← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanxu haka zakuyimin? Duk kugudu kubarni da kewarku? Abida tace dasu cikin laushin murya.
Alawiyya tace da ita "Mommy Abida ba haka bane dole ce ta samu zamu bar school d'in duk kuwa da son da muke mata, dama gatanmu Allah kuma Addawiyya ce idanunmu sabida tun muna js 1 take kula damu domin duk abinda zai cutar damu zata fad'amana kada muje wurin sannan ita d'in haskenmu ce gashi ta tafi tabarmu don haka agaskiya bama mu iya zama bama ganinta ba "tabbas hake sis bazamu iya jure rashinta ba a school d'innan sannan kuma ga wannan masifar datake tashe yanzu ta mafiya, kawai atsotse mawa mutum jini abanza da wofi, kai ni gobema zan bar school d'innan domin mufarkin Addawiyya yana bani tsoro sabida yakan zama gaskiya.
Shiru Abida tayi tana sauraren yaran, kuma tagaza tofa ko kalma 1 cikin zancen dasuke mata illama wani mugun sanyi da jikinta yayi, lallai da alamun zancen daughter zai zama gaskiya sabida najima ina zargin shakira tana cikin qunqiyan matsafa. Azuciyanta take zancen zuwa can taja numfashi ta dubi yaran tace "a'a Alawiyya kidai bari zuwa ayi hutu tunda kinga kun soma text sai in kun tafi kuyi zamanku domin nima nasoma tsorata da lamarin na yarda ake mutuwa akai akai a makarantar bakuma ga d'abibai kad'aiba harda wasu cikin malaman musanman 'yan bautan qasama"tam mommy Allah ya kaimu yakuma qara tsaremu da sharrin dukkanin wabi abu mai cutarwa ta amsa "Amin. Sannan ta jasu suka nufi masallaci don gabatar da sallar azuhur.

**** Addawiyya tunda suka fice get d'in makarantar ta kwantar da kanta acinyar ummi ta runtse idanu ta ahaka har barci ya d'auketa.

Bayan 1hr ta farka afirgice tana haki kamar wacce tayi gudu. Ummi ta riqeta gam tasoma tofa mata addu'o'i har ta sami nutsuwa ta koma ta kwanta tana danqe da gefen cikinta sai zufa takeyi, Abbie wanda yake zaune gefen driver ya juyo yace "Rabi'atu mike daminki? Dan na lura tun zuwanmu bakya cikin yanayi mai kyau.

"Bakomi Abbie sai dai ina son kacigaba dayimin addu'an nan ta kariya daga sharrin shed'anun mutane da aljannu "to Allah yayi mana katangan qarfe dasu, ummi ta amsa da "Amin.

Tafiyan 2hrs yakawosu cikin garin kwantagora, suna isowa suka cimma salma tsaye abakin get da alama su take tsumaye.

Suna fitowa Da gudu ta isa ta rungume ummi tana ihu kamar wata qaramar yarinya.
Addawiyya ta tureta gefe tace "angirma ba saiti sai tarin shashanci, dundu ta dage ta dimawa Addawiyya abaya wanda sai yasa Addawiyya ta durqushe awurin ta saki wani razananniyar ihu tare da dafe gefen cikinta tana kiran "ummi cikina zan mutu wayyo!!!
Da sauri Abbie ya kamata ya d'agata tsaye ummi ta janye hannun data dafe cikin dashi saiga jini har ya jiqa farar rigan makarantar datake yanye dashi.
Cikim gigita Salma taja baya tana cewa "yau na bani daga dukan baya sai jini a ciki? Sai kuma ta saki kuka "wallahi ummi bani naji mata ciwonba da abinta tazo dama can. Wani tsawa ummi ta daka mata yasa tayi shiru hannunta dafe da bakinta tana matsan kwalla.

Ganin Salma tayi iya bakin qoqarinta don ganin jinin ya tsaya amma ta kasa gashi Addawiyya tasoma galabaita yasa aka d'auketa zuwa hospital.

Cikin hanzari suka amsheta suna tambayar abinda yasameta.

Abu fa yayi mugun firgita doctors sosai domin duk iya dibaransu nagnin jinin ya bar zuba amma yaqi tsayawa ga ciwo ba wani mai yawaba domin d'an yankane kad'an kamar na ya kushi to shine yake fitar da jini haka.

Cirko cirko sukayi anrasa wanda zai iya fita yasanar da su Abbi halin da ake ciki.

K'uri tayima gefen damarta tana kallo bako k'iftawa, shi kuwa sai matsowa yakeyi fuskansa ahad'e babu alamar fara'an nan data sanshi dashi, har ya iso gabanta ya miqa hannunsa ya shafa wurin ciwon tare da tofa addu'a atake jinin ya d'auke doctors sunagin haka suka soma hamdalah shi kuwa yaja baya ya sakar mata murmushi tare da hura mata iskan bakinsa atake taja wani numfashi ta lumshe idanunta bakinta d'auke da kalmar "thank you uncle.
Jinijina kansa yayi yazama farin haske ya bace.

Doctors sukayi dressing d'in wurin tare da yi mata allura domin tasami hutu.

**** cikin zumud'i ta kama hannunshi sai kuma tayi saurin saki tana yamutsa fuska, dariya yasaki yace "sanyi ko? Kai ta gyada mishi, yakuma darawa "mai babban suna ya jikin naki? Saida ta shafa gefen cikin sannan tace "uhmm na warke ai, " to madallah.

"Amma uncle kana ina kabari kuraye suka kusa halakani? "Affuwan mai babban suna nayi tafiyane yazomin abazata, naraka kakana garin makka ne domin lokacin shiga bautan dazai sake sabon jiki yayi.
"Jikin mi? Ta tambayeshi cike da mamaki.
"Mu zauna sai inbaki labarin yarda zakifi fahimta. Zama sukayi samar wasu kujeru masu kama da azurfa.
Ya kafeshi da idanu tace "uncle bani insha wata qila ba'arasa ilimi ciki.
"Tam mai babban suna yanzu kuwa, mudai jinsin musulman junnu idan mun kai shekaru d'ari hud'u aduniya lakacin mun tsufa sosai sai mutafi qasa mai tsarki cikin kogon dutse mu d'aura niyyar azumi na kwanaki talatin cif ba ci ba sha sai muyi ta sallah tare da zikiri har na tsawon kwani, idan mun cika sai musha zamzam da dabino sai mu fito wajen kogon muyi girgiza muna mai miqa godiya ga Alllah mad'aukakon sarki wanda baya barci bare gyangyad'i, akake kuwa Allah sai yamaidamu abinda muka qudurta acinkin zuciyarmu ta yarda muke son kasan cewa wasu matasa suke komawa wasu kuma dattijai sai mudawo ga 'yan uwanmu cikin aminci mu cigaba da rayuwarmu kamar da.

"Tabd'ijan amma lamarinku yana da ban mamako uncle wato haka zakuyi tayi kenan har izuwa ranar tashin qiyama? "Eh mai babban suna "to yanzu kai sau nawa kayi girgizan? Dariya yayi mata ya miqe yace "dawo duniyarku ga danginkinan sun cika d'akin suna jiran farka wanki ya soma ja dabaya yanayin sama tare da d'aga mata hannu har ya bacewa ganita cikin cloud.

**** tabud'e idanun tayi arba da su ummi, Abbi, mama, Abba, aunty hindu, mushaffa'u tare da Salma duk sunyi tsuru cike da jimami.
Suna ganin farkawanta sukayo kanta suna ta jera mata sannu, kai take gyad'a musu cike da murmushi, shigowar doctor yasa suka bashi wuri ya dubata tare da tambayarta inake mata ciwo yanzu ta amsa "banajin ciwon komi yanzu "Alhamdulillah ya furta sanna ya juyo yace dasu Abbi zuwa magariba zamu sallameta bayan ta amsa alluranta na marece amma yanzu abata abu mai ruwa ta sha kamar tea mai d'umi dai dai ba mai zafi sosai ba, daga haka ya fice.

Hundu ce take bata tea d'in tana mara magana qasa qasa ita kam sai dariya takeyi mai sauti zuwa can ta kalli inda Salma take zaune tazuba uban tagumi ta yafitota da hannu ta taso ta iso ta tsaya gefenta idanunta cike da hawaye tace "ayya Addawiy na kiyi hakuri wallahi bansan zanji miki ciwo haka ba "mintsilin cinyarta tayi cike da tsokana tace "ke nifa da ciwona nazo dama don haka kibar kukan hakanan matar bishiyar baure uwar arhan zubar ruwa.

Duk aka dariya, mushaffa'u ya amsa "matar sarakinta ne oga Muhammad mushaffa'u.
Mama tayi masa daquwa yasoke kansa yana murmushi yafice waje Salma tabi bayansa Addawiyya ta ware murya tace "yayi matar mai abocin azumin lada badon ya shiryaba, da sauri taqarasa ficewa batare da ta kula taba.

Bayan magarib aka sallameta suka nufo gida cike da annashuwa naganin yarda Addawiyya tadawo normal.

Aunty hindu ta had'a mata ruwan wanka tajata zuwa toilet ta tsareta da idanu tace "oya dube in miki wanka, zare idanu tayi zana shirin yin magana ta tareta "ko har kingirman da kika wuce in wanke kine? Tura baki tayi tasoma buga qafa "Allah ni dai ban ceba amma nikam kifita zan iya da kaina don ba'inda kemin ciwo yanzu, "ok autan ummi dai ta girma tana boyemin sirrinta, dasauri ta sa hannu ta rufe fuskanta wai taji kunyar maganar.

Washe gari bayan sungama break fast Abbi ya dubi Addawiyya yace "Rabi'a wacece shakiran da kike ta kira sanda jini yake zuba miki jiya? Gyara zamanta tayi tace "itace wacce take bani tsoro acikin barcina kullum tun a cikin daren dana koma makaranta.... "To miye had'inki da ita autan ummi? Shiru tayi kamar bazatace komiba sai kuma zuwa can taja ajiyar zuciya ta soma da cewa....

*mrs j moon*
[1/2, 12:07 AM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*This page is for you: Haermeebrah, Mmn Ihsan(yaya sadiya), Aisha Umar, Hauwa'u Gombe, Imranat, tare da my lovely sis Asma'u (seema) sosai nakeji daku Allah yabar zumunci Amin*

Happy birthday Halimatus Sadiya Lawal Bala ('yan matan k'warni).😅
Allah yayiwa shekaru Albarka ya kuma qaro wasu masu cike da ni'imomi Amin. 👏🏻

*21*

Ranar da nadawo makaranta da dare mun fito daga masallaci sallar isha'i har mun kusa isa hostel sai natuna namanta da littafin addu'o,ina sai nace dasu Asiya su jirani nakoma na d'auko sabida ina son induba wani nafila dazanyi da dare, naje na d'auko zan dawo sai na hangi wata bishiyar mur datake nesa da masallacin tana haske sai na nufi nurin donmin naga mike haske haka koda na isa sai naga senior Shakira ce take ta wasu abu buwa kamar tsafi ina ganin haka sai nasoma addu'a inaja baya domin kada taganni amma na makaro don taganni, ta juyo idanunta kamar garwashin wuta ta nufoni ni kuma na kwasa da gudu ina karanta ayatul kursiyu afili.

Su Asiya suna hangoni ina gudu suma suka d'iba a sukwane.

Sai numfashi muke saukewa sanda muka isa cikin hostel, sunso nafad'a musu abinda yabani tsoro har nake gudu amma naqi fad'a sabida nayi tunanin duk wanda yarufawa wani asiri Allah zai rufa mishi amma agefe na qudurta zan mata wa'azi data bar tsafi domin shi hanyar zuwa wutan jahannama ne.

Ban dak ganinta ba ko awurin assembly sai dai kullum inaganinta cikin barcina tana bani tsoro dan komamin namun daji takeyi masu mugun ban tsoro, duk tadagulamin lissafi nakoma mara karsashi kuma naqi sanar da kowa labarin.
Chapter 10 · 0% Book details