqiyarsu.

Tafiya tasomayi don ta isa wurinsa amma sai taga yana mata nisa sai ta soma gudu gudu kad'an nanma dai takasa isa inda yake sai kawai ta soma kuka tana kiranshi tare da falfalawa da matsanancin gudu, yana dai ta cigaba dayi mata nisa tare da yi mata murmushi yana kuma d'aga mata hannu ita kam sai gudu takeyi don ta isa wurinshi amma sai taga kamar ana janta baya ahaka har ya bacewa ganinta ta zubbe bisa guiwoyinta a filin mai cike da ciyayi kwance lufluf tare da kalla mishi kira da qarfi "Ya Alee!!!!!.

Kiran da yayi amsa kuwwa cikin room d'in tare da haddasa farkawanshi a firgice sabida amsa kuwwan da sautin yayi cikin kunninsa, bakinsa d'auke da salati.

Shafa kanta yayi ahankali tare da kiran sunarta, tabud'e idanunta wanda suke cike da hawaye sai sauka sukeyi bisa quncinta.

Hannu ya kai yasoma share mata hawayen tare da girgiza mata kai face d'insa cike da annuri.

Kallonsa takeyi kamar yau tasoma ganinsa sabida sai taga yaqara mata kyau sosai kamar bashine aka kawo rai a hannun Allah ba, agefe 1 kuma zuciyarta cike take taf da mamakin mufarkin da tagama yanzu.
Shin ko me hakan ke mufi?
" beauty bani ruwa insha maqoshina kamar zai kama da wuta.
Maganarshi ta katse mata tunanin data afka ciki.

Jikinta ba kwari ta motsa domin d'auko mishi ruwan roba.
Tana shirin bashi ruwan kenan Hameed ya shigo tare dasu Abba.

Hameed yayi hanzarin cewa "A'a Addawiyya kar kibashi bari na dubashi tukunna.

Komawa tayi ta zauna ahankali tana rintse idanu sabida zafin datakeji kad'an2 aqasarta har yanzu sai kuma tayi saurin zamewa ta sunkuya ta gaishe da Abba tare da aunty Hindu suka amsa suna tambayarta mai jiki "yaji sauqi ta amsa.

Hameed ya dubashi tare zare mishi drip d'in sannan ya bashi ruwan da kanshi.
Ya tambayeshi "yanzu ina yake mishi ciwo? Ya amsa "ba ko ina, naji sauqi sosai.

"To Allah ya qara lafiya, cewar Abba suka amsa "Amin.

Aunty Hindu ta had'a mishi tea sabida koda zaiji karfin jikinsa.

Ita take bashi abaki fitar Abba da Hameed yasa ta miqawa Addawiyya ta bashi ba musu ta amsa tasoma bashi har yasha rabi sanna yace "haskena shanye sauran don nasan kema bakici komi gashi kuma bakya da lafiya.

"Mike damun autan ummin? Hindu ta tambayeshi.
Murmushin qarfin hali yayi sannan yace "aunty tana buqatar kulawa dan Allah kitaimakeni tasamu.

Had'e rai tayi tana zabga mishi harara ya saki 'yar dariya kad'an tare da janyota jikinsa tayi sauri tashi ganin haka Hindu ta fice d'akin yarage daga ita sai shi.

"Haskena wurin yabaryi miki zafi ko? Banza tayi mishi, ya matse ta ta saki 'yar qara, ya sake cewa "yabari ko kuwa? "Eh, yabari "da gaske? "Eh "to madallah sannu kinji na wahalar dake jiya ko?
Kauda kanta tayi gefe sannan tace "Ya Alee kabar yawan surutu kasan kana buqatar hutu inji doctor ko?

"Uhmm beauty to nayi shiru amma d'an matsamin qafafuna jinsu nake kamar ba nawaba.
Cike da tausayawa tasoma matsa mishi qafafun shi kuma yayi mata quri da idanu yana aikin kallonta bako qiftawa.

Suna a haka zugan su ummie suka shigo, tayi saurin komawa samar kujera ta zauna suka kayi tayi masa ya jiki yana amsawa cike da murna. Ita kuma ta gaishe dasu cikin ladabi.

Yafito aunty Hindu yayi da hannu ta matso daf da bakinsa ganin yana tunata yasa tayi saurin barin d'akin sabida tasan maganar d'azunne bai bariba.

Koda tafito gefe ta samu ta zauna tazuba uban tagumi.

Hameed ya qaraso wurin ya zauna gefenta yace "yakamata ki cire damuwa aranki haka nan ko don ingantuwan lafiyarki.

"Uhmm kawai tace.
Ya gyara zama yana qare mata kallo cike da mamaki, donmin ya kauda zarginsa sai yace "amma kamar qafafunki sunayi miki ciwo ko?
Kallons tayi tama rasa mizatace mishi.

"Nagano hakan ne tayarda kike tafiya kamar ba dai dai ba.

Kauda fuskanta tayi cike da yabawa rashin kunyarshi wato amatsayinsa na doctor yariga da tuni ya gano komi kenan amma don tsaban rainin wayau tare da fitsara shine zai zo yasata agaba da tambayar wofi.

"Kaga malam banason sharhi, ni lafiyata lau don haka sai ka barni naji da abinda ke damuna.

"Uhmm "aunty Addawiyya kenan daga zan tai makeki sai ki hauni da masifa, to Allah yabaki lafiya amma dai ina cikin mamakin yar da abin yakasance haka alhalin kun wuce 3yrs da aure yanzu.

Tsaki taja tare da miqewa tayi gaba tana qoqarin dai daita tafiyarta tun kafin wasu sa'idanawar su gani.

Murmushi yayi tare da shafan sajensa ya furta "kin canci asoki da girmamaki, ina tayaka murna brother da samun 'yar albarka.

Tana shiga Hindu ta kama hannunta tayi qasa da murya "autan ummi mike damunki Haydar yaketa jaddadamin cewa in baki kulawa bakyajin dad'i?

Kallon inda yake kwance tayi yako sakar mata murmushi ta wulla mishi harara tareda tura baki ya yafitota ta kaqe kafad'a.

Ita dai Hindu sai kallon ikon Allah takeyi, ganin sunqi daina maganar kuramen sai taja hanunta zuwa bakin gadon tana mai cewa "ku sanar dani ko laulayin ciki takeyi dama naga tayi rama ta kuma qara haske.

Cike da shagwaba tace "aunty abar kaza cikin gashinta kawai amma dai nasan ni banda komi.

"To ai shikenan tunda bakyason musani muyi addu'a akai.

Zama tayi gefen gadon taqi kuma cewa himdu komi.

"Kaiko Ya Alee burinka ka tona mana sirri ko? "A'a haskena, inadai son abaki kulawa ne wanda rashin layar nan tahana in baki "to bana so nace, kabari kana sani jin kunya "tam nabari hajiyata, d'an murmushi tayi tana jifarshi da hararan wasa.

Kwanaki biyun da yayi 'yan uwa da abokan arziki sai tururuwar zuwa dubashi suketayi kuma alhdulillah yasami lafiya sosai.

A yammacin daya cika kwanaki hud'u yana zaune ya d'ora qafafunsa bisa cinyoyin Addawiyya wacce take yanke mishi farce da cut nail hira sukeyi qasa qasa xuwa can ya ja numfashi mai qarfi tayi saurin dubashi ya sakar mata lallausan murmushi yace "yanzu ace in na mutu wazaki aura?

Wani kallo tacilla mishi fuska ahad'e tace "banson zancen mutuwanan fa ya Alee
"uhmm heart beat ai kam zancen mutuwa tazama dole sabida ko kana so ko baka so dole sai ka d'and'ani d'acinta don haka amsa min tambayata kawai.

Cike da fushi ta miqe tana cewa "daga kai nagama aure don haka sai ka daina kiran mutuwa in kuma kaqi Allah yau bazan kwana da kaiba, gidan Abbie zan tafi sai da safe nadawo.

A'a zo kusa dani matata, bazan sake maganar ba.

Matsawa tayi ya sun kuyo daf da kunninta yafad'a mata wani magana wanda yasa ta zabura ta ja baya sai kuma tafice tana zubar hawaye.
Chapter 32 · 0% Book details