← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 38

Sashe 5

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa wasa Addawiyya takai kwanaki goma da bace kuma har yanzu ana zuwa nemanta cikin dajin amma ba'ayi sa'ar ganintaba.
Salma kuwa ta rame sosai, ta maida bakin itaciyar tumfafiyan nan inda Addawiyya take yawan zuwa wurin zamanta, intaje ta had'akai da guiwa tayi ta kuka tun Ummi nayi mata fad'a har ta zuba mata idanu. Abbi kam baima iya ce mata komi sabida duk in yaganta awurin Addawiyya ce ta fad'o mishi arai.

Adda'a kam tanasha na Allah yabayyanata intana raye in kuma ta rasune Allah yaji qanta da rahama.

**** zaune take gefen gadon dayazama nata ayanxu.

Inuwar Mutane take gani suna ta gilmawa ta gabanta kamar kullum, ta runtse idanunta ta bud'e sai kawai taga wata qatuqar mage kwance ta turo k'afafunta gaba ta zuba mata idanu, itama idanum ta zuba mata tana qare mata kallo,, tabbas itace take yawan gani duk inta kwanta barci tunsanda tasamu kanta awannan d'akin.
Yauma magen rik'id'a tasoma yi mata kamar yarda take gani amufarkinta ta koma mata bak'a, kore, yelo, ja sai kuma ta dawo golden zuwa can ta dawo faranta yarda take, ita dai Addawiyya quri tayi tana kallon ikon Allah sabida yanzu tabarjin tsoron duk abinda zata gani a d'akin.
Koda ta kuma kallon inda magen take sai tanemeta tarasa, ta miqe cike da sanyin jiki ta shige bayi tayo arollah tayi sallar la'asar sabida taji anata kir

Awani charming garden take ta shawaginta cike da nushad'i can nesa ta hango shi yana zaune bisa buzu yana jan tasbaha kansa sunkuye.
ahankali ta qarasa wurin ta zauna gefenshi tace "Abbi d'agowa yayi taja baya bakinta bud'e yasakar mata murmushi yace "ni uncle ne ba Abbi ba, Abbinki gashi can cikin kasuwa yana saida dabbobinshi zaiyi hijira da mahaifarshi zuwa nesa da it.
Sai ta qurshe tana wani irin kuka mai taba zuciya, ya kai hannunshi ya dafa mata kai yana girgizawa alamar rarrashi, sai kuma yakamo hannunta atake wani sanyi ya jiyarci jijiyoyin jikinta tare da bargon ta, tayi wani irun zabura ta farka sai ganinta tayi agadon umminta kuma cikin bukkan ummin.
K'ara ta saki mai k'arfi tana fad'in ummi!!!!!!!.

Salma wacce take waje tana share tsakar gida ta saki tsintsiyar ta nufi d'akin da gudu sakamakon jin muryan 'yar uwarta da tayi,, tanaganin Addawiyya zaune, ta kuma yo waje da gudu tana fad'in "tadawo wallahi, ummi,, Abbi gata can a samar gadon ummi. Atare su ka tambayeta "wa? "Addawiy ta amsa musu tare da jan hannayenzu zuwa cikin bukkan.

*mrs j moon*
[12/29/2017, 3:00 PM] Asma'u Seema1: [11:36AM, 12/7/2017] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA

*Shafin nakune my aunties Aunty Maijidda musa tare da aunty jamila gombe, sosai nake godia da karamcinku gareni Allah yabar k'auna Amin.lallai kusani Inaji daku ainun acikin ruhina*❤😘

*11~12*

Suna shiga Addawiyya tana sakkow abisa gadon. atare suka rungumeta suna ta jera kalaman godiya ga Allah mad'aukakin sarki daga dawo musu da gudan jininsu zuwa garesu batare da zato ka tsammani ba.

Ita kam Addwaiyya sai kuka takeyi tana qara k'amk'ame su ummi zuwacan ta dawo ta rungume Salma, cikin fizgan magana irin namai kuka tace "Adda nayi kewarki sosai wallahi, inna tuna daku nayita kuka bamai rarrashina.

Itama Salma kuka takeyi har da sheshsheka ta amsa "nima nayi kewarki sweet Addawiy, har suma nayi tayi danaji kin bace, ashe zakidawo gare, kai wallahi Allah shine abin godiya, Allah mun gode maka, Allah kak'ara tsare dukkan musulmi da afkawa irin wannan yanayi.
"Amin, su Abb suka amsa atare.

Cikin k'ank'anin lokaci yankin k'auyen labari ya bazu na anga Addawiyya, ta dawo gida batare da ko rauni ba. Kafin kace me gidansu Addawiyya yacika taf da al'umma masu zuwa tayasu murna tare da ganin ya Addawiyya tadawo.

Hatta ard'o dakanshi ya tako yazo ganinta.
Atsakiya suka sakata suna tayi mata tambayo na ya'akayi ta bace kuma aina tasami mafaka ta boye akayi ta xuwa nemanta batare da anganta ba?

Cikin sanyi tace dasu "sanda su hisqilu suka kamani nasamu na kufce sai nayi ta gudu har nafad'a inda mucijiya take kwana, tako biyomu tarw dasu, nasamu na tsira ahaka nayi ta rayuwa cikin daji innaji yunwa sai na ci a kayan itatuwan dajin haka innaji k'ishi sai inqarasa awata rafi nasha ruwanta sannan nayi arollah in sallah inna fahimci lokaci yayi,, nakan bata lokaci ina addu'ar Allah yakawomin mafita, to ahaka dai harna kwashe wasu kwani ina rayuwa ni d'aya batare da wani abin citarqa yasameni ba.
Nasoma bin hanya domin indawo cikin mahaifana to cikin ikon Allah sai gashi d'azun da sanyin safia na iso gida.

Cike da al'ajabi mutanen wurin sukayita hamdalah suna kumayi mata sannu, ita dai sai murmushi takeyi tana kallon gefen damarta wanda tun sanda tasoma basu labarin take kallon wurin bako k'iftawa.

Bayan kwana biyu.
Addawiyya ce tare da Salma suke hiransu cikin nishad'i zuwa can Addawiyya ta dubi salma tace "Adda ashe jikin micijai sanyi yake dashi kamar k'anqara? Idanu waje Salma take dubanta takasa tankawa, ita kam tacigaba dacewa "uhmm ai wallahi har yanzu inajin sanyin jikinta a fatata kuma hasken dake idanunta yakasa bacemin afuska, kai Allah yayi halitta awurin kam, Adda bakiganta ba wata qatuwa gaske kamar tayan babban mota kalanta fara tare da rod'i rid'in golden,, wallahi bantaba ganin micijiya mai kalantaba sai a mufarkina naran nan sai kuma lokacin dana nemi wurin tsira daga sharrin su hisk'ulu.

Jadabaya Salma tasomayi har tamatsa sosai sannan tamiqe ta kwasa da gudu tashige bukkan Abbi, tabe baki Addawiyya tayi tana mai furta "matsoraciyar banza kawai.

"Abbi wallahi Addawiy tana tare da matsala domin taboye muku gaskiyan abinda yafaru da ita.
"Kamar nami ba? Cewar ummi.
"Allah ummi yanzu take bani labarin wai jikin micizai yana da sanyi kamar k'anqara.

Azabure ummi ta jababaya tana kallon Salma tace "banson sharrinki fa yarinyar malam.
"Wallahi Allah ummi kuje ku tambayeta kuji.
"Tam munji kiramana ita, Abbi ya umurceta, wanda shima yasoma tsorata dajin labarin, dama can shi bai gamsu da yarda tayi musuba bayanin bacewan nataba yadai kyaletane kawai.

Daga nesa da ita Salma ta tsaya tace "Addawiy kizo inji Abba, harara ta wullamata sannan ta miqe tace da k'arfi "ga miciji nan ya nad'e miki k'afafu. Aiko wani tsale Salma ta daka ta fad'a bukkan Abbi da uban gudu tana ihu.
Me Addawiyya zatayi inba dariyaba, hartana kwanciya aqasa ta dafe cikinta hawaye da majinu suna ta zirara don tsaban dariyan mugunta.

Cirko2 su ummi sukayi suna kallonta tana d'agowa ta dubi Abbi tace "laaa! Gashinan ajikin Abbi zai shige mishi aljihu.
Wayyo zo kuga wani wuntsilawa da tsohon yayi ya fad'i ya k'asa ya miqe arud'e yayi hanyar waje da gudu. Ummi kam ai tuni takai cikin bukkanta ta kulle qofa dama ita kam Salma bata fitoba tunsanda tashige bukkan da gudu.

Addawiyya kam don tsaban dariya saida tasaki fitsari awando, haka yake gudu ajikinta ya wanke mata qafafu.

Abbi ne yadawo yana mazurai Addawiyya ta dubeshi ta kuma kyalkyalewa da dariya tace "Abbi wallahi duk kanku nafiku jarumta nida naga micijiyan da idanuna har natabata banyi irin wannan rud'ewanba amma ku daga ina muku wasa shine duk kuka zure haka? gama Adda Salma can cikinta yana murd'awa tana son kaiwa ma'aikatan sarrafa kashi (msk) ziyara.

"Rabi'a kinci gidanku nace, wato kinmaidamu kakan ninki ko? Girgiza kanta tayi tare da barin dariyan ta tsunu kamar ba itace ke kyakyacewa ba. Jan hannunta Abbi yayi zuwa cikin bukkanshi.

Salma naganinta ta miqe ta fice hannunta dafe da cikin, a makewayi tayada zanzo ji kake fatsatsatsa!!! Burrrr!! Burr!! Burrrriririii!!.

Tana share zufa ta shigo bukkan, Addawiy ta dubeta ka kama bakinta tana qunshe dariya.

timmm!! Salma ta timawa Addawiyya duka a baya zata qara mata wani ummi ta riqe hannunta tana hararanta, cike dajin haushi ta zauna gefen Abbi tana wullawa Addawiyya harara, ita kam sai murmushi take dokawa tare da kanne mata ido 1.

Gyara murya Abbi yayi ya sauke dubanshi kan Addawiyya yace "Rabi'a muna saurarenki da kifad'amana gaskiyan abinda yafaru dake sanda kika bace.

Zama Addawiyya tagyara ta jingina jikin ummi tasoma basu labarin da ta sanu har zuwa falkawan datayi ta ganta agadon umminta.

Baqaramin al'ajabi suka fad'aba sanda sukaji wannan sirad'i da tsallake musanman na wurin rijiyan kugu.

Salma ta matso ta kama hannunta tace "amma Addawiy taya kika tsara labarin nan sanda su ard'o suka tambayeki kuma miyasa kika boye musu gaskiyan lamarin?

Shiru tayi taqi cewa komi.
Ummi ta dafa kanta tace "autana abin alfaharina kuma haskena yi magana mana.
Quri tayi tana kallon rifin tsoron d'akin zuwacan ta gyad'a kai tana mai amsawa da "tam.

"Alokacin fa wannan mutumin ne daya tai makeni yazo ya bud'emin tafin hannunshi ina karanta dukkan bayanin danayi sabida yacemin bakowane zai yarda da abinda zan fad'aba kuma wasu zasu iya mai dani 'yar mai ganye sunazuwa suna cewa inbasu magani alhalin bansan komi akan cutarsu ba.

Jinjina kai sukayi dukkansu cike da gamsuwa da bayaninta.

Abbi ya numfasa yace "hakikanin gaskiya Rabi'a kinga abubuwan al'ajabi kuma tabbas kin had'u da aljannun musuncine, lallai nagode musu da Allah yabasu ikon taimakonki, Allah yasaka musu da Alkhairi. Suka amsa "Amin.
"Abbi dama a aljannu akwai masu kirki haka? "Sosaimakuwa Salma, dasu kuma wasun suma sun mafimu tsoron Allah sabida su d'in suna ganin mala'ikun Allah kuma suna jure bautan Allah mad'aukakin sarki fiye damu bil'adam illadai Allah mad'aukakin sarki ya tabbatar da munfisu matsayi da d'aukaka ta ko ina sabida masoyinsa habibinsa d'angatansa ma'aiki SAW ajinsinmu yafito.

"Allahu Akbar!! Suka fad'a atare.

Addawiyya tace "to Abbi miyasa ake samun azzalumai macuta cikinsu alhalin sunfimu ganin ilmomin Allah SWA quru k'uru?

"Haka Allah yake wanzar da k'udinsa da iradanshi kuma asanda yaso, kisani yarda mukammu bi'adama cikinmu akwai azzalumai marasa imani koda kuwa suna musulmai to suma haka yake a cikin jinsinsu.

"Aikam indai hakane to micijiyan nan data biyomu itadin azzalumace kuma tana daga jinsun junnu domin daganinta ba normal micijiyabace kuma hakik'a itace tayi azajalin su ilya sabida inajiyo kurukuwansu sanda ta kamasu.

"Biri yayi kama da mutum kam don koni nayi zargin ba micijiyan kyau bace

Allah bata kyau bace Abbi, bakaga idanunta ba zar haske kamar fitila kuma wallahi haskensu sunqi bacemin a cikin idanuna.
Chapter 5 · 0% Book details