← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 38

Sashe 30

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da fargaba ya had'a hannunsa da nata ya qamqe gam ta saki 'yar qara kad'an, duk da haka bai sake taba ya kuma matse yatsun nata sosai, "washh Allah!! ta furta da qarfi, sai lokacin ya saketa tare da zamewa ya kwanta rigingime kansa na kallon ceiling.

Asannu ta matsa ta kwantar da kanta bisa qirjinsa cike da sanyin murya tace "mi ke damunka? Daga kwancen ya kallota ya kai hannu bisa sumarta yana shafawa ahankali yana mai bata amsa "bana da kuzarin irinta ko wanni cikakken d'a namiji, bazan iya yin sunnar aure da keba ataqaice dai bana da kwazon da zan iya biya miki buqatarki.

Had'e rai tayi kamar bata san komi ba a kai tace "kasan hakan mi yasa kaqi sanar dani tun kafin muyi aure ko sai bayan aurenmu kasami laluran?

Tashi zaune yayi ya tallabo face d'inta da hannayenshi yace "ina gudun kiqi aure nane lokacin, gashi ni kuma ina tsananin sonki bazan iya barinki ba sannan tun da na soma mallakan hankalin kaina nafahimci ina da matsalar.

Shiru tayi tana kallomsa sai kuma sauke kanta qasa ta kuma cewa "amma mi yasa kaqi sanar dani sanda mukayi auren?

"Tsoron kada kice naci amarki ne ko ki tubure kiqi zama dani shiyasa nayita boye miki.
"uhmm to yanzu kana da yaqinin cewa bazan yima bore ba ne komi?

Shiru yayi zuciyarsa na kai komo, yakasa bata amsa.
Jan numfashi tayi tare da d'agowa ta kalleshi tace "to kuma miye na zuwa kana tona sirrinka wurin Hajja alhalin kasan ta soma tsufa ba komi ne yanzu zata iya dannewa ba, baka tunanin sanin matsalar zai iya jefata cikin damuwa?

"Wallahi tunanin haka sam baizomin ba beauty "uhmm to yayi amma miye nane man shawaran son rabuwa dani alhalin kasan bazaka iya ba?

Dafe kansa yayi cike da nadama domin yanzu yagama gano tsaf taji zancenshi da Hajja, wataqila shine yahaifar da fushin data keyi dashi.

"Ina sauraron ka mr Haydar, tace dashi cike da tsiwa.

Had'a hannayensa yayi wuri 1 yace "affuwan one's again haskena kuma sirrina, lallai nasan na kusa in tafka aikin dana sani sai Allah ya nufeni da rahama yadawo dani cikin natsuwata amma kisani billahil azim ko daidai da second 1 bantaba tunanin zan iya jure rashinki ba sannan abinda kikaji nasanar da Hajja na fad'ane kawai inji ra'ayinta akai sai gashi tayimin wankin babban bargo wanda dakyat nashawo kanta ta sauka kema ina qara neman affuwanki daki yi haquri ki yafemin duk abinda nayi miki wanda yajefaki kicin bacin rai.

Tura baki tayi tana d'an hararansa tace "ni komi ya wuce sai dai banson ka kuma fad'ama wani matsalarka irin haka donshi d'in sirrine.

"Tam bazan sakeba heart beat.

D'an murmusawa tayi tace "Ya Ali, ya amsa "na'am kayana, ta mintsili cinyarsa yasaki qara cikin wasa, ta gyara zama tace "ina son ka rubuta aranka cewa ni Rabi'atul Addawiyya zan rayu da kai acikin ko wani irin hali ka tsinci kanka har izuwa ranar maha'shar, zan zamo mai boye maka sirrinka har izuwa sanda lafiya zai wadaceka haka zan dage dayima ka addu'ar samun sauqi wurin mai duka sannan kasani koza mu dawwama ahaka ne ina tare da kai domin ban mance alkawarin damukayiwa juna ba a cikin garden, don haka kacire duk wani damuwa tare da wasi wasi kawai mucigaba da fadama Allah matsalarmu insha Allahu zaimana maganin komi kaji kayan Addawiyya, ta qara fadan haka tana kashe mishi 1 eye tare da sakin mishi wani murmushi mai kwantar da hankali.

Wani runguma ya kai mata, ya soma sunsuna ko ina na jikinta yana shafawa cike da nishad'i kuma da hanzari yake aika mata da saqon.

Gani zai jefata awani hali yasa tayi dibaran janyewa tana sauke mumfashi da sauri da sauri.
Kallonta yayi cike da tausayawa ya kuma yanjota jikinshi tana qoqarin kwacewa yace "a'a my angel kibari inbaki hot romances yarda zaki sami relief.

"Uhmm ya Ali tafi kayi wanka sai kazo inbaka labari mai dad'i "ya maqe kafad'a kamar wani yaro yace "a'a naqi wayon salon kafin indawo kinyi barci ko?
"Allah bazanyi ba, zan jiraka "ohk tam zomuje kitayani.

Idanu ta zaro tana girgiza kai, lakace mata hanci yayi tare da miqewa yana cewa "matsoraciya kawai, very soon zan soma yi miki wankan ai kuma tas zan wanke komi nawa da kyau nakuma zo na liliyeshi da mai.

Da sauri ta kauda kanta gefe cike dajin kunyar zancensa, yana dariya ya shige cikin bathroom zuciyar cike taf da qaunarta domin hakika tayi mishi bazata data yarda zata zauna da shi ahaka d'auke da lalura.

Kwanakin dasuka biyo baya zamane sukeyi mai cike da tsafta tare da tsantsar bawa junarsu kulawa wanda yake bawa mutanen dasuke tare dasu sha'awa ainun.

Bikin su Hameed da khairi yazo don gashi har nan da kwanaki biyu masu zuwa d'aurin aure, hidima yayi ma Addawiyya yawa sabida Aunty Hindu dazata shige gaba akan abin tana fama da laulayi mai wahala don haka sai itace ke gudanar da komi tare da taimakom Hajja domin Hajiya kareema Alh. Muktar yaqi sakar mata ragamar hidimar har kuwa da abinda yashafi 'yarta khairi yaqi aminta da lamarinta, tayi ta haukanta har tagaji.

Ita kam khairi ko a gyalenta indai tabata kayan gyara na Amare tana sha amma data kawo mata qorafin anyi kaza da kaza zata bar mata wurin sabida tasan tana tofawa to tsiya zata bita dashi.

Da yammacin alhamis suka gabatar da walima mai kyau da tsari.

Ranar gajiya mai suna ita kam Addawiyya tayi ta, don haka tana idar da sallar isha'i ta bingirea wurin ko wanka bata samu tayi ba. Koda su maryam sukazo tabasu gift d'in da khairi ta samu awurin qawayenta zata kaiwa momynta, sunyi2 ta tashi ta kasa saima layi take musu suna haka Haydar yashigo ya korasu suka fice cike dajin haushi, shi kuma ya ragemata kayan jikinta ya d'agata cak sai toilet.

Ita dai tajitane kawai cikin ruwa mai zafi sosai ta zabira tare da sakin qara.
Dariyan dataji yana mata ta fahinci wanka zai mata tako soma mishi shagwaba ita bataso yabarta zata iya da kanta, bai kula taba saida ya sulleta tsaf ya nad'ota kamar baby.
Koda yagama shiryata sai ya shiga nashi wankar kafim yafito tuni takuma lulawa duniyar barci. Rugumeta yayi yana cike da yabawa kwazonta ayayin aiwatar da hidimar bikin hae barci shima ya lula dashi.

Washe gari bayan sakkowa daga sallar juma'a aka d'aura auren khairi da angonta kabir sannan aka wuce aka d'auro na Hameed da Amaryanshi zuhuriyya wacce yabata sunar masoya wai riyya.

Taron biki yayi armashi sosai, qawayen Amarya khairi a part d'in Addawiyya suka tare, sai hidimarsu sukeyi cike dajin dad'i.

Da hayaniya yayiwa Addawiyya yawa sakamakon ciwon da kanta yake mata tun safe sai ta shige room d'in Haydar ta kwanta.

Kwanciyarta ke da wuya ta tsinkayi maganar babibullah yana cewa "sannu mai babban suna, ta amsa "yawwa uncle.
"Mai babban suna nacika miki alkawarinki na tambayo gimbiya zuhfa tace min ba sa hannunta cikin lamari, k'addarar daga Allah ne, zata dai tai maka da addu'a insha Allahu zai sami lafiya yazamo kamar ba'ayiba.

"Tam uncle Allah yasa hakan ya tabbata "Amin Amin.
"Bari nabarki ki huta amma kada kisake kiyi barci a irin wannan lokacin kinji? "Tam bazanyi ba, nagode da samuwarka arayuwa sosai, Allah yasaka maka da alkhairi "Amin.
Yana bacewa ta lumshe idanun face d'inta d'auke da murmushi ta furta "rayuwa kenan mai cike da qalubale, Allah kabamu ikon cinye wannan jarabawar.

***bayan kwana biyu duk 'yan biki sun watse sai gidan yakoma kamar da, tsit bakajin hayaniyar komi sai nasu hussain shima sai ranakun hutun qarshen mako.

Awani safiya Haydar tare da Addawiyya suke matsa jiki sanye suke cikin sport wear suna ta tsale kad'an kad'an a filin dake gefen garden, in tagaji ta duqa, ya miqar da ita su cigaba.

Da dai tagaji sosai sai ta kwanta tana maida numfashi ya iso ya d'ora kanshi bisa ruwan cikinta ya kai hannunsa bisa boobs d'inta yana cewa wai mi kike sha haka ne suke qara cika?
Ture hannunsa tayi cike danshagwaba ta amsa "ba kaine ka damesu da yamutsa ba, ai dole suyi ta kumburi kamar fanke.
'Yar dariya ya saki tare da matsasu da qarfi kuma alokaci d'aya yana mai mannawa cibiyarta kiss ya zarce zuwa samar qirjinta yana qoqarim d'aga mata riga xai tura kansa ciki tayi sauri tureshi tamiqe da gudu ya bita suka soma zagaye filin suna dariya.
Koda yayi nasaran kamata baiyi wata wata ba ya had'e bakinsu wuri 1 sai son kwacewa takeyi amma ta kasa, sai da yagaji don kansa sannan ya saketa tayi baya kamar zata fad'i yayi saurin tareta, idanunta lumshe ta motsa bakinta kad'an tace "Ya Ali yanzu in wani yashigo yaganmu haka mizamu ce?
Mai makon ya amsa mata sai kawai ya kuma had'e bakinsa da nata, ahaka yayi mata d'aukan jarirai ya nufi ciki da ita, ita kam sake maqalqaleshi tayi domin ji tayi kamar zai yar da ita.

Wano uban tsuka taja tare da furta "Wallahi nayi mugun tsanar ki Addawiyya kike koma wa oho.
"Eh dole kice kin tsani 'yar mutunci d'iyar mutanen arziki.
Cike da kad'uwa ta juyo tana kallo Hameed wanda yake tsaye abayanta tun sanda take leqen su Haydar kuma duk yaga abinda ya wakana.
"Mi yakawo wannan maganganun kuma my AH?
"Kinfi kowa sani sannan mi Addawiyya tayi miki da zafi da har kika tsaneta?
Banza tayi dashi zata raba ta wuce ya fisgota ya sakar mata mari yana huci yace "sai kin fad'amin maza nawa sukayi hawan daba akanki kafin in aureki?

Agigice taja baya tana mai jifarshi da wani mugun kallo, acikin ranta kam tsoro ne cike fal domin bata taba zaton wannan ranar zata risketa ba.
Chapter 30 · 0% Book details