← Book details Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 38

Sashe 31

Rabiatul Addawiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaki amsamin ko sai na karya miki wuya kin mace na huta daganin ragowar wasu? Banza kawai karya mai fuska biyu, wato kinsan baki da gaskiya shiyasa kikayitamin zille2 ko? To wallahi kisani bazan zauna da keba harbsai natabbatar da ingancin lafiyarki sabida haka wuce kishirya inje abinkikamin ke ciki da bai don bazanyi da kaina ba.
Zuhuriyya kuka ta fashe dashi mai cin rai, ko kallo bata isheshi yasakai yashige room d'insa yana maijin tsanar kanshi da kanshi duk da bai bi kyalkyala banza ba da haka bai sameshi ba, yanace shi sai mai nonuwa da duwawu to ga irinta nan ya kwasowa kanshi ta kaici, shiba mazinaci ba amma gashi ya auro mazinaciya.

*Hattara dai 'yan mata budurcinki 'yancinki ako ina*

This page is for you Aisha manumfashi, inajin dad'in soyayyarki ga Addawiyya sosai Allah yabar zumunci 👏🏻😘 sannan tace inbakibar ce mata dangin aljanu ba sai ta kai samar dutsen rafin cigogo kinkwana acan 😅 lol

*mrs j moon.*
[1/30, 9:18 PM] Mrs J Moon😊: *RABI'ATUL ADDAWIYYA*

NA
SAFIYYA.

*43*

Koda ya fito a inda yabarta tana risgan kuka nan ya sameta, shiru yayi yana kallomta ransa abace, doguwar tsaki ya ja tare da daka mata tsawa ta miqe bashiri ya nuna mata hanyar room d'inta yana mai bata umurni "dalla wuce kishirya tun ban sauke hushina akanki ba, cikin rawar jiki ta wuce tana mamakin bala'i irin na Hameed, ashe dai haka yake da tijara? Tambayar da tayiwa kanta kenan cikin ranta.

Ahanyarsu ta zuwa hospital kowa yayi shiru, sai saqe saqe sukeyi cikin zuciyoyinsu, ya d'an juyo ya kalleta har yanzu bata bar zubar hawaye ba ga kumatun ta nan inda ya mareta har ya tasa kauda kansa yayi yana mai jin tausayinta cikin ransa sabida sosai yake sonta da gaskiya.

Anyi binke iya bincike kuma antabbatar da lafiyarta lau haka shima sumul yake, koda suka dawo gida baibi ta kanta ba room d'insa ya shige ya kwanta yana ta tunanin wannan lamari abinda sam baiyi zatoba sabida dubi da irin tarbiyyan gidan data fito ashe duk ta bogine, uhmm lallai shi natsuwa ba'a fuska takeba dace ne kawai abin.

Sosai lamarin da ya risketa yabashi mamaki in bai mantaba yataba riqe mata hannu tayi ta mishi masifa wai ita ba 'yar iska bace waye2 amma ji yarda yasameta kamar qofar gari, dafe kansa yayi zuviyarsa tayi masa nauyi atake yasoma kiran sunar Allah cikin lokaci qanqani yaji sanyi yana ratsa mishi zuciya.

"Abdul hameed don soyayyarka da ma'aiki SAW kayimin affuwa, maganarta ya doki cikinn ears dinshi.

Kallonta yayi sai daga kwancen sai tausayinta yanemi karya mishi zuciya.

Janyota yayi jikinsa yace "fad'amin gaskiya miyasa kikayi yawon ta zubar?
Lafewa tayi jikinsa cikin muryan kuka tasoma magana "ba'ason raina na aikata ba, sharrin qawayene wata rana a skul qawarmu tayi birthday shine muka had'a party domin tayata murna to anan suka samin abin maye ya bugar dani mazan wurin sukayi watandensu dani, lokacin dana fahimci haka nayi kuka mara adadi sannan naja musu Allah ya isa yafi cikin Duran, baya kwana biyu sai na fad'a halin son kasancewa da d'a namiji abinda ya kaini da nemansu da kaina to tundaga nan na sami abinyi lokaci zuwa lokaci nake aikatawa, kuma agida bawanda yasani domin Abu yana da tsanani kuma yayarda dani ainun shi yasa na boye musu halin dana ke ciki tun farko don gudun jefasu cikin tashin hankali.

Ranar wata littini da bazan manta da shiba arayuwata, na sawo kai kenan cikin hostel sai naji qawayena suna gulmar wai zubamin magani mai tada dire sukeyi shi yasa nakejin son kasancewa da d'a namiji, jin hakan hankalina yayi mugun tashi na koma da baya don kada suganni.

To kundaga ranar na koma gida daga can nake zuwa skul sannan tuni na na d'aukewa qawayen nawa wuta baruwana dasu har xuwa yanzu banayi musu magana don ko bikina ban bari sun sani ba.

Ta fashe da kuka mai qarfi tana buga kanta aqirjinsa, riqeta yayi cike da tausayi yace "ya isa hakanan riyya Allah zaiyi miki sakaiya, qarshensu bazai kyauba, sannan nayafe miki Allah ya yafe mana baki d'aya.

Cike da matsanancin kuka ta qamqameshi, shima qamqametan yayi tare da cewa "fad'amin abinda Addawiyya tayi miki da zafi da har kika tsaneta?

"Uhmm ni batayimin komi ba haka kawai naji bansota sam.

D'aure fuska yayi ta mau ya nunata da yatsa " banson sakejin makamancin wannan maganar abakinki, ina ruwarki da ita da zuciyarki zata tsaneta? To kisani ita mai kyawun mu'amalace ga kowa kuma lashakka babu nasan bata damu da keba bama tasannkalar kiba tunda har yau nasan bata shigo part d'innan ba, kota shigo?

Girgiza kanta tayi tare da amsawa da A'a "to kinga tabbacin bata saki aranta ba kenan, don haka ina son kisama ranki sonta kuma ki bita tunda itace babba dake a aure duk da kin girmeta a shekaru, dafatan kin fahimceni?

"Eh, ta amsa ahankali "tam Allah ya had'amana kanku "Amin ta amsa amma aqasan ranta sam batajin sonta kuma tarasa dalilin hakan. Daganan suka koma kamar wani abu bai faruba sai dai Hameed yasaka mata idanu sosai don gudun kada azo tubar mazuru tayi.

Awani dare Haydar ne zaune yana aiki a computer.

Addawiyya ta iso wurin cikin shigar barci, ta zira kanta a kafad'arshi tana leqen abinda yakeyi kallonta yayi ta hasken computer n tare da shafar fuskanta "my angel barci yazo ko? "Uhmm ta amsa tare da kai hannunta cikin rigarsa tasoma wasa da sumar dasuke kwance aqirjinsa, kuma kallonta yayi yaga idanunta kulle kashe computer n yayi ya janyota ta dawo samar cinyoyinsa "ya akayi ne beauty? Murya can qasa ta amsa "wani kewa nakeji yana baquntata wanda narasa ta miye, ina fatan Allah yasa ta alkhairi ce dai "to Amin haskena.

Miqa tayi tare da hamma yabita da kallo yanajin tausayinta sabida yasan bakomi ke damunta ba sai dire amma ita da alama bata gano hakan ba.

"Tashi muje na ragemiki kewar dake damunki.
Kallonsa tayi kad'an ya kashe mata ido 1 tura baki tayi tace "kai ya Ali ni bawannan abin ne ya daniba kawai ji nake kamar zanyi rashin abu mai mahinmanci arayuwata, wata qila Ummie ko Abbie zan rasa. Sai saka mishi kuka sosai.

Shima sai jikinsa yayi sanyi eyes d'insa ya kad'a ji yake kamar ya tayata kukan amma yasan in yayi haka zai jagula komi don haka sai ya d'agata cak ya nufi bedroom da ita, da kyat yayi nasaran rarrashinta ta daina kukan barci ya kwasheta sai sauke ajiyar zuciya take tayi. Washe gari haka ta tashi ba walwala kuma taqi zuwa skul duk kuwa da test d'in dakake dashi don haka 12pm Haydar yataso daga office ya d'auketa suka nufi gidan su Abbie, acan suka yini sai dare duka dawo tuni ta kawo normal suka cigaba da shinfid'a rayuwarsu mai cike da nagarta.

Lamarin zamansu da zuhuriyya kuwa ba yabo ba fallasa domin tuni Addawiyya ta gano tsanarta atare da ita don haka sai ta fita shirginta tabawa banza ijiyarta inba sun had'u part d'in Hajja ba har mantawa take da wata halitta zuhuriyya.

Al'amura suna ta tafiya cike da nasarori yanzu haka matar Hameed zuhuriyya ta haihu tasami baby girl ansamata sunar ummansu suna kiranta da ummul bait haka itama khairi ta haihu ansami takwaran Abba suna kiranshi da Abbul bait.

Aunty Hindu dama ita ta rigasu haihuwa twins ta kuma sinbulowa duka mata yayin da Adda Salma itama ta kuma samun qaruwa yanxu yaranta uku biyu maza mace d'aya.

Addawiyya ce dai tun suna saran ganinta da ciki har sun haqura sun duqufa fad'ama Allah itama ya bata intana da rabo.

Karatunsu kuwa tuni har yazo gaba goshi ita da khairi maryam ce dai ake ta fafatawa don karatun medicine sai anjajirce.

Hajiya karima angamu da iftila'i domin tana zaune taji tasa tashi kafin ace me qafafunta sun kunbure suntom, anyi maganin asibiti har saudi an kaita amma ba cigaba illa dai anyi nasaran kunburin ya baje tafiya dai ne bata iyawa dole aka bata keken guragu take amfani dashi.

Ranar da ta hau tayi kuka mara adadi har tabawa kowa tausayi, atake kuma nadama yazo mata tayi ta fad'an dukanin tuggun datayi ta had'awa tun tuni tare da roqon gafararsu musanman Hindu wanda taso hala kawa 'ya'ya Addawiyya ta cecesu sai lokacin kowa yaji abinda tayi akayi ta mamaki lamarin kuma hakanan suka yafe mata tana hawaye tana yi misu godiya.

Abba yasamo wata dattijuwa dazata riqa kula da ita domin danginta kowa yaqi yarda yazo sabida sanda take da lafiyarta sunce bata tsinana musu komiba sai mulki da gadara.

*uhmm duniya kenan mai abin al'ajab kuma rawar 'yan mata na gaba ya koma baya, Allah kasa muyi kyakykyawan qarshe*

Yau da jin soyayya Haydar ya tashi domin duk inda Addawiyya tayi yana laqe da ita yana aikin latsata gashi aiki takeyi na snacks d'in birthday d'in su hassan, duk yabi ya takurata yana hana mata aikin yayi sauri.

Agajiye taja ta tsaya tana hararanshi "Ya Ali don Allah kabarni haka nan, ingama aikin dake gabana sai kayimin koma miye bazan hanaka ba.

"Kintabbata? "Eh wallahi zanma duk abinda kake so "tam gama kuwa in kasheli da love.

Siririyar dariya ta saki tace "wai ba kamar gaske "au haka kikace? To zan ko shayar dake mamaki kam "uhmm nidai naji matsa kagani inyi ingama lokaci yana tafiya.
Sa hannu yayi yasoma ta yata har suka mammla da komi suka gyara inda za'a gabatar da party n sannan sukayi wanka tare wurin shiryawa da kyat yabarta tagama yin kyalliya.

Yara sun taru sosai na dangi da makwafta.
Abin kuma yayi kyau sosai, Addawiyya ce ja gaba sai photos ake tayi misu da videos.
Daf da za'a watse taro zuhuriyya ta baiyana d'auke da yarinyarta mai kama da ubanta sak.

Addawiyya na ganinsu ta soma hararan su cikin wasa tace "akoma bama so tunda kuna gidan amma sai amakare za kuzo tayamu murnan.

Kallon tsana ta cilla mata tana murmushi, amma cikin kissa yarda ba kowane zai gane hakan ba.

Addawiyya kam tsaf tanago inda ta dosa sai kawai ta saki murmushi itama mai d'auke da matsalarki ce.
Chapter 31 · 0% Book details