← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 38

Sashe 38

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Ya kukayi dashi? Maryam ta tambayeta, "uhmm tatsuniyar gizo ai bata wuce ta qoqi kalmar so dai ya jaddamin ni kuma nace a'a.

Dariya khairi tasa sosai zatayi magana maryam rayi hanzarin rufe mata baki,Addawiyya ta dubesu ta tabe baki ta kwanta tana cewa maryam "don Allah besty yi driving dinmu mu sauke wannan 'yar neman fitinar a gidanta ko nasamu kaina yabarmin ciwo, wanda neman maganarta ya haddasamin.

"Eh, na daiji kuma dole ya Hameed yayi winning ehe.

Banza tayi da ita, tako kwashe da dariya, girgiza kai maryam tayi tare da yiwa motar key suka fice daga cikin skul d'in.

Abin kamar had'in baki tana shan kwanar shiga layinsu bayan maryam ta sauka agidansu sai tacikaro da ubaiyu tsaye a get din wani gida ko kallonsa batayi ba ta wuceshi da gudu, tana mai dad'ajin haushi.

Ita kad'ai take cewa "ni haja ce halan da kowa zai soma son samuna? abinda ban fuskanta a zamanin 'yan matancina ba shine yanzu zai zamemin qalubale?

Amsar da take buqatan sani kenan amma ta kasa samowa.

A tsiyace tayi parking ta fito afusace ta tasarma ciki.

Tana shiga parlor tayi turus kanta yakuma sarawa kamar zai tsage biyu, hannu tasa ta dafe goshinta tare da zubawa Hameed idanu wanda yake zaune a gaban ummie da ala magana mai mahinmanci sukeyi dubi da yarda ya sunyar da kanshi kamar mai d'aukan ilimin addini ga malaminsa.

Quri yayi mata shima yana kallonta tare da nazarto tarin damuwa a face d'inta.

Sallamar Ubaiyu shi yasa tayi saurin isa wurin ummie ta kwanto da kanta a bayanta tana cewa "ummie yimin addu'a kaina ciwo kamar zai rabe biyu.

Sai da suka gama gaisawa da ubaiyu sannan tayi mata addu'ar, ta miqe ta nufi upstairs, ummie tace da ita "auta bakiga Hameed da Ubaiyu bane halan dabaki gaishe dasu ba?

Dawowa tayi cikin rangaji mai nuni da alamun gajiya atattare da ita tace "sannunku ya aiki da iyalanku?

Bata tsayajin amsarsu ba ta haye sama da d'an gudunta, tana shiga room d'inta ta kife ruf da ciki samar bed ta lumshe idanunta tana jin wani mai dad'i yana kad'a mata suma kuma tana jin shigarsa cikin jikinta abinda ya haifar mata dajin kasala, tayi lamo, acan qasan zuciyanta kuwa tunani ne fal har ta rasa wanne zata kama sai kawai tasoma istiggafari, bata jimaba tanayi barci yazo yayi awon gaba da ita.

*mrs j moon*
[2/7, 10:22 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*50*

Barci ne tayishi mai mugun dad'i wanda ya d'auketa lokaci mai tsawo don sai bayan magrib ta farka, miqa tayi tare da salati sai kuma tayi jim tana tunanin wannan wani irin barci ne tayi shi haka gashi har duhun dare ya shigo, d'an tsaki taja tana mai furta "ummie bata son inayin irin wannan barci amma yariga da ya zamemin jiki.
Hannayenta ta d'aga sama tace "Allah kayaye min shi cikin amincinka, ta amsa ma kanta da "Amin.

Wanka tashiga tabata lokaci sosai cikin bathroom sannan ta fito, shiryawa tayi tsaf sai qamshi take ta zubawa, asannu ta taka ta isa wurin d'an qaramin freeze d'in dake d'akinta ta bud'e ta d'auko babban kwalin hollandia drink ta zauna gefen bed ta bud'e kwalin ta zuba a wani glass cup mai d'an girma tasoma sha tana lumshe idanu, sosai take son duk abinda ya dangainci milk.

Wasa2 sai da ta kusa shen kwalin drink d'in dika sannan ta tsagaita ta d'aga kwalin ta girgiza sai kawai tasoma dariya ita d'aya tare da kai hannu tana shafa cikinta tafurta "waya gayamin barno gabar take, ai dole 'yan hanji sunemi abincinsu, tun safe kwankwani maltina kad'ai yake cikina fa, uhmm wallahi yunwa bata da kyau, Allah ubangiji kanesan tamu da ita alfarman Annabin Rahama, Amin.

Falon qasa ta sauko direct dinning area ta nufa, ta soma bud'e kulolin dake wurin, tuwon shinkafa ne da miyar agushi taji namar saniya sai qamshi yake tashi, sai soyayyen naman jabbi sunji kayan qamshi da kunun aya mai sanyi.

Bata rai tayi domin ita kam ta tsani tuwo arayuwarta gashi kuma tanajin k'yuyar shiga kitchen, da ta dafa ko noodle ne.

Hakanan ta d'iba tuwon kad'an ta saka cinyar naman jabbo 1 ta d'auko ruwan roba ta dawo cikin parlorn ta zauna, sosai taji dad'in food d'in domin sai da ta cinye shi duka ta kora da ruwa, ta d'au kayan ta shiga kitchen ta wanke ta kife sannan ta dawo falon ta kwanta samar doguwar kujera, tunani ne yake son zuwa mata arai amma taqi barinsa yayi galabar zuwa.

Tananan kwance ummie tafito d'auke da baby ummul sai kuka take ta tsalawa, da sauri ta tashi zaune ta miqawa ummie hannu tana cewa "ayya my sweetheart kinyi kewata ko? to zuwa muji d'imin juna.

Tanako amsarta yarinya tayi tsit ta kwanta lamo a jikinta.

Dariya Addawiyya ta saki tana kallon ummie tace "aha yarinya taji d'umin momma nta tayi tsit, anyama kuwa ummie ba mintsilinta kikayi ba? Ta qarasa maganar cike da zolaya.

Cikin hararanta ummie ta amsa "Eh, mintsilinta nayi, 'yar nema kawai, kuma kisani daga yau duk inda zaki da 'yarki zaki tafi don bazan iya da rigimarta ba.

Cikin marai raita tace "Ayi haka kuwa ummie? "Sosai ma kuwa, yi yazama dole ai "uhmm muna neman affuwan ummienmu baza muqara yi miki kukan banza kinji?
Qin kulasu tayi ummien.

Ganin haka sai ta kuma rungume ummul sosai tana sunsuna wuyarta tace "yarinya 'yar gatan ummie sai qamshi takeyi kamar fure, kyal kya lewa da dariya tayi ummul kamar taji mi akace.

Tsillata sama tayi cike da jin dad'i tace "kai inajin sonki 'yata har cikin tsokar zuciyata, Allah yasa ina da rabon ganin aurenki dai.

"Amin, ummie ta amsa tare da cewa "zauna ina son muyi maga dake, "tam ta amsa tare da zaunawa a gaban ummien ta zuba mata idanu yayin da ummul tuni ta sauka tasoma wasanta dama kukan rigimar son ganin addawiyya takeyi.

"Auta shin abinda kikayi d'azun kin kyauta kenan?
"Minayi kuma ummie? "Au kin manta irin gaisuwar asharuwan tsintsayen da kikayiwa Hameed da Ubaiyu d'azun?
Sunkuyar da kanta tayi qasa tana sosa tsinin hancinta, taqi cewa komi.
Kallonta ummie tayi sosai tana son gano damuwarta amma bata gano komi ba sai kawai ta cigaba da cewa "lallai hakika d'azun raina ya baci kuma naji kunyarsu sosai sabida ina ganin qimarsu fiye da tunaninki don haka banason sake ganin kin maimaita hakan koda abayar idanuna ne.
Ahankali ta amsa "tam ummie bazan sakeba ayi min affuwa, nadawo ne da matsanancin ciwon kai shi yasa.
"Allah ya sauwaqa to "Amin.

Miqewa tayi sabe da ummul wacce tasoma gyangyad'i.

"Koma ki zauna bangama maganar ba ai.
Kallon ummien tayi taga babu wasa sam atare da ita sai ta koma ta zauna gabanta yana fad'uwa.

*Ayi haquri da wannan don Allah*

*mrs j moon*
Chapter 38 · 0% Book details