Sashe 34
Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Miqewa tayi azabure tana waige2 can ta kumajin ance "mai babban suna nine ba Alee ba nayi miki muryanshi ne don kisan nima nayi kewarsa kuma natayaki jimamin rashinsa, kisani mai babban suna, rayuwa bata taba inganta sai taci karo da qalubale haka cikakken mumuni ne Allah yake jarabtarsa da k'addara domin ya gwada qarfin imaninsa don haka ki zamo cikin bayi nan nagari masu yawan godiya ga Allah in k'addara tazo musu.
Tana kuka ta amsa "tam uncle nagode, Allah saka da alkhairi da tunatarwa.
"Bakomi mai babban suna daga haka yabace ita kuma tamiqe ta fito zuwa kitchen inda ummie take had'a lunch.
Hakan yayi ummie dad'i sosai wanda takasa boyewa sai da ta furta "masha Allah autana tasoma dawowa cikin farin cikinta.
D'an murmushi tayi tare da cewa "uhmm ummiena kenan.
Ranar tayi hira sosai tare dasu kuma taci abinci kad'an, abinda yayi mugun faranta musu rai ainun.
Awani yammaci tana zaune a compound hannunta riqe da Alqur'ani tana bita, sam hankalinta yayi nisa cikin karatun datakeyi sabida yanzu shine aikinta kuma sosai take samun natsuwa da sanyi cikin zuciyarta duk intana karatun.
AL-QUR'ANIN KAREEM KENAN MAGANIN DUK KAN WANI CUTA.
Allah ta dawwamar damu cikin bitarshi Amin.
Kamar daga sama ta tsinkayi muryan su hassan suna kira sunarta "aunty Adda tare da rungumeta suna kyalkyala dariyar murnan ganinta.
Cike da murnan ganinsu itama ta rungumesu tare da cewa "ku dawa kuka zo?
Atare suka amsa mata da "mu da yaya Hameed da kuma ummul bait, yace ma wurinki yakawo miki ita kyauta, mamanta tana ta kuka sanda muka barota Hajja nata bata haquri.
Cikin bargaba ta dubi parking lot ta hangoshi jingine jikin motarshi sabe da ummul bait.
Sai taga yakoma mata Haydar sak, hatta kallon dayake mata hak irin ta haydar.
Rintse eyes d'inta tayi ta sake bud'ewa sai taga ya koma mata biyu gashi sabe da ummul ga kuma Haydar tsaye gefensa yana yi mata murmushi da qarfi ta miqe tana furta "ya salam!!.
"Mai babban suna zuciyarki ce take hasko miki photon Alee amma shi tuni yadad'e da koma ga mahaliccinmu don haka ki cire tunanin zai kuma dawo. Muryan uncle kenan yake tunatar da ita.
Jiki a sanyaye ta koma ta zauna tare da rungume su hussain hawaye yana bin fuskanta.
*mrs j moon*
[2/2, 9:49 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*
NA
SAFIYYA.
*Assalamu Alaikum fans ina mai jinjina muku abisa comments d'inku daya riske ni ta ko ina agame da rasuwar Alee, hakan ya dad'a tabbatarmin dacewa kuna tare dani sau da qafa, to ina godiya sosai. Sannan ina son kusani ita rayuwa ko ya take tana tafiyane cike da qalubale haka duk abinda kakeso to tabbas wata rana sai yayima nisa ko kai kayi masa nisa. K'addara ita sikeli ce ta ma'aunin mizanin imanin mummunan bayi, don haka rashin Alee shine k'addarar Addawiyya. Aqarshe ina mai bawa fans wad'an da suka taya Addawiyya kukan rashin Haydar dama wad'an sukayi juriya basu zubda jurwayeba da duk kanin masoya labarin hak'uri, kuma wannan shafin na sadaukar muku dashi kyauta kuyi yarda kukaso da shi bamai hanaku domin nakune*💃 😅 LOVE YOU ALWAYS FANS❤😍😘
*46*
Hucin saukan numfashinsa taji daf da ita yasa ta waiga da sauri.
Subbahallahi!! Ta fad'i cikin ranta, sai kuma tayi sauri miqewa tsaye tana jifarshi da wani kallo wanda yarasa gano ma'anarshi.
Ahankali yace "wannan kukan baya da amfani agareshi illah azaba da yake qaramishi don haka nasan kin sani wata qila mugunta ce yasa kikeyin hawayen don yayi ta qonashi.
Afusace ta wulla mishi harara tana mai point d'insa tace "Hameed ya isheka tijaran da kazo yimin har cikin gidanmu kuma kasani kada kaga wai uwa 1 uba 1 kuke da ya Alee kayi tunanin kafini sonsa tare da jin zafin rashinsa, to wallahi ko kwatan2 abinda nakeji game dashi kai bakaji sabida haka kada kasake cemin inayi masa mugunta ehe, ta qarasa cike da tsiwa ga kuma kwalla yataru cikin idanunta sai qoqarin maidasu takeyi don bata son su zubo.
Shiru yayi yana binta da kallo fuskasa cike da murmushi.
Ganin ya maidata sauna sai tamiqa hannu ta fizgo ummul wacce take ta sharan barcinta bisa kafad'arsa, tayi gaba sai kuma ta juyo fuska a had'e tace "nagode sosai da kyauta amma kasani bana son yawar bibiya inkana son ganin 'yata sai kanasar dani in ina da lokaci domin bazan lamunta ka riqa zuwamin baqatatan ba, dafatan kajini da kyau?
Shafa kwantarcen sajensa yayi cike da mishad'i sannan ya amsa "naji hajiya Rabi'atul Addawiyya matan malam badamasi.
'Dan sakin fuska tayi batare da ta kuma magana ba tawuce ciki su hassan suka rufa mata baya.
Yajima duqe a wurin yana sake sake zuwa can ya miqe ya isa wurin motarsa ya bud'e boot ya d'auko akwati biyu d'aya babba sosai d'aya kuma d'an madai daici, yayiwa falon tsinke.
Ummie ya tarad zaune tana bitan wani littafin addu'o,i.
Har gabanta ya isa ya zauna sannan ya gaisheta, ta amsa cike da fara'a tare da tambayarsu mutanen gidan ya amsa "suna lafiyalau.
Kallonsa ummie ta kuma yi tace "Hameed haka akeyi ka d'auki mutum sukutum kayi kyauta da shi? Baka tunanin ita uwar yarinya wani hali zata fad'a saka makon rashin gudar jininta kusa da ita?
Sauke kansa qasa yayi kuma cike da ladabi ya amsa "babu komi ummie, ai ni da Addawiyya duk 'ya'yan kune kuma nasan zuhuriyya bazata taba bijirewa umurnina ba haka babu halin dazata fad'a don bata tare da ummul hasalima anrage mata d'awainiya ne sabida yanzu haka batajin dad'i bata iya hidimar ummul sam, nike mata dukkan wani abun da yashafi raino, ga aikina ga hidimarta sai kawai nayanke shawaran bari na cika alkawarin dana d'auka kawai.
"Tam yayi Allah yatayata riqo ya kuma raya ummul cikin ni'imar Allah.
"Amin, ya amsa.
Hira sosai suka sha da ummie, inda ta tashi da kanta ta kawo mishi kayan motsa baki, yanaci suna hira har lokacin sallar magrib tayi.
Ummie tamiqe ta shige room d'inta dake qasa don ta gabatar da sallah.
Yana ganin haka ya haye upstair da sauri.
Koda ya hau sai yatsaya yana nazarin wani room zai shiga, qasa qasa yake jiyo dariya sai ya doshi d'akin kai tsaye, tabawa yayi yajita bud'e don haka sai ya saka kansa kawai batare da neman iziniba.
Su hassan yagani zaune tsaliyar bed d'inta duk sunyi caka caka da chocolates tare da biscuits suna ta aikin sha, sunsa ummul a tsakiyarsu in sun bare nasu sai su bare mata su miqa mata ta amshe.
Ingina da qofar yayi yanata aikin kallonsu cike da jin dad'i, kuma cikinsu bawanda yalura da zuwarshi.
Motsin fitowarta daga toilet yasa ya zubawa qofar bathroom d'in idanu.
Fitowa tayi d'aure da guntun towel wanda iyakarshi cinyoyinta ya rufe.
Ba tare data lura da shi ba, ta isa gaban mirror tasoma shafa mai, ta matso lotion zata shafa a qirjinta ta tsinkayi maganarsa inda yace "kai kai!!! Jira infita tukunna basai kin nunamin kayan ruwan naki ba.
Zabura tayi wanda kad'an yarage towel d'in bai sunbule qasa ba, sabida sosai ta firgita dajin muryanshi don batayi zaton da mutum ba.
Kallonsa tayi kamar zatayi kuka tace "kasan Allah in har nacre bamyafe makaba sai Allah yafitarmin da hakkina da ka d'auka ta hanyar tsoratani.
Kashe mata ido 1 yayi tare da matsowa inda take tayi sauri d'aga mishi hannu tana mai cewa "kul ka taka shari'a kuma kaficemin a room tun ban saukema kwadon rashin matunci ba.
Matsowa ya kuma yi a fusace ya kama dantsen hannunta ya matse da qarfi tako kwalla qara don azaba yasa qafarsa ya take mata yatsu tare da murzawa ta rintse idanunta cike dajin azaba ta dubeshi tace "sakeni Hameed banson irin wannan bad'alar.
Mai makon ya saketa sai kawai ya kai bakinsa daf da kunninta yana mai cewa "kinsan Allah in har kikace tsiwa zaki tsiromin dashi to ni kuma zan soma baki wuya kala kala don haka sai ki kiyaye kinsanni bana d'aukan wargi musanman kan mace, macenma kwaila irinki, yafad'a hakan tare dabin jikinta da kallo.
Da qarfi ta fizge daga riqon da yayi mata, tayi saurin janyo hijab d'inta ta saka ta nuna mishi hanyar qofa tana mai bashi umurni "malam kaficemin a d'aki nace, bana da lokacinka.
Wani damqan ya kawo mata tayi sauri fad'awa cikin su hussain tana ihu, aikam yaran da tun dazu suke kallonsu suka saka mata dariya hassan yace "laaa yaya Hameed yafi qarfin Aunty Adda, hussain ya amshe da "eh, Allah yafita, bakagani ba har yakusa sata kuka, sai suka kuma kwashewa da dariya har da Hameed d'in.
Wani uban tsawa ta daka musu take sukayi shiru suna mazurai, yayin da baby ummul ta fashe da kuka don taji tsoro.
Hameed wanda yake ta kyal kyala dariyan zancen su hussain yayi hanzarin kai hannu zai d'auketa, tako buge mishi hannu tare da cewa "dalla malam kar ka tabamin 'ya, baya yaja yana dariya qasa qasa ta kuma bata rai tace "wai ka soma mensuration ne halan da kanajin time din prayer zai wuce amma katsaya d'aukan magana kamar nid'in ba auntynka bace?
Kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma ya miqawa su hassan hannu suka kama ya d'agasu suka fice batare da yakuma kallon inda take ba.
Tsaki taja mai sauti tare da cewa "iskancin banza da wofi kawai, yawani zo duk ya dagulamin lissafi har yana wani cemin kwaila a'a kwanso ce ba kwaila ba.
Tare dashi da Abbie sukaci dinner, su kuma su hussai sukaci tare da ummie ita kuwa Addawiyya ta qule cikin d'aki da 'yarta tana aikin bata priso.
Tana cikin gyarawa ummul kwanciya ya kuma shigowa ta d'ago tare da cilla mishi harara bai kulata ba illa iyaka yamatsa kusa da 'yarshi ya manna mata kiss daga haka ya fice tabi bayanshi da harara kamar kwayar idonta zai fad'o.
Ummie ce ta shigo da kanta ta tasata a gaba duka sakko don tayi sallama da Hameed.
Baki ature ta isa wurin ta miqawa su hussain ledar chocolates tace dasu "kugaidamin da momynku, dadynku, hajiyarku tare da tsohuwar kirki Hajjanmu, atare suka amsa da "to aunty adda.
Juyawa tayi tabar wurin batare da ta dubi inda Hameed yakeba.